advanced Search
Dubawa
16240
Ranar Isar da Sako: 2012/05/21
Takaitacciyar Tambaya
mene ne ma’anar Takawa?
SWALI
Mene ne ma’anar Takwa?
Amsa a Dunkule

Takawa wani karfi ne cikin ruhin mutum mai tsawatarwa da hana shi aikata ayyukan kuskure, kamalar takawa na kasancewa in an hada da nesantar abubuwan haramun, kamar nesantar shubha. Kuma ita Takawa tana da marhaloli da rabe-rabe, da kuma alamomi, zamu bijiro da su a jawabi na dalla-dalla.

Amsa Dalla-dalla

Lafazin Takawa an samo shi daga Kalmar (Waka, Yaki, Wikayah) ma’anarsa sanya zuciya cikin abin da zai tsare ta ya kuma kareta.1 Amma a ma’a nan shari’a shi ne: kamewa da kuma dakewa a gaban rudun zununbai da kurakurai; a wata ma’anar dabam: ita Takawa wani karfi ne fadakarwa, me tunatarwa a cikin zuciyar mutum, tana kareshi da kuma tsareshi daga zarcewar sha’awa da kuma aikata ayyuka masu saba wa (shari’a). kamalar takawa na tabbatuwa ta hanyar nesantar shubhohi, ballantana kuma nesantar muharamai.

Hakika kamanni da kuma siffofi masu yawa sun zo a kur’ani da ruwayoyi. Daga cikin su zantukan Imam Ali (as) kamar haka:

1-Hakika ita guzuri ce da tanadi: hakika Kur’ani yana kamanta takawa da guzuri da tanadi, kai ! ya ma sanya ta a matsayin mafi kyawun guzuri. A cikin fadinsa Madaukaki; ‘’ Ku yi guzuri, domin mafi kyawun guzuri shi ne Takawa’’.2

2- al-Kur’ani ya kamanta Takawa da cewa ita tufafi, ya ce kuma ita ce ma mafi kyawun tufafi. Kamar a fadinsa madaukaki: ‘’Tufafin Takawa shi ne mafi alheri’.’3

3- (Garkuwa mai buwaya) mai fuskantar hadarin zunubai: Imam Ali (as) yana cewa: Ya ku bayin Allah, ku sani ita Takawa a gida garkuwa ne mabuwayi’’.4

4- Horar dabba ‘abin hawa’. shugaban masu takawa yana cewa a wani zancen dabam: Ku saurara! Kuma ita dai Takawa kamar dabbobin hawa ne horarru, an dora musu laftun kaya, aka saki linzamin su, sai suka kai su aljanna.

5- Daya daga cikin manyan malamai ya kamanta Takawa da cewa kamar mutum ne zai ratsa gona wacce take cike da kayoyi, sai ya yi kokarin kare rigarsa kada ta kama kaya, kuma tafiyarsa zata zama cikin taka-tsantsan da kula don kada kafarsa ta taka kayoyi, ko kuma rigarsa ta kama. Daga wannan misalai zamu amfana kwarai, cewa ita dai Takawa ba janye jiki da kauracewa gefe guda ba ne. amma abin da ya hau kan mutum shi ne ya shige tsundum cikin al’umma tare da kokarin kare kansa.7

Kuma ita Takawa na nuni da imani da Allah da kuma makoma. Kuma ita ma’auni ce na daukaka. Kuma da ita ake tantance dattakon mutum a musulunci.8

A mahangar Kur’ani lallai ita Takawa wani haske ne na Allah (t) wanda yake tattare da ilimi da sani (ma’arifa) a duk inda ta sauka ta kuma kafu.

 

Marhalolin Takawa: Takawa na da marhalai masu yawa; yayin da sashin malamai suka sanya Takawa hawa uku:

  1. Kare kai daga azaba madawwamiya ta hanyar samar da akida mai inganci.
  2. Nesantar kowane nau’in zunubi, wanda ya kunshi barin wajibi ko aikata sabo.
  3. Watsar da duk wani abun da ke shagaltar da zuciyar mutum, ya kautar da ita daga barin gaskiya (Allah) wannan ita ce takawar kebantattun bayin Allah. Kai ba ma haka ba, sai kebantattun-kebanttatu’’.

Rabe-raben takawa: takawa nada rabe-rabe masu yawa, daga cikinsu abin dd zamu yi nuni kamar haka: akwai takawar dukiya, tattalin arziki, da mu’amala, da mu’amalar mace da namiji, rayuwar al’umma. Da takawar siyasa, da takawar dabiu, da sauransu….mutum mai takawa shi ke kiyaye mafi kyawun wadannan rabe-rabe na takawa.

Tasirin Takawa: Takawa tana da tasiri mai kyau mai yawa a cikin rayuwar dan Adam, bari mu yi nuni ga sashen su:

  1. Gina mutum: Imam Ali (as) ya yi nuni ga wani sashe na dabiun masu takawa a wajen gina mutum kammalalle, Kamar haka; sha’awarsa matacciya ce, fushin sa abin kamewane, ana burin samun alheri daga wajensa, an aminta daga sharrin sa, in yana cikin rafkanannu sai a rubata sunansa a cikin masu ambaton Allah, in ko yana cikin masu ambaton Allah ba za a rubuta sunansa cikin rafkanannu ba. Ya na yin rangwame ga wanda ya cuce shi, yana baiwa wanda ya hana shi, yana zumuncin wanda ya yanke masa, ya nisanci alfasha, mai tattausan zance, abin kyama ya buya daga barinsa, alherin sa kuwa yana tare da shi, alherinsa mai fuskantuwa ne, sharrinsa ya juya baya, a yayin firgici shi mai nutsuwa ne, a yayin matsaloli shi mai dauriya ne, a lokacin zaman lafiya shi mai yawan godiya ne, ba ya zaluntar wanda yake ki, ba ya wuce gona da iri ga wanda yake so. Yana yin ikirari da gaskiya kafin a tsaida shehu a kan sa.’’
  2. Daukar Dawainiya: mutumin da yake da Takawa baya gujewa nauyin da ya hau kansa na shari’a, amma yana karbar su da murna. Tare da fuskantar dukkan matsaloli da wahal-halu cikin tabbatuwa.
  3. Yanci: Ita Takawa hanya ce ta yantuwar mutum daga kowace irin bauta. Domin shi mutumin da ke da Takawa bai yiwuwa ya mika wuya ga sha’awowinsa, ba kuma ba zai bada kai ga sauran dabi’unsa na karkata da sha’awance-sha’awancen ransa ba, shi yana cikin aminci daga kowace irin halaka.
  4. Rabauta a ranar lahira: Takawa ita ce mabudin shiriya, saboda mutumin da ya shiriya yake kuma tafiya a kan tafarkin shiriya zai samu rabautar duniya ga kuma lada da kuma tanadi a ranar kiyama.
  1. Ragib–al-isfahani, Hussain Bn Muhd, Mufradat fi Garibul Kur’an, juz1, shafi881 maddat (waka). Dar-al-ilm. Darul shamiya. Damaskus. Beirut 1412 kamari.
  2. Albakarat 197
  3. Al’a’araf, 26
  4. Nahj-ul-balaga, huduba 157
  5. Nahj-ul-balaga, huduba: 16
  6. Abulfatahi Alraziy, Hussain bn Ali, Raudul Jinan fi Tafsiril Kur’an juz’1 shafi 101 Astan Kudus rezawi, Mashad, 1408 kamari, Makarim Shiraziy, nassit Tafsiril Amthaal juz1 shafi 80 darul kutubul-islamiya.tabat al’ula. Tehran1374 shamsi.
  7. Altafsir-al-amthal.juz22 shafi204.
  8. A-lhujurat 14. ( (mafi daukakar ku a wajen Allah wanda ya fi takawa
  9. Al-bakara: 282 ( (ku ji tsoron Allah sai Allah ya sanardaku)).
  10. Altafsir-al-amthal, juz22, shafi 205, Allama Majlisi, Biharul anwar, juz70 shaafi, 136 mu’assatul wafa, Beirut lebenon. 1404 hijra kamari
  11. Nahj-al-balagah, hudubar masu takawa.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa