advanced Search
Dubawa
8854
Ranar Isar da Sako: 2010/12/27
Takaitacciyar Tambaya
shin ya inganta mutum ya karanta littatafan wasu malamai irinsu Dr. Ali shari’ati (a.j)?
SWALI
shin ya inganta mutum ya karanta littattafan wasu malamai irinsu Dr. Ali shari’ati (a.j)?
Amsa a Dunkule

Akwai ra’ayoyi mabanbanta masu sabani da juna dangane da karanta littatafan Dr. Ali Shari’ati. Akwai masu wuce gona da iri, akwai masu tauye shi. Sai dai daidaitaccen ra’ayi kan batun shi ne ra’ayin Sayyidul Ka’id Ali Khamana’i. Wannan shi ne ra’ayi madaidaici kuma mafi adalci a wannan batun, wanda shi ne ra’ayin Sayyidul Ka’id Ali Khamana’i. Dan haka za mu takaitu da abin da ya ce a kan wannan batun:

 “Ina ganin duka bangare biyu; watau masu goyon baya da ‘yan adawa sun zalunci Dr. Ali Shari’ati. Hakika an gaza gano wannan jajirtaccen mutum masoyi wanda yin hakan watsi ne da kimarsa da rashin sanin wane +ne shi.

Su kuwa masu adawa da shi sai suka yi riko da wasu kurakurensa da ya yi, wadda yin hakan ya sa an yi watsi da kyawawan ayyukansa da fakewa da kurakurensa da yin watsi da inda ya fi mahimmanci!

 Sabanin yadda wasu ke yadawa, Shari’ati bai taba samun matsala da malaman Addini ko na Hauza ba, mutum ne daga cikin muminai da ya ke kimanta malaman Addini (irfani). Yana ganin tilas Hauza ta wanzu, kana ya dauke ta babbar cibiya mai tushe da bata da ma kusata ta kowace fuska. `Kuma duk wani mai kushe ta ya fada tarkon ‘yan mulkin mallaka kuma ya zama dan korensu ne. Wannan shi ne ra’ayin mutumin da babu kokwanto a kai. Sai dai Shari’ati yana ganin malaman Hauza na Addini da na tarbiyar ruhi ba su ida sauke nauyin da ke kansu ba.

Amsa Dalla-dalla

Akwai ra’yoyi mabanbanta masu sabani da juna dangangane da karanta littatafan Dr. Ali Shari’ati. Akwai masu wuce gona da iri akwai masu tauye shi. Sai dai daidaitaccen ra’ayi kan batun shi ne ra’ayin Sayyidul Ka’id Ali Khamana’i. Wannan shi ne ra’ayi madaidaici kana mafi adalci a wannan batun, wanda shi ne ra’ayin Sayyidul Ka’id Ali Khamana’i. Dan haka zamu takaitu da abin da ya ce a wannan batun:

 “Ina ganin duka bangare biyu watau masu goyon baya da ‘yan adawa sun zalunci Dr. Ali Shari’ati. Hakika an gaza gano wannan jajirtaccen mutum masoyi wanda yin hakan watsi ne da kimarsa da rashin sanin wane ne shi.

Su kuwa masu adawa da shi sai suka yi riko da wasu kurakurensa da ya yi, wanda yin hakan ya sa an yi watsi da kyawawan ayyukansa ta fakewa da kurakurensa da yin watsi da inda ya fi kwarewa!

A ganina Shari’ati ya yi wasu kurakurai da ba za’a daukesu kanana ba, sai dai a ganina ta yiwu a ture wadannan kurakure da tuntuben alkalami a gefe guda kana a kalli ayyukansa nagari fitattu cikin ayyukansa. Ya na daga cikin zalunci yin watsi da mahimman ayyukan mutumin da maida hankali kan kurakurensa zalla. Ba zan manta ba, a kwanaki na karshe a sanda jayayya ta tsananta na sukansa wadda za a iya cewa matakin karshe ne na kace-nace a kan Dr. Shari’ati –inda Imam Khomain ya sa baki ya yi hannunka mai sanda– ba tare da ya kira suna ba, ya yi batu kan Dr. Shari’ati ya ke zance a kan gutsuri-tsoma da ake a kansa. Lalle mun samu kaset din a Najaf a lokacin inda Imam ya taka rawa wajen dakushe kaifin rigimar da kwantar da fushi da kace-nace, a sanda ya yi batu a dunkule inda ya ce: “Bai dace a ci mutuncin mutumin -bai kira suna ba- sabodo kurakure hudu da aka samo a littattafansa”.-

Wannan lamari kuwa bai takaita ga Dr. Shari’ati kadai ba, ya Shafi kowa. Dan haka bai dace a zubar da kimar mutum saboda samun wasu kurakure na fahimta ko koskure na manufa tasa ba. To tilas a dauki matsakaicin matsayi kuma ingantacce da duba na tsanaki a guraren rauni da karfi na wannan mutumin da yin bitarsu bisa wannan mahanga ta adalci.

Zaluncin da masoya da masu goyon baya suka lika masa, ya ma fi na masu rigima da shi. Ko kuma a ce ya fi muni da baci!. A sanda ya dace su maida hankali a wajen yada kyawawan manufofinsa da dora jama’a a kai, sai suka ja daga suna kokarin tabbatar da cewa shi abin koyi ne kai tsaye, komai nasa daidai ne ba wani kuskure ko tuntube a ciki, alhali sun yi watsi ne da duk wani kuskure.

Hakika Shari’ati ya damu ainun bisa rashin tafiyar da tsarin musulunci, kana yana jin zafin rashin tafiyar da tsarin musulunci a tsari na zamnatakewa dari bisa dari da wadatuwa da manufofinsa da tunaninsa na fatar baka. Ya yi matukar fadi-tashi da nufin aiwatar da musulunci a matsayin kyakkyawan tunani da nufin gina rayuwa a matsayi na zamantakewa da fahimta kyakkyawa don warware matsalar rayuwa.

Babu Shakka Shari’ati gwarzo ne a fage na yada musulunci. Kuma daya ne daga cikin gwaraza a fagen yada musululnci a sabon salo a wannan zamani. Sai dai, akwai da yawa da suke da fahimta ta musulunci a zuzzufar fuska kamar yadda Shari’ati ya fahimce shi. Sai dai ya saba da su a salon da suke bi wajen gabatar da nasu tunanin fahimtar da su da Shari’ati ta hanyar bayani filla-filla da jan hankali.

Shari’ati gwarzo ne a fagen fayyace matsaloli da suka Shafi Musulunci da zurfafawa ta fuskar amsa kalubalen zamani da kawar da Shakku da iya kyautata bayani a kansu.

Sabanin yadda wasu ke yadawa, Shari’ati bai taba samun matsala da malaman Addini ko na Hauza ba, mutum ne daga cikin muminai da ya zurfafa a bangaren malanta (irafani). Yana ganin tilas Hauza ta wanzu, kana ya dauke ta babbar cibiya mai tushe da bata da kamarta ta kowace fuska. Kuma duk wani mai kushe ta to ya fada tarkon yan mulkin mallaka kuma yana musu aiki ne. Wannan shi ne ra’ayin mutumin da babu mai kokwanto a kai. Sai dai Shari’ati na ganin malaman Hauza na Addini da na tarbiyar ruhi ba su taka rawar da ta dace bane1.

Daga abin da ya gabata za’a fahimci cewa kowane masani da marubuci gogewarsa kan bayyana ne a bangaren da ya fi gogewa. Kasantuwar Dr. Shari’ati ya goge ne a bangaren ilimin zamantakewa, a nan ne ya fada wasu kurakure dalilin shiga wani hurumi da ya Shafi Musulunci da ba fanninsa ba ne. Sai dai duk da haka a fannainsa ya yi matukar taka rawa a bangaren da ya fi gogewa a kai, ya yi hobbasa ta azo-a-gani a fagen ilimi. A nan ne nake ganinn ya zama dole a ba da fifiko a goraren da ya fi tagazawa:

  1. Sai dai kafin karanta littatafan Shari’ati ya kamata a fara duba tafsiran wasu malamai irinsu tafsiran Amsal na Sheik Makarim Shirazi, da littafan Shahid Mudahhari.
  2. Ba zai yiwu a kalli rubece-rubucen da ya yi a fagen sanin Musulunci, ko tarihin Musulunci da bayani game da al’amuran Musulunci ba, (kai tsaye). Kusan ba shi da wani bambanci da na wasu marubuta, ba ya da wata kariya ta kuskure ba za a dauke shi a matsayi na tatacce da babu kokwanto a ciki ba.
  3. A duk sanda aka ga matsala da sabani a rubuce-rubucen Dr. Shari’ati, to ba wani bambanci tsakanin shi da sauran marubuta da masana to a nan, litas a koma a dauki zancen marubuta matsakaita da ke da zurfin sani a wannan bangare domin samun mafita da ta dace, sai a yi watsi da wannan taburza a fagen ilim.
  4. Hukunci da muka ambata bai takaita ga Dr. Shari’ati shi kadai ba, ya hade da sauran masana da marubuta.

Domin Karin bayani za’iya duba: al’imam ba roshan fikran (الامام و روشنفكران، القسم الاول) Juzu’i na farko; Shin wane ne Shari’ati kana me ye ra’ayinsa, kana me ya haifar da sabani?

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa