Please Wait
Dubawa
5816
5816
Ranar Isar da Sako:
2008/11/22
Takaitacciyar Tambaya
Shin ya halatta a yi salla a gefen Kabarin Imamai wanda wani lokacin Kabarin nasu kan zama a bangaren alKibla kuma ya dace da inda mai yin salla ya ke kallo?.
SWALI
Aya ta 33 ta surar Kahfi na cewa kar ku riKi Kabari ya zama masallaci, don haka zamu iya cewa akwai matsala mutun ya yi salla a gefen Kaburburan Imamai wanda wani lokaci kabarin kan zama daidai da inda alKibla take inda nan me sallar ya ke kallo?
Amsa a Dunkule
Bisa haKiKa zahirin wannan ayar abin a duba ne. ayar tana magana ne kan halaccin gina masallaci a kusa da Kabari, kama bayanan da suka zo a tafsirai na nuna cewa wannan masallacin an gina shi a gefen Kaburran Ashabul Kahfi.
Duk da cewa a kwai ruwayoyin da a zahiri suna nuna cewa ana magana ne kan hana gina masallaci a gefen kaburra, amma bisa la’aki da wannan ayar da kuma bincike da aka yi kan waDannan ruwayoyi ya bayyana cewa waDannan ruwayoyin suna hani ne kan a daina mayar da Kaburran (bayin Allah) wajen bautar Gumaka wanda yin haka ya saBa da bautar ubangiji kwata- kwata, kuma wannan jigon ya yi hannun riga da magana kan gina masallatai kusa Kaburburan bayin Allah Ta’ala, kuma sallar da aka yi ana kallon alKibla ingantacciya ce, kuma magana kan cewa akwai wani shinge da ya shiga tsakanin mai salla da ka’aba makar Kabarin Imamai da ko ma wani abu daban baya sa salla ta sami matsala (ta Baci).

Amsa Dalla-dalla
Bisa haKiKa tambayar da ka yi da buKatar a rarraba ta zuwa tambayoyi da ya zama lalle ne aba da amsar su sannan ne zamu samu gamsashshiyar amsa.
1- Shin ayar nan ta suratul kahfi da ta yi nuni kan hani a kan gina masallaci a gefen Kaburbura, tana Dauke da ma’anar yin hana kan gina masallaci a gefen kabari kenan ko kuwa?
2- Shin akwai wasu wurare da suke da Kima da daraja ta musamman da suka banbanta da sauran wurare waDanda zamu iya kiran su da wurare masu albarka ko kuwa?
3- Yin salla da sauran ibadodi a kusa da Kaburra ko da ma in mun kaddara cewa Kabarin yana inda al’Kibla take (inda muke fuskanta); shin hakan na da sabani ko ya yi hannn riga da bautar ubangiji, kuma wace mahanga shi’a imamayi suka samo daga imamansu kan yadda ake yin ibada a gefen kaburbura?
Dangane da kaso na farko zamu iya cewa, ayar nan ta 21 ta surar Khafi an yi kuskure wajen tambayar da aka yi da aka dangana ta da aya ta 33 wacce take bayani kan cewa muminai sun yi alkawarin a sarari cewa sai sun gina masallaci a kusa da Kaburburansu, kuma Kur'ani bai yi bayinin cewa yin haka yana da aibi ko laifi ne ba, tare da cewa idan har bakancen da waDannan gungun suka yin a gina amasallaci ya saBa da aKidar addini da ya zama lalle Kur'ani ya ja kunnansu kan wannan bakancen da suka yi, wannan lamari ne na tarihi da ya faru kuma ya zo a cikin da yawa daga cikin litattafan ahlussuna[1]. Saboda haka daga ayar {wallahi da sannu zamu yi masallaci a inda kaburburansu suke} ba bu wata fuska da za a iya ciro wata ma’ana daga wannan ayar da ke nuna cewa wannan aya na yin hani kan gina masallaci. Tabbas a cikin wasu tafsirai na Ahlussunna a Kasan wannan ayar sun kawo wasu ruwayoyi da ke nuni kan hana gina masallata a gefen Kaburbura[2]. Kuma bisa dace mai bincike kan ci karo da wasu ruwayoyi makamanta wDannan a cikin manyan litattafan Hadisi na Shi’a.[3] wannan dalilin ne ya sa masana ke ta neman hanyar warware wannan cakuDeDeniyar, tun da ta Bangare daya ba zai yiyu a iya kawar da ido daga halaccin gina masallaci a Kaburburan ashabul kahfi ba wanda ayar ta halatta a sarari, ta daya Bangaren kuma ba zai yiyu a ce rawayoyin da suke magana kan hana a riKi masallaci alKibla da kuma gina masallatai a kaburbura ace ba su da tushe ba.
Bisa wannan asasi dole a haDa tsaknin waDanna ayoyin da ruyayoyin waDanda a zahiri suna yin hani daga wannan aiki[4] sannan a gwama su da juna a fassara su da fassarar da ba za a sami cin karo tsakaninsu ba.
Wasu daga cikin malaman tafsiri sun tafi kan cewa a KoKarin su na su ga sun kare aKidarsu ta kowa ne hali ta hana gina masallaci a Kaburbura sai suka bayyana wannan maganar da cewa ko dai ya zama waDannan da suka gina masallaci kafirai ne su ko kuma muminai ne da suka aikata a bin da ba daidai ba,[5] bisa wannan tafsirin na su haKiKa sun yi ko in kula da zahirin al’Kurani, da wani yaren sun yi kokari shafi haKiKanin abin da ayar ke magana a kan sa. Amma kamar yadda muka bayyana a baya waDanda suka gina masallacin ayar ba ta zarge su ba kuma Allah ta’ala bai aibata aikinsu ba, ballantanama wannan ayar ita ce mafificin dalili kan mustahabbacin abin da suka aikata.
Allama Majlisi wanda Daya daga cikin manyan malaman Shi'a ne, ya yi bayani kan yadda za a haDa tsakanin ayar da ruwayoyin yana mai cewa: “yahudawa da nasara sun maida Kaburburan annabawan su alkibla kamar yadda masu bautar gunki ke fuskantar gumakansu su yi musu sujjada (bisa wannan dalilin ne Manzo (saw) ya zarge su kuma ya nuna kuskuren wannan mummunan aiki)” amma idan mutum ya gina msallaci a kabarin wani bawan Allah ta’ala na gari da niyyar neman samun temako daga ruhi mai tsarki na wannan bawan na gari ko kuma ya rika bada ladan ibadun da ya yi ga wannan bawa na gari, ba ya riki Kabarin a matsayin alKibla ba, ba kuma ya riKe shi a matsayina abin bauta yana girmama shi ba, haKiKa yin haka (gina masallaci da nufin samon temako) bai saBa da koyarwar musulunci ba, kuma Allama ya bada misali domin ya Karfafa abin da ya ke da’awa ya dauki Dotsen Ismaila (Hajari Isma’il) a matsayin dalili yana mai cewa kowa ya san cewa Hajaru Isma’il a gefen ka’aba ya ke tare da cewa Kabarin Annabi Isma’il ma a nan ya ke! Amma dukkanin musulmai sun yi imani da cewa yin salla a wajen ba kawai ba shi da matsala ba ne a shar’ance, yana ma da falaloli masu yawan gaske.[6]
Wasu daga cikin malaman tafsiri na ahlussanna sun fahimci wannan lamarin har ma suka ce wannan ruwayoyin ba su da saBani da ayar gina masallaci a Kaburbura.[7]
Bisa wannan asasi sakamakon wannan bincike zai zama cewa; bai halatta a yi waKabari sujjada ba, ko kuma a rike su alKibla kamar yanda masu bautar gunki suke yi, amma gina masallatai a gefen Kaburbura da kuma yin bauta a wannan masallacin alhali alKiblarmu ita ce wannan dai da Allah ta’ala ya yi umarni da ita wacce ita ce ka’aba, kuma ya zama nan muka kalla muka yi sujjada, to babu wata matsala cikin yin wannan.
Wani dalili kan da za mu iya kawo wa kan wannan da’awa tamu shi ne musulmai sun bisne jiki mai tsarki na Manzo (saw) da sahabbansa guda biyu a kusa da masallacinsa wanda daga baya bayan da ka fadada masallacin sai Kaburburan nasu suka wayi gare wani Bangare ne daga masallacin, amma ba wani malami da ya dogara da waDannan ruwayoyin ya bada fatawar hana yin salla a masallacin Annabi (saw), tare da cewa yanayin masallacin a yanzu da yin salla a wannan waje mai tsarki wato masallacin Manzo (saw) da yin salla ‘yan shi’a a sauran Kaburbura masu tsarki ba shi da wani banbanci.
Dangane da abin da ya shafi Bangare na biyu ya zama lalle mu yi bincike kan wasu lamurra mu kuma warware su. Sananne ne cewa mu musulmai mun yi imani da cewa:
1- Allah maDaukakin sarki bai keBanta da wani waje ko Bangare ba kuma duk inda muka kalla to yana nan kuma shi muka fuskanta.[8]
2- Allah maDaukaki bisa tausayawarsa domin ya tsara wa bayinsa yadda za su rika bauta masa, ya zaba musu wuraren da zasu rika kalla yayin da suke bauta masa a matsayin alkibla kuma a lokacin Manzo (saw) ma musulmai sun kasance sun kallon alKibloli guda biyu, ma’ana masallacin Akasa da kuma Ka’aba da wani yaren ita alkibla a kan kanta ba ita ce ke da kima ba, abin da ya ke da babbar kima ta musamman shi ne bautar Allah kuma wannan lamari ne da Kur'ani ya yi bayaninsa a sarari.[9]
3- Bisa umarnin jagororin addinin kadai wanda ake yi wa sujjada shi ne Allah ta’ala, amma wannan ba ya nufin cewa yin sujjada kan ko wane abu ko kuma tare kallon wani abu na nufin cewa shi ake yi wa sujjada ko ake bautawa ba.
Shin lokacin da muka fuskanci alKabla muke kallon ka’aba a lokacin yin sujjada na nufin ka’aba muke bautawa?
Kuma shin Allah maDaukaki bai umarci mala’iku da su yi wa Annabi Adam sujjada ba? Shin wannan na nufin Allah ya umarce sa da su yi shirka kuma shiaDan ne kadai mai tauhidi wanda ba mushrika ba don haka ne ma ya ki yin shirka ya ci jarrabawa?[10] (Allah ya yi mana tsari), ko shin mala’iku sun Ki su bautawa Allah shi kadai sai suka bauta wa Adam?
Mu abin da muka Kudurce shi ne cewa yin sujjada, alamace ta sallamawa ga Allah da yi masa biyayya, kuma idan ya ce ku yi wa wani na sujjada to da sannu za mu aikata hakan, kuma aikata hakan alama ce ta bautawa Allah da kuma yi masa biyayya. Da wani yaren mu abin da mu ka sani shi ne kaDai abin da ake kira shirka shi ne bauta wa wanin Allah ta’ala, ba wai kallon alkibla ba ko sujjada da ma sauransu ba, kuma ka’aba da muka rika a matsayin al’kibla Allah muke bautawa idan muka fuskance ta, kuma Allah kaDai muke yi wa sujjada.
4- Muna kudurce cewa dukkanin sammai da Kassai na Allah ne amma idan muka bautawa Allah a waje mai albarka hakan ya fi zama abin so da Kauna. Yin bauta a masallacin harami da masallacin Annabi (saw) dukkaninsu misali ne na waDannan wajaje masu albarka. Kuma kamar yanda ya zo ne daga Manzo (saw) cewa: “yin ibada a masallaci na kamar yin ibada sau dubu ne a cikin wani masallaci ban da masallacin harami.”[11] Wannan na nuna cewa zamu iya tabbatar cewa wasu warare na da alfarma ta musamman.
A koyarwan shi’a kari a kan masallatai, ya zo cewa yin salla da sauran ibadu a gefen kabarin imamai (as) na da lada mai tarin yawa da daraja ta musamman. Amma kuma su kansu imaman (as) ne suka tsara yadda ake yin ibadar da yadda ake karanta ziyarar ta yadda ba su da Kwarzane na shirka a cikinsu.
Ko da ya ke tun asali, bayani kan lamarin da ya shafi cewa menene amfanin ziyara be kebanta da tambayar da aka yi ba, amma idan kana so zaka iya komawa binciken da aka yi kan wannan lamarin daga ciki akwai tambaya ta 3295 a wannan site din.
1- Imam Sajjad (as) ya shafe duguwar tafita (tun daga madina) zuwa kufa yana isa bai tsaya ko ina ba sai masallacin kufa da shigar sa ya fara salla da ibad. Abu Hamza samali wanda ya kasance daga cikin manya kuma masu tsoron Allah na cikin garin kufa ya naKalto yana mai cewa “na bi shi har zuwa madaukar raKuma (inda ake daure rakuma a inda nan ne suke sauka suke hutawa in sun iso daga tafiya) ina mai bin diddgin sa sai na tambayi wani yaro baKar fata da ya ke kula da doki da kuma raKumin sa, na ce masa waye wannan bawan Allah? Sai yaron ya yi mamaki yana mai tambayata ta, a ce yanzu ba ka iya gane shi ta shakalinsa da halayensa ba? Ali Dan Husain (as) ne Abuhamza ya ce bayan da na san Imam (sa) ne sai na faDi a agabansa ina sumbantar Kafafunsa sai Imam (as) ya dago kaina a hankali sannan ya ce: kar ka yi haka, Allah kaDai ake yi wa sujjada”.[12]....
2- Wani mutum mai suna Abulyusha’u ya na cewa: na ji wani mutum na tambayar Imam SadiK kan ziyarar Imam Husain (as) yana cewa a lokacin da nake yin salla shin zan iya sanya Kabarin sa ta fuskar alKibla sai ya zama na fuskance shi, sai imami na shida (as) ya ce a ayayin da ya ke ba shi amsa: a lokacin da kake yin salla ka Dan nisanta daga kabarin kadan.[13]
3- Ya zo a wasu ruwayoyi cewa ana yiwa maziyarta wasici da idan za su yi salla, su yi ta daga Bangaren da kan ma’asumi ya ke daga gefe[14] kuma idan ka je makwantan ahlulbaiti ka kula sosai za ka ga cewa mafi yawan maziyarta hanKoronsu shi ne su yi salla a wannan wajen da aka fi sani da (saman kai) wato bangare kai daga gefe.
Dalilin yin salla a wannan wajen ta yiyu ya zama an karfafa shi ne saboda yin salla a nan shi ne, zai zama ba mu sa Kabarin waDannan bayin Allah a baya ba ballantana ya zama mun yi rashin kunya kuma ba mu sa shi a saitin inda muke fuskanta ba na alkibla ba don kar wani ya yi tsammaniin cewa Kaburburansu ne alKiblar mu, sai ya zama a wannan yanayin zamu yi sallarmu a kusa da su kuma muna masu fuskantar alKibla.
Irin waDannan ruwayoyi na nuna cewa wajibi ne a girmama imamai ma’asumai (as) kuma babu banbanci a cikin haka daidai ne a lokacin da suke raye ko kuma bayan sun bar duniya sun yi shahada, sananne al’amari ne cewa matsayinsu sama ya ke da matsayin shahidai waDanda alkur’ani ya bayyana cewa su rayayyu ne ana azurta su a wajen ubangiji maDaukaki[15], kuma bisa wannan dalilin ne muka Kudarce cewa Annabwa da Imamai (as) rayayyu ne kuma suna jin sautinmu kuma suna amasa sallamarmu amma tare da duk wannan ba su yarda girmamawa da muke yi gare su ta zama dalilin gafalar daga Allah ta’ala ba. don haka ne ma imamai su ka yi wasici da cewa kafin a karanta ziyara jami’a a fara yin kabbra sau dari[16], don kar mu manta da girman ubangiji maDaukaki, sai suka tsara lamarin ta yadda gimama su a lokacin da suke raye da kuma lokacin da suke cikin Kabarinsu mai tsaki ya zama da yanayin da zai kasance a KarKashin bautan Allah ta’ala.
Bisa sakamakon abubuwan da aka bayyana, za mu iya ganawa da mahaliccinmu bisa yanayin mafi kyau kuma mafifici a gefen kaburburan waDannan manya bisa la’akari da mujahadarsu da kuma kokarin yin koyi da su.
Amma fadin ka cewa wani lakacin wajen da kake tsayawa ka yi ziyara na dacewa da alkaibla, amma a Kudurcewarka shin kana nufin lokacin da harami ya cika taf babu masakar tsinke ta yadda ba wani wajen da mutum zai iya tsayuwa ya yi salla in ba inda ya ke fuskar kabari ba kuma ya dace da inda kabarin mai tsarki ya ke ba, kana fufin dole ya koma ya sami wajen da baya fuskantar kabari sannan ya yi salla? Tabbas ba wani musulmi da zai karbi wannan maganar a iran wannan yanayi. Don haka ka sani, tare da cewa akwai ruwayoyi masu yawa, cewa ya dace wajen sallar mu kar ya zama inda muke kallon saitin Kabari ne dari bisa dari, duk da haka wannan sallar ba Batacciya ba ce kuma baza ta zama wacce ba ashar’anta ta ba. Tun da fuskanci kabari mai tsarki ya yi sallarsa, a lokacin da harami ya ke cike da mutane maKil, kamar dai yadda ya ke a masallacin harami idan ya zama kan da’irada mutum ya ke tsaye tana kallon kabari a yayin yin salla, zai iya yiyuwa a tuhumce mutane da irin wannan tuhumar cewa sun maida Kabari alKiblarsu, idan ba haka ba kasantuwar mafuskantar masallaci ta dace da kasantuwar kabari a wajen ba zai zama dalilin da zamu jefi wasu da irin wannan tuhuma ba, sai dai in mai yin tuhumar ya fita daga shingen adalci kuma ya kangarewa gaskiya, kuma shin idan wasu suka yi salla a kewayen ka’aba daidai saitin maKami ibrahim ta Bangaren alKibla shin za ka iya cewa waDannan mutanen ba ka’aba suka kalla suka yi sallar su ba, maKami ibrahim suka kalla suka yi salla?!
Tabbasa idan wasu DaiDaikun mutane a yayin sa suke salla suka kau da kai daga alKibla bisa rashin sani suka fuskanci Kabari suna salla, iran waDannan mutanen ba kawai lamarin ya taKaitu da cewa sallarsu ta baci ba, haKiKa ‘yan shi’a za su Kalubalanci wannan aiki, kuma idan aka sami wani ya yi haka, tare da cewa yin hakan abu ne mai wuya, ba zai yiyu a danganta aikinsa da mazahabar shi‘a ba. (ya zama kuskure ne na kashin kai ba na mazahaba ba tun da mazahabar bata halatta masa yin haka ba).

[1] Dabaria , abu Ja'afar Muhammad dan jariri a cikin jami’ul bayan fi tafsiril kur’an j 15 shafi na 149, darul ma’arifa baireut 1412.
[2] KurDabi Muhammad dan Ahmad a ciki aljami’u li ahkamul Kur’an j 11 shafi 379. Intisharati nasir khusru tahran, 1364.
[3] A koma wannan adreshin shekh saduK a man la yahdhuruhul faKih j 1 shafi na 178 ruwaya ta 532, muassar nashrul islami KOM 1413.
[4] Kurbabi adreshin da ya gabata a baya j 11 shafi na 379.
[5] Ibni kasir a cikin tafsirin Kur'ani mai girma j 5 shafi 134-133, darul kutubul ilmiyya baitrut 1419.
[6] Majlisi Muhammad bakir a cikin Biharul anwar j 79, shafi 56 muassaatul wafa bairut 1404.
[7] Mazhari, Muhammad Sana’ullah a cikin Tafsirin mazhari j 6 shafi na 25 maktabar rushdiyya Pakistan, 1412
[8] Surar BaKara aya ta 115 {gabas da yamma dukkanin su na Allah ne duk inda kuka kalla kun dace da inda ubangiji ya ke}.
[9] Surar baKara aya ta 142-145.
[10] Surar baKara aya 34. Surar a’arafi aya ta 11 da surar isra’I aya ta 61 da kahfi aya ta 50. Dss....
[11] KurDabi Muhammad Dan Ahmad a cikin Jami’u li ahkamul Ku’an j 10 shafi na 372.
[12] Hurrul amuli Muhammad dan Hasan a cikin wasa’ilush shi’a j 14 shafi 407 -408, ruwaya ta 19474 muassatu Ahlulbait Kom 1409.
[13] Adreshin da ya gabata j 4 shafi 519 ruwaya ta 19731.
[14] Adreshin da ya gabata j 14 shafi 519 ruwaya ta 19731 da shafi na 520 hadisi na 19732.
[15] Surar Ali (as) Imrana ayWa ta 169.
[16] Majlisi Muhammad baKir a biharul anwar j 99 shafi 127.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga