advanced Search
Dubawa
10958
Ranar Isar da Sako: 2006/05/31
Takaitacciyar Tambaya
Me ye alaka tsakanin Zuhudu da ci gaban zamani?
SWALI
Mece ce alaka tsakanin kalmar Zuhudu da saukin rayuwa, da kuma ci gaban rayuwa da zamani, wai shin akwai wani sabani tsakaninsu ta yadda zamu karbi zuhudu da saukin rayuwa, ko kuma mu karbi rayuwar walwala mu watsar da zuhudu?
Amsa a Dunkule

Kalmar zuhudu da saukin rayuwa suna daga kamalar halaye, wanda ya koma zuwa ga littattafanmu na shari'a zai samu cewa sun muhimmantar da wannan kalma da yawa, kuma sun karfafa ta sosai, suna masu nuni da kwadaitarwa da rashin damfaruwa da duniya da adonta, sai dai abin takaici an samu wuce gona da iri, ko gazawa a cikin wannan lamarin -a tsawon tarihi- a bayanin zuhudu da rashin la'akari da sunnar annabi (s.a.w) da tarihin imamai (a.s) kan wannan lamarin, al'amarin da ya kawo mana bata surar ma'anar zuhudu da saukin rayuwa, imam kazim (a.s) ya fada yana mai nuni da wannan lamarin na wajabcin tsakaitawa tsakanin rayuwa da daidaito a mahangar rayuwa da addini da nau'in rayuwa:

"Wanda ya bar duniyarsa don addininsa, ko ya bar addininsa don duniyarsa, ba ya daga cikinmu".

Sannan da zamu duba addinai baki daya da mazhabobi ba zamu taba samun kamar addinin musulunci ba wurin kwadaitar da mabiyansa kan ci gaba da neman sani da neman abin rayuwa, da kokari na tunani a yin rayuwa.

Wannan lamarin haka yake a fili yake a cikin littattafan addini, don haka ne zaka samu musulunci yana kwadaitar da ci gaba da wayewar zamani a wurare masu yawa, kuma wannan lamarin ne da yake cike da hasken tunanin musulunci. Sai dai wannan lamarin da muke ganin na kwadaitarwa kan samun ci gaba da wayewar zamani da tsayar da tilasata ko dora ta kan tafarki da tsofaffin al'adu, ba yana nufin cewa musulunci ya kwadaitar da sanya rayuwa kan tafarkin wayewar turai maras ma'ana da ake nufi a yau ba.

Sannan yana daga abin da yake muhimmi mu sani a nan shi ne: Daukakar da musulunci yake kwadaitarwa a kanta a yau, tana daga nau'in da ba ya sanya mutum ya zama bawan sha'awa da holewa da bin abin da ransa take so, sai dai yana kokarin ganin ya 'yanta mutum daga ribacewar sha'awa da son rai ne ma.

Amsa Dalla-dalla

Musulunci ya bayar da kula ta musamman ga ma'anar zuhudu da saukin rayuwa, kuma littattafan addini masu yawa sun yi bahasi da kwadaitarwa kan wannan lamarin na zuhudu a duniya, da nisantar adon duniya da kawayenta, da rashin karkata da bin sha'war duniya da son rai na karkata zuwa ga duniya, don haka ne ma kur'ani ya yi magana da cewa:

"Kada ka sanya idanuwanka ka kwallafa ranka zuwa ga abin da muka jiyar da su dadi da shi mataye daga gare su, kawar rayuwar duniya ce domin mu fitine su a cikinta, kuma arzikin ubangijinka shi ne ya fi kuma shi ne mafi wanzuwa"[1].

Daya daga cikin masu tunanin musulmi yana fada game da wannan lamarin cewa: “Hakika adon duniya da jin dadinta ba ya karar kowa, domin wannan duniyar tana da tsananin sanyi, kuma duk sa’adda furen rayuwarta suka so su bayar da ‘ya’yan itaciya sai wannan iskar mai sanyi ta zo ta watsar da su daga rassanta, ta sanya su kamar abin cikewa cikin iska” [2].

Ko da yake mun samu ra’ayoyi masu yawa da suka zo a tsawon tarihi da bayanai mabambanta game da zuhudu da takawa a matsayin daidaiku da al’umma, sai dai wadannan bayanai da suka zo a tarihi suna nuna mana yadda aka samu ko dai wuce gona da iri, ko kuma takaitata, wannan yana nuna yadda aka samu mummunar fahimta game da wannan ma’ana ta zuhudu a addini, kuma aka yi mata fahimtar kuskure. Sai dai abin da ya zo a sunnar ma’asumai da tarihin rayuwarsu an watsar da shi a wannan fagen, ba a nuna shi ga mutane ba, wannan lamarin kuwa shi ne ya sanya bata surar ma’anar zuhudu kyakkyawa da yake da shi na ma’anar zuhudu da saukin rayuwa, har sai da aka hada kalmar zuhudu da ma’anar komawa gefe, da kebewa wuri daya, da nisantar mutane, daga wayewa da ci gaban rayuwar duniya, da habaka, sai aka fahimci cewa yana nufin kiran mutane zuwa ga ibada da addu’a da kebewa da nisantar lamurran rayuwar duniya!!!

Wannan shi ne abin da yake fara zuwa tunanin mutum idan ya ji an ambaci kalamr zuhudu, sakamakon wannan mummunar fahimtar da aka yi wa wannan lamarin da ba a fahimce shi kamar yadda yake ba, a kan haka ne muka ga Imam Sadik (a.s) yana cewa: “Zuhudu da gudun duniya ba shi ne ka tozarta dukiya, ko a haramta halal ba, sai dai zuhudu gudun duniya yana nufin kada ka zama ka fi amintuwa da abin da yake hannunka fiye da abin da yake hannun Allah mai girma da buwaya” [3].

Daga Imam Ali (a.s) ya ce: “Dukkan zuhdu (gudun duniya) yana cikin kalmomi guda biyu na kur’ani. Allah madaukaki yana cewa: “Domin kada ku yanke kauna da bakin ciki kan abin da ya kubuce muku, kuma kada ku yi farin ciki da abin da ya zo muku”[4].

Ashe ke nan zuhudu da takawa suna nufin rashin damfaruwa da duniya da adonta, da kawayenta, da rashin damfaruwa da al’amuran duniya mai karewa da sauran kayan rayuwar duniya masu gushewa, da kusanci da mai mulki mai gaskiya ubangiji mai tsarki da daukaka, wannan lamarin kuwa shi ne zai kawo hutun rai da kwanciyar hankali, da samun sauki don daukaka zuwa ga samun kyawawar daukaka da rayuwar mutuntaka.

 

Idan mun san wannan sai mu tambaya cewa shin samun ci gaba da hadaka da koyar da mutum da tarbiyya ta hanyar amfani da ni’imomin Allah domin samun tsiran mutum ya saba da zuhudu da takawa, kuma zai hana samun su?

Da mun duba addinai da mazhabobi gaba daya ba zamu samu wani addini kamar na musulunci ba, wanda ya bayar da fifiko da daukaka ga ilimi da sani, muhimmanci mai yawa, kuma ya kwadaitar da neman ci gaba da daukaka, da ci gaban tunani.

Shin manzon Allah (s.a.w) bai ce: “Ku nemi ilimi ko da a kasar Sin ne” [5]. Kuma ya fada cewa: "Neman ilimi farilla ne a kan dukkan musulmi"[6].

An ruwaito daga Imam Ali (a.s) cewa ya ce: “Ilimi rayuwar zukata ne daga jahilci, kuma hasken gani ne daga duhu”[7].

Wannan bayani ne bayyananne a fili game da matsayin ilimi a musulunci da kuma nuni ga wulakantuwar duniya da damfaruwa da ita.

Amma game da alaka tsakanin addini da ci gaba ya kamata ne mu ce: Abin la’akari a duk fadin tarihin musulunci cewa musulunci har yanzu shi ne addinin da yake kira zuwa ga ci gaba, sai dai wannan ba yana nufin musulunci yana kiran ci gaba da ma’anar da yake a yammacin duniya ba ne da abubuwan da wannan ma’anar ci gaban ta kunsa wanda bai dace da tunanin musulunci da daukakarsa ba, sai dai shi musulunci yana kira zuwa ga ci gaba da daukaka da ma’anar cewa kada a dakatar da rayuwa a tsyar da ita bisa al’adun da suke lalatattu wadanda ba su da wani dalili na hankali ko shari’a da rashin dacewa da zamani, don haka musulunci yana son a dora rayuwa bisa ci gaban zamani tare da kiyaye kyawawan halayen musulunci da umarnin Allah madaukaki, wannan kuwa abu ne mai haske da yake a fili a tunani da fikirar musulunci.

Sai dai akwai abin da aka yi tarayya a ciki tsakanin wadannan fahimtoci guda biyu, misali zamu iya nuni zuwa ga kwadaitarwa ga ci gaban zamani da ilimi a fahimtar musulunci, wanan kuma yana daga cikin abubuwan da aka dage a kansu a fahimtar yammacin duniya da ci gaban zamaninsu, haka nan kariya ga hakkin dan’adam, sanya hankali a al’amura, tattaunawa da masu sabani da ‘yan hamayya, da sauran addinai, dukkan wadannan abubuwan suna daga cikin abubuwan da ake karfafa su a duniyar yammacin duniya, duk wadannan abubuwan zamu same su da ma’anarsu mafi kamala a cikin fikirar musulunci kuwa.

Haka nan daga misalan irin wannan akwai batun tunanin ‘yanci a addini da nisantar zartar da hukunci bisa tabbaci[8] ba da wani dalili mai karfi ba da yake wakana a yammacin duniya wanda yammacin duniya ya samu asalin wannan daga musulunci ne.

Sai dai abin da ya kamata mu bayar da muhimmanci a kansa shi ne cewa yayin da musulunci yake kwadaitarwa a kan ci gaban wayewar zamani yana son mutum ya fita daga son rai na sha’awa ne, kuma kada ya sanya kansa a matsayin abin da sha’awa ta ribace shi. A nan ne zamu ga Imam Ali (a.s) yana ganin cewa dukkan ilimin da hankali ba ya karfafa shi to bata ne da karkacewa, yana mai cewa: “Duk wani ilimi da hankali ba ya karfafarsa, to bata ne” [9], haka nan musulunci yake ganin duk mutumin da ranakunsa suke daidato –ba tare da yana samun ci gaba ba- to shi mai hasara ne. Wannan fahimtar zamu ga tana nuni ga muhimmancin da musulunci yake bayar wa ci gaba da wayewar zamani matuka.  

Sannan akwai ruwayoyi da suka zo a wannan fagen masu yawa kwarai da zamu kawo wasu daga ciki kamar haka:

Imam Sadik (a.s) ya ce: “Masani da zamaninsa, rikirkitattun abubuwan ba sa kai masa hari” [10].

Daga Imam Ali (a.s) ya ce: “Hakki ne a kan mai hankali ya raba wa ra’ayinsa ra’ayin masu hankula, kuma ya raba wa iliminsa ilimomin masu hikima” [11].

Daga Imam Ali (a.s) ya ce: “Kwarewa ba ta karewa, kuma mai hankali yana neman karinta”[12].

Daga Imam Musa Alkazim (a.s) ya ce: “Wanda ya bar duniyarsa don addininsa, ko addininsa don duniyarsa, ba ya daga cikinmu”[13].

 


[1] Daha: 131.

[2] Jawadi Amuli: Abdullahi, Tafsirul maudu’I, marahilul akhlak fil kur’an, shafi: 172.

[3] Almajlisi, biharul anwar, j 67, shafi: 310.

[4] Littafin da ya gabata.

[5] Sayyid hamid alhusaini, muntakhabu mizanul hikma, hadisi 4480.

[6] Muhammad dan ya’kubu alkulaini, alKafi: 1/30/1.

[7] Biharul anwar, j 1, shafi: 171.

[8] Baztabe andishe, adadi na 20, shafi: 21.

[9] Abdulwahid al’amudi, gurarul hikam, shafi: 384.

[10] Alharrani, tuhaful ukul: 356.

[11] Gurarul hikam: 384.

[12] Littafin da ya gabata: 42.

[13] Biharul anwar, j 1, shafi: 171.

 

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa