Please Wait
12537
Idan muka koma wa tarihi da littattafansa zamu ga cewa Abubakar dan Ali dan Laila ‘yar Mas’ud assakafi, da Umar dan Ali dan Ummu habib, da Usman dan Ali dan ummul Banin (s), dukkansu ‘ya’yan Imam Ali (a.s) ne, kuma bayan mun duba sanadin ambatonsu da wadannan sunaye na halifofi uku ne zamu iya cewa:
Al’ada da tunanin mutanen wancan lokacin ba ta bayar da muhimmanci kan suna iri daya, kuma ba ta nuna yarda ko ki da wani mutum, ambaton wadannan sunayen a wancan lokacin ba ya sanya tunawa da sunayen wadannan halifofi uku.
Amma mu sani cewa a wancan lokacin wadannan sunayen sun yadu ta yadda ambaton da Imam Ali (a.s) ya yi wa ‘ya’yansa da wadannan sunayen ba ya kawo tunani game da wani daga cikin halifofi uku na farko, hada da cewa akwai wasu daga cikin sahabban manzon Allah (s.a.w) da suke da wannan sunan kamar Usman dan Maz’uan da waninsa.
Wadannan sunayen sun yadu kuma sun shahara a wancan lokacin da bayansa a rayuwar Imamai (a.s) baki daya, kuma littattafan tarihi cike suke da hakan, don haka sunaye ne da suka kasance ba su da wani abin yabo ko muzantawa a wurin Shi'a a wancan zamani kamar dai sauran sunaye suke. Kamar yadda zamu ga marubuta tarihin amintattun mutane na ruwayoyi sun kawo daga ciki kusan shafe 60 na masu ruwaya da yake dauke da sunyan umar, ga ma Usman dan Sa'id daya daga cikin wakilai hudu na Imam Mahadi (a.s) a lokacin karamar fakuwa.
Idan muka koma wa littattafan tarihi zamu ga cewa Imam Ali (a.s) yana da ‘ya’ya daga matan da ya aura bayan shahadar sayyida Zahara (a.s) da uku daga cikin suke da sunayen halifofi uku na farko da suka yi halifanci bayan annabi (s.a.w) da suka hada da; Abubakar dan Ali babarsa Laila ‘yar mas’ud[1], da usman babarsa ummul banin dukkansu sun yi shahada a Karbala karkashin tutar dan’uwansu Imam Husain (a.s) [2], na uku kuwa shi ne umar dan Ali shi ma[3].
Idan kuma duba dalilin ambaton su da wadannan sunayen halifofi uku zamu ga akwai bayanai kamar haka:
1. Tun farko ba za a iya la’akari da sanya sunayen ‘ya’ya da dangi ba na wasu mutane dalili a kan sonsa da kaunarsa ko tarayya da shi a wata akida ko mazhaba ko siaysa da sauransu – kamar yadda rashin ambaton ‘ya’ya da sunan wani mutum ba ya nuna dalili kan rashin sonsa ko kaunarsa da sabawa da shi, sai dai zai iya yiwuwa kauna ko rashin kauna su shiga cikin wasu abubuwan irin wannan a wasu lokuta.
Hada da cewa al’ada da tuannin wancan lokacin ba su kasance suna bayar da muhimmanci mai karfi game da sanya sunayen ba, ba sa nuna yarda ko rashin yarda da mai sunan. Don haka ambaton wadannan sunayen bai kasance yana nuni ga karkakta ga halifofi ba, su wadannan sunayen kamar sauran sunaye ne kawai, sai dai da nisan tafiya a tarihi ne sai wadannan sunayen suka bayyana bayan wancan zamanin ya wuce, amma a lokacin Imam Ali ambaton ‘ya’yansa bai kasance don tunawa da wadannan sunayen na daya daga halifofi ba ko tunawa da halifa na farko.
Kamar yadda babu makawa ne mu sani cewa wadannan sunayen uku ba su kebanta da wadannan halifofi uku ba kawai, su sunayen sun yadu cikin larabawa kafin musulunci da bayansa, don haka sanya sunayen ba sa nunu zuwa ga soyayya da kauna.
Misali a Iran sunan sarkin da ya gabata (Shah) “Muhammad Ridha”, kuma ya kasance mutumin da mutanen iran suka fi kyama, sai dai wannan bai hana kasancewar wannan suna ya kasance daga sunayen da suka fi kowanne sunaye yaduwa a iran ba. Daga cikin sahabban annabi (s.a.w) akwai wanda ake kira da usman dan maz’un da waninsa, me zai hana Imam Ali (a.s) ya ambaci ‘ya’yansa saboda wadannan sahabbai masu daraja ba halifofi ba. Kamar yadda zaku iya gani idan kuka koma wa littattafan tarihin mazajen ruwaya kamar al’Isti’ab na ibn Abdulbarr da Usudu Gaba da ibn Asir, ku lura sosai sun kawo sahabbai masu yawan gaske da suke da sunan Abubakar, Umar, Usman. A nan zamu wadatu da littafin “Usudul Gaba fi Ma’arifatil Sahaba” mu kawo wadanda suke da sunayen Umar cikin sahabbai.
1_ Umar al’Aslami, 2_ Umar al’Jam’I, 3_ Umar dan Hakam, 4_ Umar dan Salim al’Khuza’I, 5_ Umar dan Suraka… 22_ Umar dan alYamani; wadannan duk suna daga cikin wadanda ibn Asir ya kawo su.
Kamar yadda zaku gani wadannan sunayen sun yadu matukar gaske tsawon tarihin musulunci da kafinsa, sun yadu cikin mutane baki daya.
Amma tabi’ai kuwa daga wadanda aka kira su da umar suna da yawan gaske, misali muna iya kawo littafin nan na amintattun masu ruwaya da ya kawo kusan shafi 60 kan adadin masu rawayar da suke da sunan Umar.
Wadannan sunayen sun yadu haka nan a lokacin imamai ma’asumai masu daraja (a.s) kamar abubakar dan Abdullah al’ash’aari, ko abubakar al’hadhrami, sun kasance daga masu ruwaya da suke ruwaitowa daga Imam Sadik (a.s), kamar yadda haka nan muna iya ganin usman dan Sa'id daga wakilan Imam Mahadi (a.s) a lokacin karamar fakuwarsa. Wannan duka yana nuna cewar ambaton wadannan sunayen ba ya sanya tunanin mutane ya juya zuwa ga wanda yake ba mai sunan ba. A tarihi Ali ba daya ba ne, haka ma abubakar da umar da usman ba daya ba ne da Imam Ali (a.s) zai ambaci sunayen ‘ya’yansa don su, sai dai ambaton sunayen ya kasance ya yadu da ma cikin mutane kamar dai sauran sunaye.
Da ambaton sunayen ya kasance da umarnin Allah (s.w.t) ne na musamman don wadannan sunayen da sai ya samu tsarki da daraja ta musamman kamar yadda yake a sha’anin sunayen ‘ya’yan Imam Ali (a.s) da Fadima (a.s) wato Hasan da Husain (a.s).
Don haka wani abu ne da ya kasance sananne cewa wannan sunan da wadancan sunayen na halifofi sun kasance daga sunayen da suka yadu a cikin larabawa lokacin jahiliyya da musulunci duka, jin wadannan sunayen a wancan zamanin ba ya sanya tunani ya juya ya koma zuwa ga halifofi sam. Don haka ba zai yiwu a yi amfani da sunayen domin nuna cewa akwai wata alaka da sosayya ta musamman tsakanin Imam Ali (a.s) da sauran halifofi ba don a rufa duk abin da ya faru na tarihi da musunta abubuwan da suka wakana[4].
2. Muna iya gani cewa Imam Ali (a.s) ya boye dukkan matsaloli da musibun da suka same shi don hikimarsa da basirarsa da rinjayarwarsa ga maslahar baki daya, sai ya tsayu da tafiya tare da halifofi da hukumarsu don kiyaye musulunci da maslahar al’umma, kuma ya kasance sau tari yana taimaka wa halifofi yana karfafar su yana ba su hannun taimakawa gare su, har ma sau tari umar yana cewa: “Ba don Ali ba da Umar ya halaka” [5], to akwai tsammanin cewa wannan sunayen da Imam Ali (a.s) ya sanya yana daga cikin hikimominsa da iya zamansa da mutane, domin shi yanayi ne da yake iya kaiwa ga samun wata kafar sulhu, da kawar da kokwanto da juna, da karanta matsaloli da sabanin da yake cikin al’umma, ba don wai yana karfafa ayyukansu ko son su ba. Ko mai dai me ye “Da mun yi duba da idon basira zuwa ga wancan lokacin mai duhu da dimuwa, da kuma tsananin da yake kan Shi'a a wannan lokaci, da mun ga cewa imamai ma’asumai (a.s) sun zama – bisa tilas – saboda kiyaye rayuwar mabiyansu – su yi aiki da takiyya ta hanyoyin kamar; ambaton sunan ‘ya’yansu da sunayen halifofi ko aure da manyan sahabba don su boye halin tsoro da takura da take kan shi’awa, domin hukumar Banu Umayya da Banu Abbas masu zalunci suna son su samu damar rashin wayewa da karancin tunanin mutane da sunan cewa imamai (a.s) ba su yarda da halifofin farko ba, sai su yi amfani da wannan damar don dada takura musu da tsanantawa da kisa da kora”[6].
Kamar yadda nuni zuwa ga wannan lamari yana da muhimmanci matukar gaske, idan mun duba littattafan tarihi ba mu ga wani bayani ko daya daga yke nuna cewa Imam Ali (a.s) shi ne da kansa ya sanya wadannan sunayen, don haka akwai tsammanin cewa sanya wadannan sunayen ya kasance daga iyayensu mata ne ko wasu makusantansu, kuma Imam Ali (a.s) bai hana su ba don ya girmama su.
[1] Mu’ujamus sikat, j 21, s 66, bisa mahangar dan Ashuubul Auham.
[2] Al’irsha, s 484.
[3] Mu’ujamus sikat, j 13, s 45.
[4] Attabri, Muhammad, jawabus shabil shi’I, s 55 – 56.
[5] Sai na ga hakuri a kan haka shi ya fi, sai na yi hakuri alhalin akwai kwantsa a ido, akwai shakewa a makogaro, ina ganin gadona abin kwacewa. Nahajul balagap; subhi salih, s 48, huduba ta uku.
[6] Attabri, Muhammad, jawabis shabil shi’I, s 56 – 57.