Please Wait
10475
Lalle shi shedan daidai gwargwardon yanda ya zo a cikin Kur’ani yana da zarafin da zai iya salladuwa a kan dukkanin ‘yan Adam face bayin Allah nan da aka tsarkake. Su wadanda aka tsarkake, su ne wadannan da suka kai ga manyan–manyan mukamomi ta yanda shedan ba zai taba samun wata kofar da zai isa gare su ba.
A nan muna bukatar wasu hanyoyi wadanda ba makawa, don samun kubuta a fagen fafatawar nan da shedan da rundunarsa, har mu iya yakar sa mu kuma yi nasara a kansa. Bari mu yi nuni ga wasu daga cikin su kamar haka:
Imani: Kur’ani yana la’akari da imani shi ne abu na farko kuma ginshiki domin dankwafe mamayar shedan.
Tawakkali: wani jigo daga cikin abubawan ake nasara a kan shedan da rundunoninsa shi ne tawakkali ga Allah tsarki ya tabbata a gare shi.
Tsari (isti’aza): shi ma’anarsa na nufin neman mafaka ga Allah madaukaki.
Ambaton Allah: domin shi ambaton Allah yana baiwa mutum basira kuma yana nesanta shi daga waswasi, ya kuma toshe kofofin da shedan ke bullowa ta cikinsu.
Tsoron Allah: samar da tabbatacciyar dabi’ar tsoron Allah da kuma inganta ta yana bude idanuwan zuciya a kan waswasin shedan, sannan kuma ya kare mutum daga afkawa cikin komar shedan.
Lalle shi shedan daidai gwargwadon yanda ya zo cikin Kur’ani, yana da zarafin da zai iya salladuwa a kan dukkan yan Adam sai dai bayin Allah wadanda aka tsarkake. Yayin da shedan ya yi rantsuwa a kan cewa sai ya halakar da mutane baki dayan su, sai dai wadanda aka tsarkake ‘’Ya ce, Ya Ubangiji tun da dai ka halakar da ni, to wallahi zan kawata musu barna a bayan kasa, kuma sai na halakar da su baki daya (1). ko kuma fadar Kur’ani mai girma, Sai ya ce; na rantse da girman ka sai na halakar da su baki daya. (2) Amma su mukhlasun (3)’’ wanda aka tsarkake su gwargwadon abin da wannan ayoyin su ka ce sun kubuta daga kangin shedan. Wannan tabbaci ne wanda Kur’ani ya bayyana kamar yanda shedan ya yi ikirari. Kuma Kur’ani ma ya fada cewa: Lalle bayina ba ka da wani iko a kansu, ubangijinka ya isa ya zama me wakilci’’ (4)
Hanyoyin gwagwarmaya da shedansu ne wadanda suka kai ga manya-manyan mukamai ta yanda shedan bashi da wata kafa da zai bi zuwa gare su. A nan muna bukatar wasu hanyoyi wadanda ake matukar bukatarsu don cimma nasara a wannan kokawar da shedan. Muna samunsu za mu iya yakarsa mu kuma yi nasara a kansa. Bari mu kawo kadan daga cikin su: -
- Kur’ani mai girma yana daukar imani a matsayin tubali na farko domin dankwafe mamayar shedan. Kamar yanda ya ce: ‘Yan da al’amarin yake shi ne bashi da iko a kan wadanda suka yi imani.5
- Wani ginshikin kuma daga cikin ginshikai masu sa a yi nasara a kan shedan da rundunarsa shi ne tawakkali: Allah ya ce lallai ba shi da wani karfi a kan wadanda suka yi imani, kuma ga Allah kawai suke yin tawakkali’’6 don haka imani da Allah mai girma da daukaka da ayoyin sa na hana biyayya ga shedan da kuma yadda da hukuncinsa a kan mutum. Ba shi da iko a kan wanda ya yi garkuwa da garkuwar imani kuma ya yi tawakkali ga Allah. Amma mulkinsa yana kan wanda ya karbi jagonrancinsa ya kuma hada Allah da wani ‘’abin sani kawai shi ne ikonsa na kan masu jibintar al’amarinsa, wadanda suka zama masu shirka da shi Allah’7
- Neman tsari: ma’anar sa neman mafaka a wajen Allah (s). ita wannan mafaka wani lokacin tana iya zama ta dabi’a ko kuma ta shari’a. Idan muka tunkude abubuwan sharri na dabi’a neman tsari zai tabbata a gare mu wanda yake daga cikin mafaka na dabi’a na Allah (s) wannan na nufin dukkan tsare-tsare, da al’adun ubangiji wacce aka sanya a cikin tsarin hallita. Ta hanyar sababi da tasirin dabi’a. Kuma har-wala-yau in aka kare kai daga sharrin zuciya za a sami fa’ida daga mafakar shari’a. Kamar yanda Allah ya ambata a cikin surar (Nas’’ wanda yake nuni ga koyarwar Allah tabbataciya a shari’a mai tsarki bisa tsari irin na ikida da kuma salo irin na tarbiya ‘’idan wani dan tunani mara kyau ya same ka daga shedan to, ka nemi tsari daga Allah shi mai ji ne kuma masani’8 shi tauhidi yana hukunta wa mutum neman dauki daga Allah (s) don samun amfani da alheri ta hanyar fara ayyukansa da ambaton Allah. Kuma ya nemi daukinsa don tunkude cuta da sharri, ta hanyar fara ayyukan sa da cewa ‘’a’uzubillahi’’ saboda hakika babu mai tasirantuwa sai Allah shi kadai a dukkan duniya. Kamar yanda ya tabbata a cikin tauhidi.
- Ambaton Allah: shi ambaton Allah yana taimakawa dan Adam da basira, ya kuma nesanta shi daga waswasin shedan, ya kuma toshe kofar da shedan zai isa dagare shi. Allah ya ce lalle wadanda suka yi takawa idan wani abu daga shedan ya shafesu, sai su ankara (tunawa) sai ka ga har sun fadaka (10) imam Al-Sadik (as) ya ce: shaidan bai samun ikon sanyawa mutun wasiwasi face sai idan ya bijirewa ambaton Allah (swt) sai kuma ka ga har su fadaka (12).
‘’Ta’if’’ shi ne kewaya gefen abu, to kamar yan da waswasin shedan yake kewayewa a gefen ruhin dan Adam da tunaninsa ba kakkautawa don ta sami hanyar kutsawa cikinsa. To haka nan shedan ba zai iya yin wani tasiri ba a kan ruhi mai karfin imani da kuma takawa. Amma fa koyaushe yana nan yana dakon wata dama wacce ta dace da shi sai ya watsa wasu sashen soye-soyen rai, kamar sha’awa da fushi da hassada da ramuwar gayya, har sai ya samu ya kutsa cikin sa domin kawai ya batar da shi.
Wasu hanyoyin daban masu amfani don tunkude makircinn shedan su ne: ambaton ahlul-bayt (as) da kyautatawa masoyinsu. Da dagewa don kaiwa ga matsayin wadanda shedan bai iya cimmasu da sauransu.
Sakamakon wannan binciken; lalle kudurce samuwar Allah (swt) mai kariya ce kuma mai fadakarwa ce sosai, tana taimakon mutum ta kuma kare shi daga sabo da zunubi. Haka nan ma fadakuwa game da girman Allah da hikimarsa da juyar da al’amura ga zatinsa mai tsarki tana zaburtarwa ga ruhin bawa cikin fito-na-fito dinsa da shedan. Tare da cewa karfafa imani da tawakkali, da kuma takawa, gami da ambaton Allah ko da yaushe, da kuma zuwa da ayyukan da ke jawowa da korar shedan. A karshe neman tsari na hakika a lokacin da aka hadu da sharri da barna ta fuskacin shedan. Dukkan wadannan ana daukarsu a matsayin matakai masu tasiri da fa’ida wajen kare kai daga kutsowarsa.
Abu muhimmi da zamu fada a karshe shi ne duk abin da aka ambata, zai yiwu ya tabbata ta fuska mafi kammala ta hanyar yin tawassuli da ahlul-bayt (as) da kuma kulawa da su da fuskantarsu.
Maudu’ai masu alaka da hanyoyin da shedan ke kutsawa cikin mutum 987 (mauki: 1051
Manufofin da shirye-shiryen shedan, 1144 (mauki: 1777)
- Alhijr, 39
- Surar Sad, 82
- Mai yin lkhlasi shi ne wanda ya karkade ruhinsa daga kulli da algushu hna dabi’a, da kuma al’amuran dukiya, ya kuma tsarkake ransa daga duk abin da ba Allah, ya kuma cika shi da sonsa.
- Surar israi.65
- Surar nahl, 99
- Surar nahl, 99
- Surar nahl, 100
- Surar a’araf, 200
- Surar fussilat, 36
- Surar a’araf, 201
- Al Muhaddith-al-Nuriy, Mustadrak-al-Wasa’il, juz1 sahfi178, mu’assasatu alul bayt, kum. 1404 kamari; almajlisi Muhammad bakir, behar-al-anwar, juz72 shafi124 mu’assasat al-wafa, Beirut, 1404 kamari
- Al Amudi, al-Tamimiy, Abdulwahid, Gurat-al-hikan.wadurrar-al-kalim. Shaafi188, maktaabat-al-islamiy, kum.1366, shamsi.
- A’araf, 201