Please Wait
Dubawa
4963
4963
Ranar Isar da Sako:
2013/06/18
Takaitacciyar Tambaya
Cikin kissoshin addini game da kissar kashe kananan yaran cikin banu isra\'ila da ya zo daidai da haihuwar Annabi Musa (a.s) wanda muka ji labari kamar yadda kur\'ani karara ya bayyana cewa umarnin da fir\'auna ya bayar kan kashe wadannan kananan yara, shin ya samo asali ne bayan annabtar Musa (a.s)?
SWALI
Shin a wane lokaci Fir\'auna ya bada umarni kashe yara maza daga `ya`yan banu isra\'ila? Ciki kur\'ani mun karanta na\'uka biyu na kisan, nau\'in kisa a lokacin da musa ya riga ma ya zama Annabi har ma ya fara bayyanawa fir\'una sakon Allah gareshi cikin suratu gafir ayab ta 23-25 (hakika mun aiko musa da ayarmu da wani dalili mabayyani ya zuwa Fir\'auna da hamana da karuna sai suka ce mashi kai matsafi ne makaryaci* yayin da ya zo musu da gaskiya daga gare mu sai suka ce ku kashe `ya`yan wadanda sukai imani tareda shi.....) nau\'i na biyu shi ne ko dai lokacin da musa ya kasance jariri kamar yadda ya zo cikin suratu daha aya ta 38-39?
Amsa a Dunkule
Fir'auna sau biyu ya bada umarnin kashe kananan yaran banu isra'ila
1 na farko shi ne lokacin da aka haii Annabi Musa (a.s) ya bada umarnin kashe yara maza don ya takawa rayuwar Annabi Musa (a.s) birki.
2 na biyu kuma ya kasance bayan Annabi Musa (a.s) ya zama Annabi, gargadar Fir'auna da musa ya yi kan kisan `ya`yan banu isra'ila da fir'una yake yi domin raunana su.

Amsa Dalla-dalla
Bisa abin da ya zo daga ayoyin kur'ani zamu samu cewa Fir'auna karo biyu ya bada umarnin kisan kanan yara maza na banu isra'ila sai dai cewa kowanne umarni daga cikin biyun nada kebantaccen dalili mai cin gashin kansa.
1 na farko ya kasance sakamakon labarin da masana ilimin jujjuyawar taurari da falaki sun ba shi labarin cewa za a haii wani yaro cikin banu isra'ila wanda wannan yaro zai zama babbar barazana gare shi da mulkinsa, shi kuma Fir'auna a yunukurin na kaucewa da kauracewa afkuwar hakan sai ya bada umarnin kashe duk wani jinjiri na miji da aka haifa cikin banu isra'ila[1]
Duk da cewa cikin kur'ani bayanin kisan bai zo karara ba, sai dai cewa musulmai ba su da abani kan wannan kissar sun rungume ta hannu bibiyu ; saboda haka malaman tafsiri su ka yi takaitaccen bayani kissar karkashin ayoyi da sukai ishara zuwa ga kissar, sannan suka karkata da riwayoyin da su ka yi bayanin kissar daya daga cikin ayoyin da sukai ishara ita ce wannan aya kamar haka:

«أَنِ اقْذِفيهِ فِي التَّابُوتِ فَاقْذِفيهِ فِي الْيَمِّ فَلْيُلْقِهِ الْيَمُّ بِالسَّاحِلِ يَأْخُذْهُ عَدُوٌّ لي وَ عَدُوٌّ لَهُ وَ أَلْقَيْتُ عَلَيْكَ مَحَبَّةً مِنِّي وَ لِتُصْنَعَ عَلى عَيْني»
Ki wurga shi cikin akwatu sannan ki jefa cikin koramar nilu koramar za ta cillashi bakin gabar ta sannan makiyi na wanda yake kuma makiyin sa zai dauke shi na jefa maka soyayya daga gareni kuma domin a tarbiyantar da kai kan kulawata kan ido na.[2]
Bisa abin da malaman tafsiri suka tafi kai shi ne kiyayyar Fir'auna ga Allah ta fito fili karara a kur'ani kamar yadda Allah ke faddi cikin ayar (makiyi na) sakamakon da'awar allantaka da Fir'auna ya yi wa kansa sannan kiyayyarsa da Musa (a.s)[3] ta samo asali daga kisan jarirai maza kamar yadda bayanin hakan ya gabata, sannan awata aya kuma anyi ishara da wannan kissa kamar haka:
Munyi wahayi zuwa ga mahaifiyar musa da ki shayar da shi idan kuma kinji tsoro a kansa to ki jefa shi cikin kogi ka da ki tsorata kar ki yi bakin ciki lalle mu masu dawo muki da shi ne zaku ma mu sanya shi daga ckin manzanni.[4]
Cikin wannan aya cikin Kalmar (idan kika ji tsoro game da shi) ishara ce kan kisan da fir'auna ke yiwa `ya`ya maza na banu isra'ila, ba'arin malaman tafsiri cikin karashen wannan aya da Allah ke cewa (hakika mun yi wani ihsani gare ka a wani lokaci dabam)[5]

