Please Wait
15752
An ambaci fuskokin gajiyarwar (kalu balen) da Kur’ani mai girma ya yi wadda zai yiwu na ambaci uku daga ciki:
- Ya gajiyar ta bangaren yare da bayani
- Ya gajiyar da fuskacin abin da ya kunsa
- Sannan kuma ya gajiyar ta fuskacin abin da ya zo da shi.
Amma gajiyarwar (kalu balen) da ya yi ta bangaren bayani da lafazi (yare) ya kasu gida biyu:
(A) Gajiyarwar (kalu balen) sa tabangaren balaga:
Tabbas salon bayani na Kur’ani to fuskar rashin iya gogayyar kowane irin zance na mutum ko waye shi kai har ma zancen Manzon Mafi Grima tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ta yadda ba a iya gwada shi da zancen Kur’ani, a nan ne ma da suke ba da kariyarta suka yi raddi game da abin da wasu sashe suke fada domin ba da kariya na tunane tunanen nan na cewa an hana rubuta sunna ne don hujjar cewa don a kange Kur’ani mai girma ne daga cakuduwar sa da waninsa.
(B) Gajiyarwar (kalu balen) ta Fuskacin Adadi:
Duk da ci gaba mai abin mamaki da aka samu a duniyar fasaha da kuma fisga nan take da aka samu a duniyar kwamfiyuta, duk da haka, masu bincike sun sami damar cin karo a kan wata alaka ta adadi na lissafi a tsakanin lafazan Kur’ani da kalmomin sa da kuma harufan sa, wadda zai yiwu ta kowane hali daga cikin halaye da za a ce kirkirar tunanin Dan Adam ne.
2- Gajiyarwa sa ta fuskacin abin da ya kunsa:
A wannan kason na gajiyarwa zai iya yiwuwa mu kasa shi zuwa wani adadi na kashe kashe:
- Rashin samun sabani a cikinsa
- Ba da labarin gaibu game da wasu sashe mutane da abubuwan da sukan faru wadanda suka tabbata dai-dai da yadda ya ba da labarin da kuma yanayi na karshe.
- Ta fuskacin ilimomi da sannai na Kur’ani, wanda shi Kur’anin ya kunshi wasu ilimomi da sannai da a zamanin da wahayi yake sauka a bisa mafi karamci takadiri (awo) ba zai yiwu dan Adam ya iya kaiwa garesu ba, su wadannan sannai sun kunshi wasu kiwaye masu zurfi na sufanci da falsafa (hikima) da kuma bincike bincike na hankali da makamantansu.
- Gajiyarwar (kalu balen) sa ta bangaren tabbatuwar wasu ilimomi da sannai na Kur’ani da rashin lalacewar da bacewar su duk da wadannan shekaru da karnoni masu tsawo da ya dauka.
3- Gajiyarwar (kalu balen) sa ta bangaren abin da ya zo da shi:
Tabbas Manzo mafi girma tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, ya kasance mutum Ummiyi (wanda bai koyi karatu da rubutu daga wani ba), sannan an tayar da shi ne a yanayi na jahiliyya wanda ya nisanta nisanta sosai game da ilimomi da sannai, amma tare da haka ya zo da wannan littafi mai nagarta to shin zai iya yiwuwa ga mutumin da yake ummiyi kuma a cikin yanayi mafi ci baya a ilimi da wayewa shi a kashin kansa ya iya zuwa da irin wannan littafi wanda ya gigita hankula da zukata?!! Kai tsaye ba zai yiwu ba.
An ambaci wasu fuskoki masu yawa na gajiyarwar (kalu balen) da Kur’ani mai girma[1] yake da su, wadanda zai iya yiwuwa mu rarraba su zuwa kashe uku:
- Gajiyarwar (kalu balen) sa ta fuskacin bayani da yare
- Gajiyarwar (kalu balen) sa ta fuskacin abin da ya kun sa
- Gajiyarwar (kalu balen) sa ta bangaren abin da ya zo da shi
- Gajiyrwarsa ta bangaren harshe da kuma bayani
Bincike game da gaijiyarwar da Kur’ani mai girma ya yi ta fuskacin harshe ya auku ne ta fiska biyu:
1- Gajiyarwar (kalu balen) sa ta fuskacin balagarsa da kuma kididdiga
Sannan tabbas bincike game da gajiyarwar (kalu balen) da Kur’ani Mai girma ya yi ta fuskacin balaga ko balagar Kur’ani yana daga cikin bincike-bincken da a kai ta Karin haske a kan sa tun zamunan baya kuma aka san hakan tun karnoni masu yawa, wadda zai yiwu mu ce yana daga cikin matsalolin da tuni aka fadaka da su aka kuma yi ittifaki a kan su, ta bangaren dukanin mazhabobin musulunci. Haka abin yake cewa a kwai wadanda suka bambance tsakanin al’amarin gajiyarwar (kalu balen) sa ta bangaren balaga da kuma wasu al’amurorin daban, kamar a tsari da salon sa da bayani suka ce: Daya daga cikin fuskokin mu’ujizar Kur’ani shi ne gajiyarwar (kalu balen) sa ta bangaren balaga, ta daya fuskar kuma gajiyarwar (kalu balen) sa ta bangaren tsari da salon bayani. Masu magana daban kuma sun tafi a kan cewa gajiyarwar (kalu balen) tasa, hadin gamayya ne na balaga da tsari da kuma salo,[2] amma a bisa hakika wannan ta fuskancin yawaitawa ne a misali kawai, domin dukanin guraren da suka ta’allaka da salon a bayani na Kur’ani suna kamawa ne zuwa gajiyarwar (kalu balen) sa ta bangaren balaga. Wato ba abubuwa ne mabambanta ba.
Tabbas salon bayani na Kur’ani mai girma salo ne domin da ya gajiyar da dukannin dan Adam na ya iya zuwa da irin sa, har inda manzo mafi girma tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi duk matsayin da Madaukaki da ya kebanta da shi (s.a.w).
Karin bayani:- a kan haka shi ne: Ahlul sunna a cikin babi na “Tarihin Hadisi” sun yi da’awar cewa manzo mafi girma ya yi hani da ka da a rubuta hadisin sa da zantukan sa tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi kuma suka jingini hakan ga ruwayoyin da aka rawaito daga gare shi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi,[3] a yayin da suka ci karo da tambayar da zata zo na cewa: To saboda me ya yi hani da rubuta hadisin sa kuma me ye hikima a kan haka?
Daya daga cikin amsoshin da take sananniya a tsakanin su ita ce: Hanin da Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya yi game da ka da a rubtau hadisin sa domin yana jin tsoron cakuduwar hadisin sa da Kur’ani mai girma ne kawai. Amma Sheikh Mahmoud / Abu Rayya daya daga cikin masu bin diddigi na Ahlul sunnah kuma yana daga cikin Malaman Azhar ya yi raddi a kan wannan dalilin ba zai amsar da duk wani malami mai hankali ba. Sannan mai bin diddigi da nazari ba zai karbe shi ba. Allah ma sai dai in mun sanya hadisan suna daga cikin jinsin Kur’ani a balagar su, sannan kuma salon[4] su wajan gajiyarwar (kalu balen) irin nasa ne, wannan kuma yana daga cikin abin da babu wani mutum daya da ya yarda da haka har ma wadanda suka zo da ra’ayin. Idan mun kaddara cewa Manzon mafi girma tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi zai iya zuwa da abin da ya yi kama da Kur’ani da balaga, sai Abu rayya ya amsa yana mai cewa: “Ma’anar haka ita ce a wargaza mu’ujizar Kur’ani ke nan da kuma rusa ta a matsayin kallon da ake masa na wata ka’ida”.[5]
A kowane irin hali dai shi ne, mas’alar nan da da’awar an sami hani daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, duk da cewa ba hadisi ba ne da zuwan sa yake komawa gare shi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi din ba.
A kowane irin hali dai, mas’alar nan ta da’awar hana rubuta hadisi, kuma daga wurin Manzo Mafi girma tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi tare da cewa hadisin na sa da suka zo daga gare shi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ba wai maganganu ne gama-gari ba, na sun kasance fatawoyi ne da kalmomi na haske da shari’a, saman suke iya warware mafi yawan kulle-kulle da matsalolin al’ummar Musulunci wadda wannan daya daga cikin matsaloli na tushe da ke fuskantar masu tunani da malamai na Ahlul sunna, daga nan ne muka ga cewa su ‘yan shi’a tun tuni har kuma ya zuwa yanzu suna kore tunanin nan na hanin da aka ambata, suna ma ganin ta a matsasyin da’awa ce da ba ta da inganci sannan kuma ba ta da wani asasi a hakika.
Fuska ta biyu, na gajiyarwar (kalu balen) da Kur’ani ya yi ta bangaren harshe (yare) ita ce: Gajiyarwar (kalu balen)sa ta adadi, wadda an jefo wannan fuskar baya-bayan nan ne ba ya da ci gaba mai abin mamaki ya faru a fagen dabarin kayan lantarki na komfiyuta, yayin da aka gane dangantakoki na lamba ta musamman a tsakanin lafazozi da harfofin Kur’ani mai girma wadda ba zai yiwu hakan ya tabbata ba game da zance mutum ta kowane irin hali.[6]
2- Gajiyarwar (kalu balen) sa ta hanyar abin da ya kunsa: An ambaci wasu fuskoki na gajiyarwar (kalu balen) da Kur’ani ya yi ta nahiyar abin da ya kunsa zamu yi nuni ya zuwa gare su.
- Rashin samun sabani a cikin sa, maganar Allah Madaukaki ya yi nuni ya zuwa ga wannan hakika inda ta ce: “Shin ba za su rika yin kai-kawo a kan Kur’ani ba ne, da a ce daga wanin Allah yake da an sami sabani masu yawa a cikinsa”.
- Labarurruka ne gaibu: hakika Kur’ani mai girma ya ba da labarurruka game da wasu masifu da abubuwa da za su faru a nan gaba, bayan saukar ayoyi a matsayin dai-dai ku da ma a matsayin al’umma, kuma duk wadancan labarurruka sun tabbata a aikace, kamar labarin sa game da cin nasara da Musulmi za su samu a kan Rumawa bayan ‘yan wasu shekaru, da fadawar kisira a hannun Farisawa, inda maganar Allah ta zo a cikin Suratul Rum, “Alif Lamem, an ci nasara kan Rum… ba da dadewa ba, amma su ma bayan hakan za a ci nasara a kansu”.[7]
- Gajiyarwar (kalu balen) Kur’ani ta bangaren ilimomin da sannai: Hakika Kur’ani mai girma ya bijiro da wasu sashe na sakamakon ilimi ya kuma yi magna a kan su, kuma dukan su ba suna karkashin tunanin dan Adam ba ne, a dan karamin takadiri hakan kuma tun lokacin da ake sauko da sakon, kai dai-dai ne, a kwai wasu sashe na ilimomi da sannai na Kur’ani madaukaka wadanda dan Adam ya gaijya game da ya san su har ya zuwa yau, idan har ma ka ga ya sami massaniya a kan su to ya samu bayan labararruka da Annabi mafi girma da Imamai ma’asumai amincin Allah su kara tabbata a gare shi, a bayan sa ta hanyar shiryarwar su mai ci gaba suka ambata, ta yadda muka sami cewa wasu gungu masu yawa ne hadisan da suka zo daga gre su. Irin ruwayoyin nan da suka bijiro da wasu hikimomi na falsafa (hikima) da ilimin iya tunani, da ma wasu fagage na ilimin sufanci. A kowane irin hali dari da za mu kaddara cewa ga wani mutum da ya sami ikon tattaro dukkanin sannai na Kur’ani tare da faifaye su, ko da ko muna da yakini cikakke na cewa da can irin wannan bai saba faruwa ba, to wannan ba ya nuna samun gibi game da gajiyarwar (kalu balen) Kur’ani a abin da ya cancanta mai waiwaya mu gani shi ne tabbatar da wannan gajiyarwar da Kur’ani ya yi, ba wai saboda ga ta hannun wanda ya zo ba ne,. (wato Annabi) sai dai kai wadancan ilimomi da sannai na Kur’ani masu zurfi madaukaka, da suke kasancewa suna da wani matsayi mai girma ta yadda suka fifici kowacce irin kwakwalwa da tunani a wancan zamanin a dunkule su ba wai kirkire-kirkire ba ne na mutum, su wasu sifofi ne da alamomi na wahayi.[8]
- Gajiyarwa game da iya wargaza sannai da ilimomi na Kur’ani: Abin lura shi ne, ita kwakwalwar dan Adam duk da wannan fadada da ci gaba da ilimi wadda ilimi ya kai zuwa gare shi, kuma duk da samun gamayyar ilimi da al’adu ko wayewa, tare da haka din dai dan Adam ya gajiya a gaban iya gabata tare da wargaza sannai na Kur’ani da ilimoninsa, wannan shi yake bayyanar da cancanta da fifikon tunane-tunanen Kur’ani mai girma a kan kowane irin tunanin dan Adam.
Tabbas zai iya yuwuwa a ce akwai wasu sashe na ilimomin dan Adam kamar lssafi da mandik wadda an tattara su an rubuta su a tsakanin bango-da-bango ina littattafi sannan kuma sun kai zuwa gare mu tun zamunan baya, amma ga su babu wasu canje-canje ko iya batawa da aka samu a kan su sama, wadda wannan alamarin yana iya ba ta da’awar da ta gabata, na zamowar fifikon can-cantar Kur’ani a kan kowane irin fagage na ilimoi. To za a iya bad a amsa a kan wannan waiwaye ta hangar al’amura masu zuwa.
- Su wadancan ilimomi sun kasance suna kai kawo ne a kewayen abubuwan da hankali zai iya fahimtar su nan take a matakin farko, kuma suna daga cikin abin da aka boye a fidirar (kwayar halittar) dan Adam, kowane mai hankali mai tunani, sannan su wadanda suka rubuta wadancan litattafan da ilimomin ba wai su ne suka kirkiri ilimomin ba, ga su ne dai suka hada su waje guda, kawai.
- Da ma yanayi na gaba daya shi ne, rabuce-rubuce da litattafan da aka wallafa ta fuskacin dan Adam, sun kasance ba kuma za su gushe ba suna kewayawa a kewaye daya sannan sun kebanci wani ilimi ne ayyananne mai fage daya a halinsa na daga cikin mafi kebanta tare da banbance-banbance da daukakar fuska da ilimomi da sannai na Kur’ani da kuma buwaya da yalwatar sa a kan sauran fagage da bincike-bincke na ilimomi da ma nune-nunen da yake da su a kan gomomin ababen nema kuma cikin kalma ko zance daya shi ne yana da kebantaka ta wannan gamewar da yake da ita. A bsia hakika wannan al’amari ana lissfa shi a matsayin wata fuska daban daga cikin fuskokin gajiyarwar (kalu balen) Kur’ani wanda a cikin abin da yake na nade na abin da ya kunsa shi ne irin wadancan nau’o’i na ilimi mabanbant, ta ina mutum zai iya zuwa da dukanin wadannan ilimomi da saman da suke da zurfafawa da tabbatawa da kuma shiga jiki da gamewa! Kuma rika samar da jonuwa tsakanin ilimomin ya damfara wasu tare da wasun su ta yadda za su haifar da kala-kala da abin ci mutane ta yadda zai samar da wani gibi ba, game da manufar zantuka, jerin hadisai da dacewar sa ba za su sami karo da juna ba, sannan babu wani kuskure a cikin sa, ga shi ya wanzu tsawon wadannan karnoni sai kara haske - haske sannan kuma an kare shi daga iya bata shi da gamsuwa da shi!![9]
3- Gajiyarwar (kalu balen) sa ta fuskancin abin da ya zo da shi; bincike ya gabta a wannan bangare na mu’ujizar Kur’ani tun lokutan baya, a inda wannan ra’a yi suka jinginawa Manzo tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, cewa mutumin da bai iya karatu da rubuta ba, to amma tambaya? Zai iya yiwuwa ga mutumin da yake bai iya karatu da rubutu ba (ummiyi) wanda ya rayu a wannan yanayi mai kaushi ko na ci baya a nahiyar Larabawa wadda ta nisanta daga fagen wayewa; ya iya zuwa da wadannan ilimoi da sannai madaukaka na ilimomi a kashin kansa daga aljihunsa, mutukar bai dogara da wata kudara boyayya ba wacce ita ce take tanadar sa da guzurin na dukanin wadancan ilimomi da sannai madaukaka ba?. [10]
Abin da ya kamata mu ambata shi ne yin bincike game da gajiyarwar (kalu balen) da Kur’ani yayin duk da ya zama yana daga cikin binciken da a bisa al’ada a kan bjiro da su a cikin abin da yake kunshe ne na bincike-bincike na ilimomin Kur’ani (Ulum-al-Kur’an), amma duk da haka a hakika, bincike ne na ilimin iya magana (ilmu al-kalam), daga nan muka sami cewa haka nan ana tattauna shi a cikin sashen litattafan ilmul-kalam.[11]
Wanda yake neman Karin bayani a kan haka ya duba: Mahadi Hadaawi tehrani, mabani kalami ijtihad, mu’assasai farhange khaniye khirad, Kum, buguwa ta farko 1377, Darul kur’an.
[1] Fuskokin gajiyarwar al’kur’ani na sayyid m ustafa khomaini shafi 167-178.
[2] Fuskokin gajiyarwar al’kur’ani na sayyid m ustafa khomaini shafi 169.
[3] Mahmud a bu rayya a cikin littafin adhwa’u alal sunnatuil muhammadiyya shafi na 42.
[4] Mahmud a bu rayya a cikin littafin adhwa’u alal sunnatuil muhammadiyya shafi na 46.
[5] Mahmud a bu rayya a cikin littafin adhwa’u alal sunnatuil muhammadiyya shafi na 47.
[6] Dakta sayyid ali kadiri ya samar da sgiryayyen shiri na ilimantarwa na komfiyuta a wannan fagen wanda ya ba wa suna (kaddara)
[7] Surar nisa’I aaya ta 82.
[8] Surar rum aya ta 1-3.
[9] Allama daba-daba’I ya ciro wannan zancen a kimanin waje 114, daga dukkanin litattafan ilimin alkur’ani wanda za a iya ciratowa daga dukkani surorin alkur;ani.
[10] Wasu daga cikin malaman yammacin dubiya sun yi raddin wannan da cewa ai annabi yana karatu da rubutu yana kai kawo tsakani malaman addinan yahudu da na nasara, sun dauka cewa ma’anar Kalmar “ummiyi” a laranci a bias ma’anar da ta zo a kur’ani bat a saba da ma’anar wanda baya kararu da rubutu ba.b suka fassara ta da ma’anar annabin “ummiyai” (wadanda basa karatu da rubutu)
[11] Hadawi dahrani a littafin mabani kalamiye igtihad, shafi na 47-51.