Please Wait
26804
Kallon namiji ga jikin mace wacce ba muharrama ba haramun ne, ko da nufin ya ji dadi ko bai nufin hakan ba. Amma kallo fuska da hannaye idan ya kasance da nufin jin dadi to haramun ne, sai dai idan ya kasance ba da nufin jin dadi ba to babu komai. Haka nan kallon fuska da jiki da gashin yarinya da ba ta balaga ba idan ya kasance ba da nufin jin dadi ba, kuma babu wani tsoron fadawa cikin haram, to babu komai gareshi, sai dai bai kamata ya kalli wuraren da bisa al’ada ana rufe su ba, kamar cinya, da ciki, bisa ihtiyadi[1].
Amma kallon namiji ga jikin mace muharram, idan ya kasance ba da nufin jin dadi ba, to babu komai, sai dai ban da al’aura biyu. Sai dai kawai miji shi ne ya halatta ya kalli dukkan jikin matarsa da nufin jin dadi.
Imam khomain (k.s) yana fada a game da haka cewa: “Ya halatta ga namiji da mace muharramai su kalli jikin junansu da kallon dukkan jikin juna in bada al’aura idan ba da nufin jin dadi ba”, don haka ya halatta ga dan’uwan uwa ya kalli dukkan jikin matan da suke haramun gareshi in ban da al’aura, ba da nufin jin dadi ba[2].
Kuma bai wajaba kan mace ba ta rufe jikinta gaban muharrami, sai dai bai halatta ga namiji ba ya kalli kowane wuri ne a jikin muharramarsa da nufin jin dadi[3]. Idan kuna son karin bayani sosai to sai ku koma wa wadannan shafukan:
1- Maudu’i: Da’iratu Hijabil Mar’a, tambaya 1759 (Shafin Intanet: 2327).
2- Maudu’i: Satruz Zufri, was sha’aril must’ar an gairil muharram, tambaya 3663 (Shafin Intanet: 2923).
[1] Taudhihul Masa’il: Mai Hashiyyar Imam Khomain, j 2, s: 485, mas’ala: 2433.
[2] Taudhihul Masa’il: Mai Hashiyyar Imam Khomain, j 2, s: 489, mas’ala: 2437.
[3] Ya kamata a kiyaye janibin halaye na gari a cikin irin wadannan lamurran, abin da aka fada hukuncin fikihu ne kawai.