«فَإِذَا خِفْتِ عَلَيْهِ» «وَ لَقَدْ مَنَنَّا عَلَيْكَ مَرَّةً أُخْرى»
Ma'anar Kalmar (mun yi ihsani da baiwa gare ka) shi ne ceto shi da Allah daga kisan Fir'auna yayin da aka haife shi.[6]
2. Fir'auana a karo na biyu bayan wancan da ya gabata ya kara bada umarni kashe `ya`ya mazan banu isra'ila wanda hakan ya kasance bayan annabtar Musa (a.s) da bayyanar wasu adadin mu'ujizozi daga musa (a.s) kur'ani ya yi bayani afkuwar hakan a sarari kamar yadda zamu gani cikin ayar da zato zo:

«فَلَمَّا جَاءَهُم بِالْحَقِّ مِنْ عِندِنَا قَالُواْ اقْتُلُواْ أَبْنَاءَ الَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُ وَ اسْتَحْيُواْ نِسَاءَهُمْ وَ مَا كَيْدُ الْكَافِرِينَ إِلَّا فىِ ضَلَلٍ».
Yayin da ya zo musu da gaskiya daga gare mu sai suka ce ku kashe `ya`yayen wanda su ka yi imani tare da shi suka raya matansu kaidin kafirai bai bakin komai face bata.[7]
Manufar fir'auna cikin wannan umarni da ya bayar na kashe kananan yaransu maza[8] shi ne raunana banu isra'ila kai wannan karan fir'auna bai wadatu da kashe yara maza ba kadai ya ma bada umarni da a raya `ya`ya mata daga banu isra'ila domin su yi hidima gare shi da fadawansa.[9]
A cikin wata ayar Fir'auna ya bada wannan umarnin kamar na baya sai dalilin ya fi bayyana a ayar da ta gabata
«وَ قَالَ المْلَأُ مِن قَوْمِ فِرْعَوْنَ أَتَذَرُ مُوسىَ وَ قَوْمَهُ لِيُفْسِدُواْ فىِ الْأَرْضِ وَ يَذَرَكَ وَ ءَالِهَتَكَ قَالَ سَنُقَتِّلُ أَبْنَاءَهُمْ وَ نَسْتَحْىِی نِسَاءَهُمْ وَ إِنَّا فَوْقَهُمْ قَاهِرُونَ».
Sai manyan daga mutanen fir'auna suka ce yanzu ku zaka zura wa musa ido da mutanensa su yi barna cikin kasa ya watsi da kai da ubangijanka sai ya ce; da sannu zamu kashe `ya`yansu maza mu raya mata daga `ya`yansu lalle mu ke da buwaya kansu.[10]
Bisa haka zamu fuskanci cewa Fir'auna ya bada umarni kashe `ya`yan banu isra'ira karo biyu, na farko gabanin haihuwar Musa (a.s) na biyu kuma bayan an ba shi annabta.[11]
Bisa haka zamu fuskanci cewa Fir'auna ya bada umarni kashe `ya`yan banu isra'ira karo biyu, na farko gabanin haihuwar Musa (a.s) na biyu kuma bayan an ba shi annabta.[11]
[1] Mafatihul gaibi wallafar abu Abdullah muhammadu ibn umar fakrul dini razi juz 27 sh 506 bugun darul ihya'u turasul arabi bairut bugu na uku shekara 1420
[2] Suratu daha aya 29
[3] Intisharatul islamiya kum bugu na biyar shekara 1417 hijra kamariya iAlmizan fi tafsirul kur'an wallafar muhamamd husaini tabataba'I juz 14 sh 150 bugu daftar. Atyab bayan fi tafsiril kur'an wallafar sayyid abdul husaini juz 9 sh 30 bugun intisharatul islami Tehran bugu na biyu shekara 1378 hijra shamsiy.
[4] Kasas aya 7
[5] Daha aya 37
[6] Kur'an wallafar sayyid Muhammad husaini fadlullahi juz 15 sh 108 bugun darul malak liltaba'a wannashri bairut bugu na biyu shekara 1419 hijra kamariyya. Tafsirul min wahayul
[7] Gafir aya 27
[8] Wallafar muhammadu ibn umar fakrul razi juz 27 sh 506. Majma'ul bayan wallafar fadalu ib hassan dabarasi.mukaddimatul balagi wallafar Muhammad jawad juz 8 sh 809 bugun intisharatul nasir kosro Tehran bugu na uku shekara 1372 hijra shmasiyya. Mafatihul gaibi
[9] Majma'ul bayan juz 8 sh 809
[10] A'araf aya 127
[11] Tafsirul jawami'il jami'I wallafar fadau ibn hassa dabarasi juz 4 sh 8 bugun jami'ar Tehran, idarar hauzar ilimi da ke birnin kum mai tsarki bugu na farko shekara 1377 hijra shamsiya. Tafsiril amsal wallafar ayaatullahi al'uzma nasir mukarimul shirazi juz 20 sh 76-77 darul kutubul islamiya bugun farko shekara 1374 hijra shamsiya
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga