advanced Search
Dubawa
14339
Ranar Isar da Sako: 2006/09/23
Takaitacciyar Tambaya
A kawo hadisan da suka yi haramta rawa da kuma madogararsu.
SWALI
wane hadisi ne daga cikin hadisai ya haramta rawa, kuma mene ne madokarar hadisin?
Amsa a Dunkule
Kafin mu ba da amsar wannan tambayar ya kamata mu lura da wani abu guda mai muhimmanci kamar haka, dan an samu ruwaya daya a cikin litattafan ruwayoyi bai wadata ba wajan kafa dalili da ita ruwayar. Domin kafa dalili da ruwaya wani abu ne da ya shafi malaman ilimin fiqihu saboda su ne suka kware wurin fidda hukunce-hukunce shari'a; saboda kafa dalili da wata aya ko ruwaya yana buqatar gabatarwa da ilimi wanda ya shafi hakan saboda haka ba kowane mutum ne zai iya kafa dalili da ruwaya ba. Wananna bangaren ya shafi maluma ne na musamman.
Domin haka ne in muka lura ko muka duba litattafan fiqihu zamu ga bambamcin ra'ayi na malamai a kan abin da ya shafi rawa. Wasu suna ganin cewa ba dukkanin rawa take haramun ba,  da wannan ma'anar cewa in dai yin rawa ba zai kai mutun ga aikata aikin haramun ba ba wannan irin nau'I na rawa bai haramtaba. A mahangar ayatullahi ku'I. a cikin amsar da aka tambayensa dan gane da cewa rawa da kuma tafa hannuwa ayayin buki wanda kuma rurin maza ne kadai ya halatta? Shin yin hakan kuma ga mata ya halatta?, sai yace rawa a matsayinta na rawa ba haram ne ba, matuqar ba za ta kai mutun ga aikata haramunba, kamar cakuduwar maza da mata da makamancin haka[1].
Ajmajirin ayatullahi ku'I wato ayatullahi tabrizi shi ma yana da irin wannan mahangar. Wasu kuma maraje'i na ganin cewa dukkan wani nau'i na rawa haramun ne, lokacin da zai tayar ma mai yin ta sha'awa ko kuma zata kai sa ga aikata haramun. Ayatullahi sayyid Ali khamna'i dangane da hakan yana cewa: Rawa in zata zamanto da yanayin da zata tayar da sha'awa ko kuma zata kai ka aikata haramun ko kuma mukaddama ta aikata fasadi, to irin wannan rawar ba ta halarta ba[2].
Wasu ma na ganin dukkanin rawa haramun ce[3].
Zamu iya kafa dalili da nau'i biyu na hadisai wadanda sukai nuni da haramcin rawa:
1.Kashi na daya su ne wadanda ke hani da dukkanin nau'I na wasa da wargi da makamancin hakan, wanda rawa na daya daga cikin wadannan jerin wato wasa da wargi, kamar hadisin imam Sadiq (a.s) dake cewa: {zamanin da annabi Adam ya bar duniya shaidan da kabila sun yi murna da kida da waka. Saboda haka dukkanin mutumin da yayi irin wannan murnar a doran duniya to ya sani yana koyi ne da wadannan ne wato shaidan da kabila[4];[5]. Ko kuma hadisin da aka samo daga Amiralmumini Ali (a.s) da yake cewa: "Ba mai hankali ba ne wanda ya shagaltar da kansa da wasa da wargi a kowane lokaci[6];.
2. Kashi na biyu su ne su kai hani da rawa kai tsaye, kamar wannan hadisin da zamu kawo; daga imam Sadiq (a.s) an rawaito daga manzon Allah mai tsira da aminci da iyalin gidansa yana cewa: Ina hanin ku daga rawa da kida[7];. a rawaito Daga manzon allah (a.s) ya yi hani da rawa da kida da dukkanin wani nau'I na wasa da wargi, da kuma zuwa irin wadannan wurare da kuma sauraran su[8]…. .
Sai dai bincike da neman inganci wadannan ruwayoyi kowane na bukatar bangare da masana wadanda abun ya shafa[9].
 
 

[1] Saradal najat, ayatullahi ku'I { da hawashi tabrizi }. Jildi na daya , shafi na 372
[2] Ajubatul istifta'at { da harshen larabci } jildi na 2 , shafi na 14.
[3] Mahmudi sayyid muhsin , masa'il jadid, a mahangar malamai da maraja'oin taglidi, jildi na daya ,shafi na 203 zuwa da 204.
[4] Hurul amuli , Muhammad bun Hassan , wasa'il shi'a, jildi na 17 ,shafi na 314 ,
[5] Wannan ruwayar bata inganta ba saboda sanad din ta daya ne kuma a cikin sanad din akwai rawi mai suna abdullahi bin kasim hadrami, wanda ya shahara da karya. Dangane das hi najashi na cewa : makaryaci gullat daga gullat yake yawaito hadisi dan haka ruwayarsa bata da inganci. Shaikh tusi na cewa dangane da bin kasim shi daga mazahabar wakifi yake , mujaml rijal alhadis.jildi na 10 ,shafi na 285.
[6] Nuri , mirza hussain , mustadarak alwasa'il, jildi na 13 , shafi na 220.
[7] Kafi , jildi na 6 , shafi na 432, babi na gina… wasa'il shi'a, jildi na 17 , shafi na 313.
[8] Mustadrak alwasa'il , jildi na 13 , shafi na 218, mussase ahlulbait , wanda aka nakalto daga awali al'ali , jildi na daya , shafi na 262.
[9] Gayatul amal fi sharh kitablmakasib , jildi na daya , shafi na 124.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa