Please Wait
9284
Wannan magana ta zo cikin hadisin Manzo (s.a.w), abin nufi da ranaku a nan su ne ranakun sati, amma a mafiya yawan lokuta wannan ruwayar na nufin muhimmancin zamani da wajabcin rashin shakku zuwa ranaku ko rashin kudure su da zai sa a manta su ko muzantan su, wanda wajibi ne ka da mu shagala wajan mantawa da rahamar da mutum ke samu yayin da ya amfanu da wadannan ranaku, kai ya wajaba ma ya kyautata amfanuwa da wadannan ranakum. koda yake wannan magana na da wata ma’ana ta daban, hadisi na nan zuwa cikin bayani a fayyace.
Wannan magana tazo cikin hadisin Manzo (s.a.w),[1] zahirin maganar na shiryarwa kan bai kamata mutum ya dinga tabar da ranaku ba, ko yin kwantonsu ya kamata ka da ya yi mummunan aiki a cikinsu, domin duk wanda ya aikata haka ya aikata mummunan aiki, ya dawwamar da munanan ayyuka cikinsu sakamakon abin da ya dawwamarne zai sameshi. Zai iya yiwuwa mu kawo ma’ana ta biyun wadda zamuga tazo da ma’ana ta badini, ma’anar kuwa shi ne kan sanayyar ranakun sati. [2]
Safar dan Abi dalf daya daga shi’a Imamiyya yana zaton ranaku na nufi dare da rana, wannan ruwaya kuma ta zamto dalili wajan masu akidar ilimin taurari da masu aiki domin iyakar mutum ya ratayune da fadin dare da rana, wata da taurari, kuma mutum anan hannunsa a bude yake ba shi da ikon aikata komai. Safar dan Abi dalf na cewa: <na ziyarci imamul Hady (a.s) cikin kurkukun da yake, nace da shi, ya shugabana hadisin da aka rawaito cikin hadisin Manzo (s.a.w) bansan ma’anarsa ba, sai Imam (a.s) ya ce wane hadisi wannan? Sai nace sai nace, fadar Manzo (s.a.w) fadar Manzo (s.a.w) cewa ““ka da ku kirga ranakun sati sai su kirga ku” mene ma’anarsa sa Imam ya ce: haka ne mune ranaku mun tsayar da sammai da kassai, asabar sunan Manzo (s.a.w) ne, lahadi kuma Amirul muminin (a.s), litinin su ne imam Hassan da Husain (a.s), talata kuma Aliyyu dan Husain da Muhammad dan Ali (a.s), laraba kuma Musa dan Ja’afar da Aliyyu dan musa(a.s), Alhamis dana Muhammad (a.s), Juma’a kuma dan dana …[3]
amma a mafiya yawan lokuta wannan ruwaywr na nufin muhimmancin zamani da wajabcin rashin shakku zuwa ranaku ko rashin kudure su da zai sa a manta su ko muzantan su, wada wajibine ka da mu shagala wajan mantawa da rahamar da mutum ke samu yayin da ya amfanu da wadannan ranaku, kai ya wajaba ma ya kyautata amfanuwa da wadannan ranakum.
Daga mafi muhimmancin amfanuwa da wadannan ranaku shi ne yin tawassuli da imamin da ya kebantu da wadannan ranaku ta hanyar ziyarorinsu da ta kebanta da ranar, wadanda aka ambata cikin litattafan adduo’i kamar mafatihul jinan da sauransu.
[1] Abu Hanifa,nu’umanu dan Muhammad dan Mansur Attaimiyyil magriby, da’aimul Islam bolume 2 page 145, mu’assasatu Ahlul-bait(a.s) lil ihya’it turath Beirut Labanon bugu na biyu (second edition) 1385; muhaddisun nury myrza Husain, mustad rakul wasa’il wa mustanbidul masa’il bolume 13 page 77 mu’assasatu Ahlul-bait(a.s) lil ihya’it turath Beirut Labanon bugu na daya (first edition) 1408
[2] Majlisy, Muhammad Bakir Biharul anwar bolume 99 page 211, mu’assa satul wafa’a Beirut Labanon.
[3] sss Bakir Biharul anwar bolume 99 page 211