Please Wait
13443
Bama musun yiyuwar wannan ruwaya kai tsaye sai dai wannan ruwaya ba a cika samunta ba sai a litattafan da suka yi nisan zango da zamanin amirul muminin (a.s) nisanda mafi karanci shi ne shekara dubu, marubucin <Auwal musha sheen> na daga marubutan karshe ya ciro wannan ruwaya tare da dangantata zuwa littafin <mu’unisul hazeen> na sheikhus saduuk ba tare da bayyana danganenta da zurfi ba, bugu da kari wannan littafi da aka fada babu shi yanzu a hannun na, muna kokwanto saboda wasu dalilan danganta wannan hadisin da sheikh saduuk hadi da asalin ilimin hadisi wannan ilmi baida dangantaka da ilimin fikihu, tarihi ko akida.
sanadin ruwayar da aka yi nuni garta cikin tambaya kamar yadda ya zo a littafin <nurul mus’ash een, khulasatul buldan, da mu’unisul hazeen> muna bukatar samun ruwaya wajan war ware maganar cikin kowane littafi domin isa zuwaga natijar da muke nema.
- Littafin <anwarul mush’ash’een> cikin bayanin mutanen Kum da daukakar Kum ittafi mai juzu’i uku da akayisu da harshen farisanci, yana magana kan tarihin kum da sharhin rayuwar ya’yan imamai (a.s) da aka binne cikin Kum hakanan ya hada da sharhin ruwayoyin ma rubutan Kum tun daga shekara ta dari shida aka rubuta shi tare da yadashi sau daya a Iran tun lokacin da aka rubuta shi,
- Littafin <khulasatul buldan> an rubbta shit un shekara ta dari uku, ya yi magana kan abubuwan da suka shafi Kum, ana daukarsa cikin mafiya muhimmancin litattafan hadisi
- Shi kuma littafin <mu’unisul hazeen> ruwayar da aka samu cikin an danganta ta da sheikh saduuk wanda shi ne hasbuzzahir baban ja’afar Muhammad dan Ali, tarihin wafatinsa a takaice cikin shekara ta dubu (1000) inda ya ambato wannan ruwaya cikin littafin da ake kiransa <mu’unisul hazeen > hakanan manyam malaman da suka biyo bayansa kamar dan shahr ashuub, dan dawuus shima bai ambaci wani abu ba game da wannan littafi da aka dangantashi da sheikh saduuk ba, sai dai zaka samu cikin falaldin ashuub ruwaya da aka ciro daga <mu’unisul hazeen> tare da an ambaci wannan littafin da kulalmil alkalamin (Muhammad, kitklun naisabury) ga sheikh saduuk. magana ta biyu ita ce duk da rufe ido ga mawallafin littafin shi ne ba zaka samu dukkan wani shafewa da ga wadannan litattafan bayan dukkan abin da muka bayyana ta hannnu masu bayyana (tantance) da har zamu iya hukunta musu hukunci sanadinsa da dalilin ruwayoyin da muka ambata bayan dukkan wannan bayani muna bukatar waiwayawa zuwa wannan gabatarwar kamar haka
- Wannan ruwaya zamu iya kara duba a kanta cikin littafin anwarul mushash’een wanda ma’abocinta na daga marubutan karnin karshe, kuma ruwayar da aka samo cikinsa kanta bata da girman sanadin da za a iya wani inganta ta da shi (saboda yankewar dangane)
- Baiyi nunin wannan ruwaya tasa ba zuwa kowa ne littafi b, har ma da manyan litattafai irinsu bihar da sauransu wadanda ke dau ke da dukkan hdisai
- Dangantakar littafin mu’unisul hazeen na sheikh saduuk ya yi binciken da yake da kokwanto mai tsanani a cikinsa
- Ingancin wannan dangantaka domin kuwa tsananin <khulasatul buldan> wanda shi ne masdarin da <anwarul mush’ash’een> ya zo da shi wanda tsananin <mu’unisul hazeen > wanda ake kiran samun ruwayar a cikinsa, ansamu ruwayoyi a cikinsa wanda tazar sa da <anwarul mush ash’een> ya kai kimanin shekara dari bakwai (700) hadi da salsalar sanadinsa daga mai ruwayar zuwa sheikh saduuk ba, haduwar wannan kuwa tare da ganin babu damar sallamawa cewar daga sheikh saduuk yanke, koda kuwa littafin na da sanannen dangane ga sheikh saduuk kamar sauran litattafansa, ko kuma ya tabbata zuwa gares wannan ishkali ba zai karu ba.
- Hadi kan abin da ya zo cikin tambayar mai tambaya ya ce a cikin littafin karshe da nuna hadisin ingantacce ne tare da rashin samun sanadin da ya dangane balle a yi hukunci kan ingancinsa da rashin ingancin.
- Da mun samu ruwayar cikin littafin da ake la’akari dasu kamar kutubul arba a wadanda ake ganin lokutan da aka yisu na kusa da lokacin ma’asumai (a.s) kuma wannan ruwaya bata da sanadi, malaman addini basa la’akari da ita sai dai idan ta samu ingantuwa daga watanta, amma kuma ba su da damar musunta kai tsaye, balle ma ruwayar ba a samota daga littafin da akalla shekaru dubu (1000) bayan barin ma’asumai (a.s) kuma bata hada hanya da wani littafin da za a yi la’akari da shi ba. Kari da haka muna iya fitatar da natija kamar haka; rashin ruwayar riko da wadannan ruwayoyin, da kuma sharuddan ilimin hadisi domin tabbatar da hukuncin sa ta hantar tarihi, fikihu, magana, … kuma ba zaka iya samun tabbaci kowane littafi, dalilin lura da zai tabbatar maka da asasin rayuwar wannan bangare, sai dai hakan ba zaisa ka kore rayuwar ba muna ganin na daga larura a ambata hanyoyi kamar haka;
- Nassin larabci na wannan hadisin bamu da shi a hannunmu
- Ba zai yiwu mu kaddara wanna hadisin daga mu’ujizozin imam Ali (a.s) ba, sai dai idan zamu iya tabbatar da shi daga littafin magabata ba, kuma littafin karshen lokaci ba (ba maga bata na kusa ba)
- Wannan ruwaya ba zamu iya amfanuwa daita a matsayin dalili ba, sai dai idan zata iya karfafa mana gwiwa.
Allah ya sa mu dace.