Please Wait
9497
Ta mahangar Kur’ani mutum halitta ce da yake fizguwa zuwa ga ubangjinsa bisa fidirar halittarsa, kuma yake da jawuwa zuwa ga jiki, wannan halittar tana jansa zuwa ga ilimi da sani da alherai, a daya bangaren jiki tana kiransa zuwa ga sha’awa da sharri. Rayuwar mutum wani fagen karo da jayayya ne tsakanin wannan fidirar ta halitta da kuma jiki. Idan bukatun jiki suka yi galba kan n afidirar halittarsa to sai ya yi kasa, kuma a mahangar kur’ani wannan mutumin ya samu karkata da kaucewa hanya ne kuma ya kauce daga asalin fidirar halittar da ta dace da shi, amma idan fidirar hlittarsa ta yi galaba kan dabi’arsa to a nan mutum zai zama ya kamta hanyar shiriya ne kuma ya bisa tafarkin daidai. A mahangar kur’ani da ruwayoyi mutum lokacin da yake zuwa wannan duniya ba shi da wani ilmi da sani, amma dai yana da fidirar halittar da Allah ya ba shi. A lokaci guda kuma yana da jawuwa zuwa ga jiki, a lokacin da ya samu kansa a wannan duniyar ne yake fara samun daukaka zuwa ga sani da ilimi kuma a wani bangaren yake fara samun bin dabi’ar bukatun jiki, wannan ce mahangar kur’ani game da mutum, kuma yana ganin wannan badinin guda daya a bayan bambance bambancen da mutane suke da shi.
Mahangar musulunci game da mutum, sai dai akwai tunani guda biyu game da hakikanin mutmu da za a iya kawo a nan: Na daya; cewar mutane abu guda ne da abin da yake daure bambanci a tsakaninsu ya hada wuri daya su ne ala’du da siyasa da zaman tare. Na biyu kuma shi ne maganar nan ta ra’ayin da yake ganin cewa mutane suna da bambanci a tsakainsu a kowane zamani.
Na farko shi ne ra’ayin da mafi yawan addinai da masu irfani da ma’abota mazhabobi daban-daban na ilimi suka yarda da shi, sai dai a kan bayanin yadda hakan yake ne suek da bayanai mabambanta da juna.
Na biyu kuwa shi ne abin da wasu ma’abota falsafa suak tafi a kansa, ta yadda suek ganin mutum wani halitta ne mai bin al’ada, kuma samun bambancin al’adu yana kaiwa ga bambancin mutane ne, don haka ne ma ake da sabon isdilahi game da mutum da ake cewa mutumin tsohon zamani, da mutumin sabon zamani, sai ya zama ana ayyana mene ne hakikanin mutum da la’akari da sabon canji[1] da ya faru a turai, ko gyaran addini[2], ko wayewar zamani[3], da suka haifar da canji ga dan adam.
Sai dai abin da ya samu canji a bisa gaskiay su ne alakokin da suek tsakanin mutane ba wani abu ba, ita kuwa halittar mutane tana nan kamar yadda dan adam yake tun asali. A bisa mahangar musulunci mutane a kaowane zamani, da kuma kowace al’ummu mabambanta suna samun canji ne kawai a nau’in alakokinsu da ala’adu da yanayin gargajiyarsu, amma su mutane suna da tarayya cikin kasancewar su hakikanin wani lamari guda daya da suka yi tarayya a ciki da aka fi sani da ‘yan adamtaka, kuma kur’ani mai daraja ya shaida da hakan, haka ma mazhabobin falsafar hikima da ilimin gwaje-gwaje (tajriba) sun tabbatar da hakan.
Ta mahangar Kur’ani mutum halitta ce da yake fizguwa zuwa ga ubangjinsa bisa fidirar halittarsa, kuma yake da jawuwa zuwa ga jiki, wannan halittar tana jansa zuwa ga ilimi da sani da alherai, a daya bangaren jiki tana kiransa zuwa ga sha’awa da sharri. Rayuwar mutum wani fagen karo da jayayya ne tsakanin wannan fidirar ta halitta da kuma jiki. Idan bukatun jiki suka yi galba kan n afidirar halittarsa to sai ya yi kasa, kuma a mahangar kur’ani wannan mutumin ya samu karkata da kaucewa hanya ne kuma ya kauce daga asalin fidirar halittar da ta dace da shi, amma idan fidirar hlittarsa ta yi galaba kan dabi’arsa to a nan mutum zai zama ya kamta hanyar shiriya ne kuma ya bisa tafarkin daidai.
A kur’ani an kawo wasu abubuwa na tarayya tsakanin dukkan mutane ne, ko a matsayin kyawawan halaye, ko a matsayin munanan halaye, ba a tabbatar da kowannen ga mutum ba, sai dai an kawo cewa mutum yana da wani yanayi na halitta da zai iya siffantuwa da duka kowane janibi na halaye ne. a wani wuri an yi nuni da wannan nau’in halitta da ya kira ta da fidirar da Allah ya dora mutane a kanta[4], wani wurin ya yi nuni da cewa mutum yana da gaggwa[5] ne. wani wuri ya yi maganar halaye na gari na mutum wani wurin ya yi maganar muannan halaye na mutum. Wani wurin ya ambaci fidirar halitta ga mutum, wani lokcin sai ya ambace shi da siffofi na rashin hakuri, ko rashin karfi, da kwadayi, kuma duk wadannan siffofi ba su tare da mutum tun farko ba kyakkyawa ba mummuna. Sai kur’ani ya yi nuni da irin wannan a fadinsa cewa: “Allah ne ya fitar da ku daga cikin uwayenku ba ku san komai ba” [6], a wata ruwayar an yi nuni da cewa kowane mutum yana fita daga cikin mahaifiyarsa cikin tsarki ne[7].
A mahangar kur’ani yayin da mutum ya fito wannan duniyar ba shi da ilmi ko sani sai dai yana da fidirar halittar Allah da ya yi masa a lokaci guda yana da abin da yake fizgar sa zuwa ga biyan bukatun jikinsa. Sai a lokacin da mutum ya shiga wannan duniyar ne ya fara motsawa don kamala sai ya samu fadawa cikin wadannan abubuwan biyu, ko ya jawu zuwa ga daukaka ya fara sani da ilimi ko ya fizgu zuwa ga kasa. Wannan kuwa shi ne hangen kur’ani game da mutum.
Amma mazhabobin falsafa tun lokacin yunan zuwa yau da na yammacin duniya duk sun tafi a kan hakan cewa mutane iri daya a dabi’ar halittarsu ta fidira.
Zai iya yiwu nau’in hangen da ake yi wa mutum ya kasance a matsayin shi alheri ne a samuwa a bayanin halittarsa da fidirar samuwarsa kamar yadda musulunci ya yi bincike a kai, zai kuma yiwu ya kasance an samu kallon mutum a wata mahanga da take nuna shi a matsayin samuwar sharri ne shi kamar yadda kiristanci ya nuna shi. Sai dai idan ana maganar nau’in halittarsa a dunkule duk suan da imani da cewa muatne suna da nau’in halitta iri daya ne.
Karin bayani:
1. Mahdi Hadawi tehrani, wilayat wa diyanat, cibiyar al'adu ta Khaniye Khirad, Kum, bugu na biyu, 1380.
2. Mahdi Hadawi tehrani, bawarho wa fursish’ho, cibiyar al'adu ta Khaniye Khirad, Kum, bugu na daya, 1378.
[1] Renaissance
[2] Reformation
[3] Enlightenment
[4] Rum: 30.
[5] Ma’arij: 19.
[6] Nahl: 78.
[7] Kafi: j 2, s 12, h 4.