advanced Search
Dubawa
7530
Ranar Isar da Sako: 2012/04/26
Takaitacciyar Tambaya
Me ye gwargwadon ikon da aka ba wa wilayatul fakih (Jagorancin malami)?
SWALI
Me ye gwargwadon ikon da aka ba wa wilayatul fakih (Jagorancin malami)?
Amsa a Dunkule

Dalilan shugabancin malami (wilayatul fakih) suna bayyana cewar, fakihi shi ne wanda yake jagorantar al’umma ta musulmi, kuma yake maye gurbin imamai ma’asumai (amincin Allah ya tabbata a gare shi) a zamin da imami yafaku (boye). Ta wannan matashiyar wilayatul fakih (Shugabancin malami) tana da abubuwan da suka cancanta suke wajabta jagorancin al’umma da kuma gudanarwa, ya ga jagoran ya cancanci wannan matsayin. Wannan shi ne abin da wiyalatul fakihi take nuni a kansa ta fuskar ma’anar ta a shari’ance.

Hakika wilayatul fakih (Jagorancin malami) tana da matsayi biyu:

  1. Matsayin shi wanda yake da wilaya a kansu (shugaban).
  2. Matsayin abubuwan da yake da walicci a ciki.

Amma a matsayi na farko, shi fakihi yana da iko a kan daidaikun mutanen al’umma, musulmi da wanda ba musulmi ba, mujtahidi ne ko ba mujtahidi ba ne, mai koyi da shi, kai har ma da mujtahidai, kai har ma da kansa, idan ya bayyana wani hukunci daidai da ma’aunin shari’a to wajibi ne kowa ya bi shi har ma da sauran malamai (fakihai) da shi kansa.

Amma a matsayi na biyu tabbas waliyyi fakihi yana da shugabanci a cikin sha’anoni da al’amura na al’umma, zai fitar da huknci gwargwadon yadda yake kan ma’auni a cikin wadannan al’amura kuma wajibi ne ga kowa da kowa ya yi mara da’a.

Tun da har Wilayatul fakih (Jagorancin malami) an same ta ne daga cikin shari’a mai tasrki saboda haka, dole ne ayi aiki da ita a bisa gwargwadon da shariya ta bayyana a matakai da wurare daban-daban.

Don haka ne zai kula da maslaha a cikin hukunce-hukuncen da ba na dole ba, amma a hukunce-hukunce na dole zai kiyaye sharuddan matsatsi.

Sannan wajibi ne a gare shi ya yi riko da duk abin da yake shiga musulunci (ma’ana ya san duk ilimi na musulunci) na mabambanta wuraren aiki na al’umma, wanda ake kira a fahimtar tunani rubutaccen (mazhabi) ko (tsari) sannan ya yi kokarin gina tsarin tattalin arziki na musulunci, tarbiyya, zamantakewar al’umma, a cikin mazaunin al’umma, wannan ba komai bane face sai iyakancewa da tantance cancantar fakihi daga bangaren shari’a.

Amsa Dalla-dalla

Hujjoji na wilayatil fakihi suna bayyana cewa shi fakihi shi ne wanda ya jagorantar al’ummar musulunci kuma yake maye gurbin imamai ma’asumai (amincin Allah ya tabbata a gare shi) a zamanin fakuwar imami. Daga wannan mahangar (matafiya) za mu ga cewa ita wilayatul fakih (Jagorancin malami) tana da abubuwan da suka dace da ita dangane da jagorancin al’umma da tafiyar da jagorancin sannan tana da abin da masu hankali suke kallo a matsayin abubuwan da suka cancantar da jagoran, da kuma abin da ya sa imamai (amincin Allah ya tabbata a gare su) suka dace da wannan jagorancin.

Wannan shi ne abin da dalilai na magana suka yi nuni a kai. Musamman rubutu mai sharafi na (Imam Mahdi) wannan shi ne abin da ake ce masa wilayatul fakih (Jagorancin malami) mudlaka (sake babu kaidi), kishiyar ta kuma wilayatul fakih (Jagorancin malami) mukayyada (mai kaidi).

“Al’idlak” yana nufin rashin samuwar wani dabaibayi wannan shi ne akasin “takayyud” wilayatul fakih (Jagorancin malami) mudlakan tana da matsayi biyu:

  1. Matsayin wandanda yake da wilaya a kansu.
  2. Matsayin al’amuran da abubuwan da yake da wilaya a ciki.

Amma a matsayi na farko, fakihi yana da wilaya a kan daidaikun mutanen al’umma ta musulmi, musulmi daga cikinsu har ma da wanda ba musulmi ba, mujtahidi da wanda ba shi da ilimi, har da ma masu yin koyi da shi da kuma sauran mujtahidai, kai har ma da kansa, idan ya fito da wani hukunci wanda ya dace da ma’aunai, to wajibi ne kowa ya yi masa biyayya har ma da sauran mujtahidai.

Dalilai na wilaya a kamar yadda muka bayyana a baya ruwayoyin mudlakai na shugabancin na nuni zuwa gare shi a bisa dalilin nan na furuci (adillatul lafaziyya)[1], kai har ma da tunani na hankali wanda ke yin hukunci da jagoranci.

Sabanin wannan ra’ayin, wani yana ganin wilayatul fakih (Jagorancin malami) ta kebanta ne a kan wadanda suka kasa gudanar da abubuwa su[2] saboda kalmar wilaya tana nufin tsayawa tare da kulawa saboda wanda aka jibintawa a wannan yanayin ya kasa gudanar da abubuwan sa kuma ba ya iya bambance abin da ke yi masa amfani da abin da ba ya yi masa amfani (yake cutar da shi). Alhalin kalmar wilaya na amfani da ita a waje biyu a fikhu. A waje na farko tana nufin wanda ya gajiya, amma a waje na biyu ma’ana wilayatul fakih (Jagorancin malami) tana da ma’anar hukunci, a nan kuma ba ta nuni a kan waccan ma’anar.[3]

Don haka wilayatul fakih (Jagorancin malami) ba a shardanta gajiyawar wanda aka jibinta masa abu ba, ballantana wani ya ce jamhuriyar musulunci tana karkashin wilaya ta fakihi, wanda wannan bayani ne wanda ke tattare a kan tufka da warwara.[4]

wilayatul fakih (Jagorancin malami) tana nufin shugabanci da hukunci tare da bayyana kamalar wanda aka jibinta ba tare da gajiyawa ba, saboda gudanar da al’amuran al’umma ba tare da wilayatul fakih (Jagorancin malami) ba zai yiwu ba.

Don haka ne sauran fakihai dole su yi biyayya ga hukuncin fakihi wanda ya jibinci al’amura, ko da kuwa sun kai matsayi na wilaya a bisa mahangar nan ta ayyanawa wacce ta dace da mashahurin ra’ayi ingantacce, da biyayyar su ga fakihi saboda takaitawar su ne da gajiyawar sa to yaya dalilan wilayatul fakih (Jagorancin malami) zai zama sun game har da su.

A matsayi na biyu fakihi yana da wilaya a cikin al’amuran al’ummar, zai yiwu ya fito da hukunci gwargwadon ma’aunai a cikin wannan al’amuran, idan ya yi hukunci wajibi ne kowa ya yi masa biyayya. Dalili a kan haka shi ne; zuwan hujjoji na lafazi da kuma wajibcin shugabanci da jagorancin abin da ya hadu da wadannan sha’anai.

Wilayatul fakih (Jagorancin malami) ko shugabancin malami ya sami hujjoji daga ayoyin Alkur’ani da Hadisai, to don haka ya zama dole a yi aki da ita gwargwadon yadda shari’a ta sanya ta a wurare daban-daban.

Don haka ne an dora masa kiyaye maslaha a cikin abubuwan da shari’a ta halatta, ai abubuwan da ba a wajabta su ba, ba a kuma haramta su ba, ko da mustahabbai ne ko makruhai, don tabbatar da samuwar masalaha shi ne ma’aunin zartar da wilayarsa.

Idan aka gano wani amfanin da zai taimaka wa al’umma ko tsarin musulunci, ko wata jama’a, to fakihi zai ba da umarni ko hani (idan abin zai cutar) don ci gaban al’umma, kamar yadda mutane suke gudanar da ayyukan su game da abubuwan da suke samun maslaha a ciki fiyayyen dalili a kan haka aya madaukakiya: (Annabi shi ne ya fi cancanta ga muminai fiye da kawunansu).[5]

Sannan mu jingina wiyalatul fakihi ga wannan ayar, domin ayar tana nuni da cewa Annabi (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) shi ya fi cancanta da muminai fiye da kansu. Idan zai yiwu game su su aikata wani abu ko su bar wani abu kamar yadda yake musu dadi, to Annabi (Annabi shi ne ya fi cancanta ga muminai fiye da kawunansu) sh ne ya fi dacewa ya umarce su, ko ya hana su.[6]

Hakika dalilai na wiyalatul fakihi sun tabbatar da cewa, abin da Annabi (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya jibinta da kuma Imamai (amincin Allah ya tabbata a gare su) to fakihi ma haka ne, don haka zai gudanar da al’amura tamkar yadda Manzo da Imamai za su yi (amincin Allah ya tabbata a gare su). kuma wannan ma na wuyan fadihi, kenan shi ma zai iya tsaya wad a wannan ainihin aikin (zai iya tsayawa a wanna matsayar).[7]

Don iyakance maslaha a cikin abubuwa ba makawa sai an yi riko da bangaren ma’auni tare da kulawa, to wannan sashen sai an dawo wajen masana a cikin ilmummuka na al’umma domin su tabbatar da samuwar amfani a cikin abubuwan da aka sa a gaba.

Kamar haka ne ba makawa ga fakihi yayin zartar da ikonsa, ya nemi taimakon masana daban-daban da wadanda suka yi fice saboda ci gaba. Idan fakihi ya yi nufin zartar da abu daga cikin abubuwan da shari’a ta fitar da hukunci na lazimtawa kamar wajibici ko haramci, sai ya yi hukunci da abin da ya saba wa shari’a halattawa ko haramtawa, to wannan ya rataye ne da kiyaye ka’idojin (matsatsi). tazahumi (matsatsi) yanayi ne wanda wajibai biyu suka hada, kowa ba zai yiwu ba a yi su duka ba, zartar da daya shi ne sababin barin dayan. To a nan wajibi ne a dauki mafi muhimmanci a bar dayan duk da muhimmancin nasa.

Aikin iyakance matsatsa da abu mafi muhimmanci da muhimmi dangane da al’amuran mutane daidaiku, ya wajaba a wuyansu mutanen, amma idan abubuwa na kowa da kowane (jama’a gaba daya) ba makawa sai jagora ya dauki matsayi domin aiwatar da shi, kuma ya wajaba a kan kowa yin biyayya. Sau da yawa a kan buga misalin tazahumi (matsatsa) ta hanyoyi kamar haka:

Idan wani ya wuce ta kusa da gidan wani sai ya ga yaro zai fada cikin ruwa ko ma zai nutse a cikin ruwa (swimming pool), to a nan matar ya fuskanto wajibai guda biyu ba zai iya yin su ba duka nan take. Wajiban su ne:

  1. Kubutar da yaron daga nutsewa.
  2. Rashin shiga gidan ba tare da izini ba, ba makawa a nan sai ya gabatar da mafi muhimmanci a kan muhmmi shi ne: kubutar da rayuwar yaran nan a kan muhimmi (rashin shiga gidan ba tare da izini ba). Bugu da kari, a kan abin da yake da nasaba da tazahumi (matsatsa) a cikin abubuwan al’umma, zai yiwu mu ba da misali mai zuwa. Idan fari ya zo gari, sannan kuma ga matsalar kayan ci, idan ba a warware matsalar ba mutane da yawa za su afka cikin wahala har wasu ma su mutu, hakan kuma zai jawo tsarin musulunci ya shiga cikin hadari. A wani gefen kuma akwai kayan ci wanda aka haramta kamar kofin da ba shi da bawo a saman fatarsa (kishir) za a fita daga cikin wannan kuncin idan aka halatta cin kofin. To a nan cin wannan kofin ya halatta saboda lalura, wannan shi ne misalin tazahumi (matsatsi). Nauyi biyu ya hau kan hukumar musulunci.
  1. Wajibcin kiyaye rayuawr al’umma.
  2. Haramcin cin kifi maras bawo.

A nan wajibi ne a rinjayar da mafi muhimmanci, tabbas kiyaye rayuwar al’umma daga halaka, a kan mafi karancin muhimmanci kifi maras bawo, saboda haka sai a bayyana halaccin cin kifin. A wannan yana yin cin irin wannan kifin ya halatta ga baki dayan mutane, yadda abin yake tazahurimi (matsatsi) ba ta tabbata sai tare da rashin wata hanya ta warware matsalar yanwar ba, sai dai idan an halatta cin irin wannan kifin.

Ta wannan janibin hukunce-hukuncen da ake fito da su lokacin tazahum (matsatsi) suna zarcewa matukar matsalar ba ta gushe ba. idan matsalar ta tafi to wajibi ne a dawo wa hukunci na farko. Don haka wajibi ne a kan fakihi kiyaye maslaha a hukunce-hukuncen da ba na dole ba, ya wajaba ya kiyaye lokutan tazahumi a hukunce-hukuncen tabbatarwa.

Sannan wajibi ne ga fakihin ya san duk abin da ya danfaru da musulunci har ma da wurare mabambanta na ayyukan al’umma, wanda ake kira a mahangar nan ta (mahanga matabbaciya) (nazariyatul fikri madawwan) mahaba da tsari (mazhabi da ‘nizam’).[8] Sannan ya tabbatar da tsare-tsaren tattalin arziki na musulunci, tarbiyya, zamantakewar al’umma a mahallinta. Wannan fa shi ne abin da yake iyakance dacewar fakihi a shari’ance.

Domi karin bayani a koma mahadi hadawi dahareni wilayat wa diyanat muassatu farhange khane dar, kun, bugu na biyu, 1380.

 


[1] Maudhu’in dalilan shugabancin malami.

[2] Al kussru jam’I ne na kasir wanna na nufin mutumin da y a gajiya kan gudanar da lamarin san a kansa. 

[3] Maudhu;in shugabancin malami.

[4] Ka duba mahdi alha’iri aluazdi. A cikin hikimat wa hukumat shafi na 216.

[5] Surar ahzab aya ta 6.

[6] Mahallin bincike kan shugabancin ma’asumai (amincin Allah ya tabbata a gare shi).  

[7]  Maudhu’in dalilan shugabancin malami.

[8] Maudhain Al’islam Wa Nazariyyatul Fakikril Mudauwan.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa