advanced Search
Dubawa
3676
Ranar Isar da Sako: 2019/05/15
Takaitacciyar Tambaya
Shin Ammar Dan Yasir ya temaka wa Imam Ali (a.s) kan lamarin da ya faru a SaKifa ko kuwa?
SWALI
Ina yin sallama a gare su, Dangane da abin da ya wakana a SaKifa, shin Ammar Dan Yasir ya temaki Ali (a.s) ko kuwa?
Amsa a Dunkule
Mutane da dama sun tafi kan cewa Imam Ali shi ne shugabansu, amma yanayin yanda suke yi masa biyayya kuma suka sallam masa ya banbanta, babu tantama tun a farko Ammar ya kasance matemaki kuma mabiyu wanda ya sallamawa imama Ali (a.s) duk da cewa ta yiyu wani abu ya Darsu a cikin zuciyarsu cewa me ya sa Imam ya zaBi yin shiru, me ya sa be zare takobinsa ba, saboda me........? dss.
«عَلِیُّ بْنُ الْحَکَمِ، عَنْ سَیْفِ بْنِ عَمِیرَةَ عَنْ أَبِی بَکْرٍ الْحَضْرَمِیِّ، قَالَ: قَالَ أَبُو جَعْفَرٍ (ع) ارْتَدَّ النَّاسُ إِلَّا ثَلَاثَةَ نَفَرٍ سَلْمَانُ وَ أَبُو ذَرٍّ وَ الْمِقْدَادُ. قَالَ قُلْتُ فَعَمَّارٌ قَالَ قَدْ کَانَ جَاضَ جِیضَةً، ثُمَّ رَجَعَ، ثُمَّ قَالَ إِنْ أَرَدْتَ الَّذِی لَمْ یَشُکَّ وَ لَمْ یَدْخُلْهُ شَیْ‏ءٌ فَالْمِقْدَادُ، فَأَمَّا سَلْمَانُ فَإِنَّهُ عُرِضَ فِی قَلْبِهِ عَارِضٌ أَنَّ عِنْدَ أَمِیرِ الْمُؤْمِنِینَ (ع) اسْمَ اللَّهِ الْأَعْظَمَ لَوْ تَکَلَّمَ بِهِ لَأَخَذَتْهُمُ الْأَرْضُ وَ هُوَ هَکَذَا فَلُبِّبَ وَ وُجِئَتْ، عُنُقُهُ حَتَّى تُرِکَتْ کَالسِّلْقَةِ، فَمَرَّ بِهِ أَمِیرُ الْمُؤْمِنِینَ (ع) فَقَالَ لَهُ یَا أَبَا عَبْدِ اللَّهِ هَذَا مِنْ ذَاکَ بَایِعْ! فَبَایَعَ وَ أَمَّا أَبُو ذَرٍّ فَأَمَرَهُ أَمِیرُ الْمُؤْمِنِینَ (ع) بِالسُّکُوتِ وَ لَمْ یَکُنْ یَأْخُذُهُ فِی اللَّهِ لَوْمَةَ لَائِمٍ فَأَبَى إِلَّا أَنْ یَتَکَلَّمَ»؛
“An karBo daga Ali Dan Hakam daga Saifu Dan Umairu daga Baban Bikri bahadhrame, ya ce: Abu Ja”afar  (a.s) ya ce dukkanin mutane sun yi ridda bayan Manzon Allah (s.a.w) in banda mutum uku, Salman da Abuzarri da MiKdad, ya ce sai na ce Ammar fa? sai ya ce: ya kasance ya raurawa sanna ya dawo, idan kana nufin wanda be yi shakku ba wanda shi ne kuma wani abu bai raurawar da shi ba to MiKdad ne, amma Salman ya kasance yana ganin cewa Imam Ali na da sunan Allah mafi girma wanda da ina ma zai roki Allah da shi, da kasa ta kamasu sun halaka baki Daya, kuma haka ne. amma Abuzarri haKiKa Imam Ali ya umarce shi da ya yi shiru (saboda tausaya wa a gare shi ba bisa umarni ba), domin ya kasance ba ya jin tsoron zargin mai zargi kal lamarin Ubangiji , sai ya Ki ya yi shiru ya ci gaba da magana”. [1]
La’akari da yanayin da musulunci ya ke ciki a farkon kira, na kasancewar sa sabon kafawa kuma sabon addini, wamda ke kewaye da haDurra masu yawa, na daga abokan gaba na cikin gida da ma na waje, waDannan dalilai zasu iya zama sirrin da ya sa Ahlulbaiti suka yi wa wasu daga  cikin sarakuna shiru, kuma wannan ne ma yasan Salman da Ammar suka yi aiki tare da hukamomi abin da ya fi wannan shi ne hidimar da Imam Ali (a.s) ya gabatar da temaka wa halifofi zai kusanto da wannan mahangar.  Da wani yaren bisa la’akari da yanayin da musulunci ke ciki da kuma kokarin kare wanzuwarsa da bada gudun mawa wajen cigabantar da shi, ba abin da zai hana Imam ma’asumi ya yi aiki tare da halifofi,[2] kumar yanda Salman da Ammar ma sun karBi matsayin gomnoni a garin Mada’in da Kufa da izinin Imam Ali (a.s).[3]
 
 

[1]. Kashshi, Muhammad  bini Umar, ikhtiyari ma’arifatul rijal, shafi 11, muassasr nashri danashgah, mashhad, bugu na Daya shekara ta 1409. Shekh mufid, al-ikhtisas, wanda aka yiwa tahKiKi aka gyara, gaffari, Ali akbar, muharrami zirnadi, Mahmud, Mahmud, shafi na 10, mu’atamarul alami lil’alfiyati shekh mufid, Kum, buga na daya, 1413.     
[2]. Saboda haka ne ma Imam Ali (a.s) yake cewa “zan sallama matuKar al’ummar musulmai zasu sallama kuma ya zama ba wanda ake zalunta sai ni kaDai” nahjul balaga, tarjamar Dashti, Muhammad  khuDba, ta 74, shafi na 122 -123; da ibni abinl hadidi j 6 sh 166; subhi salih, 102.
[3]  La’akari da yanda waDannan manyan suka sallama wa Imam Ali (a.s), yana da marukar wahalar gaske a ce sun karBi waDannan manyan ayyuka na hukuma ba tare da izinin Imam Ali (a.s) ba.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

 • Shin Shedan (Iblis) daga mala'iku yake ko aljanu?
  25510 Tafsiri 2012/07/24
  Akwai sabani mai yawa kan cewa shedan aljani ne ko mala'ika, da mahanga daban-daban. Asalin wannan sabanin yana komawa zuwa ga halittar annabi Adam (a.s) ne yayin da Allah ya ba wa mala'iku umarnin su yi sujada sai dai shedan ya ki yin sujada.
 • Tarihin Adam (as)
  18102 2019/06/16
  Amsa Filla-Filla: bayani kan rayuwar wasu nau”in mutane da aka fara halitta a bayan kasa, da kuma sanin shekara nawa kenan da halittar su zuwa wannan zamani da muke ciki? To hakika babu wata aya da ta yi bayanin hakan cikin kur”ani. Allama daba”ba”i cikin tafsirinsa na ...
 • mene ne ma’anar Takawa?
  15624 Halayen Nazari 2012/07/25
  Takawa wani karfi ne cikin ruhin mutum mai tsawatarwa da hana shi aikata ayyukan kuskure, kamalar takawa na kasancewa in an hada da nesantar abubuwan haramun, kamar nesantar shubha. Kuma ita Takawa tana da marhaloli da rabe-rabe, da kuma alamomi, zamu bijiro da su a jawabi na ...
 • Illolin wasa da azzakari, manyan zunubai, wankan janaba, dalilan haramci
  82954 2019/06/16
  Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...
 • ya zamanin hallitar annabi Adam (a.s) kusan shekaru 5764 a baya zamu kwatanta su da kasusuwan da a ka samu na mutanen da suka rayu sama da {shekara miliyan 25}?
  14076 Tafsiri 2019/06/12
  : ba wani matsala tsakanin wadannan abubuwa biyu. In da za a ce hallitar Adam yana kamawa kusan shekaru dubu shida ko bakwai da suka wuce. mai yiyuwa ne a nan ana nuni da cewa sabuwar hallitar mutum ne, don haka ba mamaki kafin wannan lokaci an ...
 • mece ce mahangar musulunci a kan samuwar halittu masu rai a sauran duniyoyi?
  10412 Tafsiri 2012/07/24
  Akwai tunanin cewa a cikin sauran duniyoyi shin za a samu halittu masu rai ko hankali, daya daga cikin tambayoyin da dan Adam ke neman bayanin su, amma har yanzu bai samu ba. Wasu bayanai a Kur’ani na nuni da samuwar wasu halittu masu rai a duniyar ...
 • Shin zai iya yuwuwa a kai ga martabar ubangijintaka?
  7716 Irfanin Nazari 2012/07/25
  Makamin matsayin ubangijintaka yana da matakai da marhaloli mabambanta, kuma don a samu wannan amsar dole ne a ga dukkan martabobi da ma’anonin baki daya. Idan abin da ake nufi da kai wa matakin ubangijintaka shi ne zatin mutum ta canja da sauyawar abin halitta ya koma ...
 • me ake nufi da duniyar zarra
  9342 Tsohon Kalam 2012/07/26
  Duniyar zarra ko kuma duniyar alkawari, na nufin wani lokaci ko wata marhala ko mahalli ko kuma wata duniya ce wacce Allah ta’ala ya fitar da rayukan dukkanin mutane daga cikin tsatson Annabi Adam (amincin Allah ya tabbata a gare shi), a bisa kankanuwar sura sosai, kuma ...
 • Shin zai yiwu ai mana bayanin tafsirin suratu kausar?
  13183 Tafsiri 2017/06/17
  Suratu kausar sura ce da take da ayoyi guda uku, abin da ya fi shahara gun malamai shi ne an sauke ta a garin makka; sannan dalilin saukar ta shi ne yayewa manzon rahama (s.a.w) damuwar da yake ciki sakamakon mauta da gorin da wasu cikin kuraishawa ...
 • Shin addini ya dace da siyasa?
  11803 Sabon Kalam 2012/07/23
  Addini ya zo ne domin rabautar mutum har zuwa karshen duniya, don haka ba yadda zata yiwu ya kasance bas hi da wani mataki game da abin da al’ummar duniya take bukata daya hada da jagorancin hukuma. Ta wani bangaren kuma yanayin dokokin musulunci sun tilasata wajabcin ...

Mafi Dubawa