Please Wait
Dubawa
7872
7872
Ranar Isar da Sako:
2014/08/21
Takaitacciyar Tambaya
Wadanne ne muhimman siffofin tafsirin Kur\'ani da kuma (kimarsu) matsayinsu na ilimi?
SWALI
Ya matsayin da kuma mihamman abin da tafsirin zamanin shabbai ya kebanta da su?
Amsa a Dunkule
Baba shakka kan cewa hakika sahabbai Allah Ta’ala ya kara yarda a gare su ya yarje musu sun bawa lamarin Kurani mai girma minimmanci sosai a lokacin rayuwar Manzo (s.a.w) da ma bayan wafatinsa (s.a.w) kuma sun dauki tutar addini da kyakkyawar koyarwa sama zuwa jama’a. kuma musulmai sun kasance suna komawa zuwa gare su suna tambayarsu ma’anar ayoyi da murdadu (masu wahalar gane wa) daga cikinsu (ayoyin), Na’ama hakika sun kasance suna dauke da martaba ta ilimi da fifici bisa gwargwadon yadda suke da karfin fahimta da kaifin basira da sauran baiwace- baiwace da tanadi, bisa gaskiya sahabai sun kasance bisa mabanbantan martabobi da kudrar fahimtar ma’anarsa da kuma bayanin ma’anarsa wacce ita ake nifi, wannan kuma yana komawa ne zuwa banbancin da suke da shi na daukar ilimi da rike shi da kuma damar da suka samu kan haka, don haka akwai tazarrori tsakaninsu a ilimi. Tare da sanin cewa da yawa daga cikin sahabbai sun ji tafsiri a wajen Manzo (s.a.w) ba tare da wasida ba, duk da cewa wannan tafsirin cikakkansa bai iso zuwa gare mu ba, kuma duk cikinsu ba wanda ya iya hada cikakkiyar daura ta tafsirin da ya ji daga Manzon Allah (s.a.w) in banda Imam Ali (a.s) da ya hada abin da ya ji daga Manzon Allah (s.a.w) amma duk da haka ana kiran abin da sahabbai suka rubuta; da taska ta ilimi mai girma a fagen ilimomin Kurani.
Tafsirin sahabai ya kebanta da da abubuwan da ba a same su dakkanin su a cikin tafsiran wadanda suka zo bayansu ba, na daga saukinsa da abin da bai wace wasu ‘yan kalmomi ba wajen warware murdadden abu ko kawar da abin da ya rikitar, a cikin bayani cikakke warkakke tare da dukkanin takaitawa da gamsarwa; da kuma kubutarsa daga jayayyar sabawa da isuwar sa daga tafsiri da ra’ayi da ma’anar dankara ra’ayi wanda bai jingina da jigo mai karfi ba; da kuma wofintar sa daga kissoshin marasa inganci da tabbacinsa kan rashin yin tsammanin shakku da yin riko da zace-zace bayan bayyanar majiginarsa da kuma fayyataccen bayanin sa.

Amsa Dalla-dalla
(Abokanta) ya abokance shi abokantaka, kuma abokinsa na nufin wanda ya zauna da shi, abokai jam’i ne na aboki kuma aboki shi ne wanda aka rayu da tare da shi, sun yi abota, mutane sun yi abokantaka kuma mutane sun abokanci shashinsu da shashi[1]. Aboki shi ne wanda ya lazimci mutum, mutum ne shi ko dabba ko waje ko lokaci kuma ba banbanci idan ya kasance ya abokance shi da jiki ne ko - kuma hakan shi ne asali kuma da wannan ma’anar aka fi amfani, kuma a al’adance ba’a kiran wani da wannan sunan sai wanda zamantakewar shi ta tsawaita, kuma idan mutum na da wani abu da ya mallaka kamar idan yana da jaki: Ana kiran mutumin da abokinsa, sai a ce a (misali; ma’abocin jaki) haka ma wanda yake da ikon yin tasarrufi da wani abu, wani lokaci kuma ana jingina Kalmar (sahib) zuwa ga abin da yake shugabanta sai a kira shi da misalin: ba’abocin runduna haka ma wanda ake tare da shugabanta ko da yaushe, ana kiransa da sahibin sarki, kuma musahaba ta fi karfi ma’ana fiye da haduwa (ijtima’u) damin musahaba na da sharadin zamantakewa ta tsahon lokaci, don haka duk wata musahaba haKuwa ce, amma ba ko wace irin haduwa ake kira abukantaka ko musahaba ba [2] .
Hakika masu bincike da masana ilimin mazaje sun fadi wani adadi na ta’arifin sahabi[3] na daga: sahabi shi ne wanda ya zauna tare da Manzo (s.a.w) shekara daya ko biyu ya je yaki tare da shi sau daya ko sau biyu.[4] Kuma an yi ta’arifin sa da cewa shi ne shahabi shi ne wanda ya lazimci Annabi (s.a.w) kuma ya lazimce shi lazamtar da ta kai a sheda cewa shi sahabi ne a al’adance ba tare da iyakance lokaci ayyananne ba [5].
Daga cikin abin da aka fahimta cikin wadannan ta’arifofi shi ne cewa wasu daga cikin manyan masana sun yi riko da kaidin (iyakance) zamani ko lokaci a cikin ta’arifinsu sai suka shardanta a cikin ta’arifinsu ya zama wani lokaci mai tsaho ya shude da ya kai ya cancanci abokantaka, wato a kira shi da sahabi, a daida lokacin da masu ta’afiri na uku suka fadada ma’anar sahabi ta yadda suka hada har da wanda ya ga Annabi (s.a.w) ko da da awa daya ne na rana guda ba banbanci ya rawaito hadisi daga gare shi ko be rawaito ba; Amma abin da ya inganta shi ne lalle abokantaka (sahabbantaka) ba ta tabbata sai da haduwa da zamantakewa da shi ko abokantakarsa (s.a.w). [6]
Mafi shaharar mafassara daga cikin sahabbai
Babu shakku cewa hakika sahabbai na daga cikin (wadanda Allah Ta'ala ya yarda da su kuma suma suka yarda da shi) sun kasance sun mihimmantar da sha’anin Kur'ani mai girma a lokacin da Annabi (s.a.w) yake raye da ma bayan lokacin da ya bar duniya, kuma sun dauki tutar addini da kyawawan halayya da koyarwar sama zuwa ga mutane. Kuma musulmai sun kasance suna komawa zuwa gare su suna tambayar su ma’anar ayoyi da ayoyi murdaddu. Na’ama hakika sunkasance suna dauke da martaba ta ilimi da fificin da gwargwadon yadda suke da karfin fahimta da kaifin basira da sauran baiwace-baiwace da tanadi, bisa gaskiya sahabai sun kasance bisa mabanbantan martabobi a sani da kudrar fahimtar ma’anarsa da kuma bayanin ma’anarsa wacce ake (Allah Ta'ala yake) nufi, wannan kuma yana komawa ne zuwa banbancin da suke da shi na daukar ilimi da rike shi da fahimtarsa, kamar yanda suke da banbanci a fagen sanin yaren su (larabci) hakika malaman tafsiri sun ambaci cewa lalle umar dan khaddabi ya karanto surar bakara har sai da ya iso inda Allah yake cewa ake cewa: {ail uanzuril insanu ila da’amih * inna sababnal maa’a sabba * summa shakaknal ardha shakka * fa ambantana fiha habba * wa inaban wa kabdha * wa zairunan wa nakhla * )
(فَلْیَنْظُرِ الْإِنْسانُ إِلى طَعامِهِ * أَنَّا صَبَبْنَا الْماءَ صَبًّا * ثُمَّ شَقَقْنَا الْأَرْضَ شَقًّا * فَأَنْبَتْنا فیها حَبًّا * وَ عِنَباً وَ قَضْباً * وَ زَیْتُوناً وَ نَخْلاً)[7]
(lalle me zai hana dan adam ya yi duba zuwa abincinsa * hakika mun zubo ruwa zubawa * sannan muka tsaga kasa tsagawa * sannan muka fitar da tsrrai daga cikinta * da inubi da ciyawa * da zaitun da dabino * [7] sai ya ce: mun san ma’anar (fakihatan) wato ‘ya’yan itaciya to menene ma’anar (abba) (abba shi ne makiyayar dabbobi) (وَفَاكِهَةً وَأَبًّا) da ke cikin wannan ayar? Sannan ya koma zuwa kan sa sai ya ce lalle wannan shi ne kallafa wato dora wa kai nauyi da ba za ka iya ba ya Umar. [8] Abu ubaida ma ya fitar ta hanyar mujahid daga Abdullahi dan Abbas. Ya ce na kasance ban saN ma’anar (فاطِرِ السَّماواتِ وَ الْأَرْضِ) {makagin sammai da kassai ba}[9] har sai da wasu larabawa kauye suka zo waje na suna jayayya kan rijiya, dayan su yana cewa ni na kage ta (أنا فطرتها،) dayan kuma yana cewa ni ne na farar da ita. [10]
Tarihi da hadisi ba su taba bamu labarin cewa Imam Ali (a.s) ya yi kai kawo wajen bada amsar tambayar da aka fuskantar zuwa gare shi ba, wanda hakan na nuna mutukar masaniyarsa da kasancewar sa kogi a cikin tafsiri da saninsa da ma’anonin ayoyin Ambato mai hikima, balle ma ya kasance yana neman kowa ya zo wajensa don sanin ma’anonin ayoyi da warware murdaddun bincike a yayin da ya kasance yana maimaita cewa: (ku tambaye ni kafin ku rasa ni).
Jalaluddini al-siyudi ya ce: mutum goma daga sahabbai sun yi shuhura a fagen tafsiri: Halifofi hudu da ibni mas’ud da ibni Abbas da ubayyi dan ka’abi da zaidu dan sabit da Abu musal Ash’ari da Abdullahi dan zubairu. [11] Amma halifofi wanda ya fi kowa rawaitowa daga cikin su shi ne Ali dan Abidalib (a.s) amma abin da aka rawaito daga sauran ukun (Abubakar da Umar da Usman) kadan ne sosai. Ta yiyu hakan ta faru ne saboda sun rasu kafin Ali dan abi dakllib (a.s)[12] kuma malam zahabi ya ce: Ali (a.s) ya kasance kogi ne na ilimi ya kasance mai karfin dalili da mai kubutaccen ta’awili, an ba shi kaso mai girma daga fasaha da khuduba da waka, kuma ya kasance mai nunanne hankali, da bisara zartatta a cikin boyayyun abubuwa kuma da yawa sahabbai kan koma zuwa gare shi a cikin fahimtar abin da ya buya da kuma fayyace abin da ya ba da matsala, kuma hakika Manzon Allah (s.a.w) ya yi masa addu’a. a yayin da ya sanya shi gomna a yemen yana mai cewa ya Allah ka tabbatar da harshensa ka shiryar da zuciyarsa sai ya kasance dacecce kuma abin shiryarwa, mai fayyace abubuwa masu rikitarwa, har sai da ya zama ana kafa misali da shi “a kwai wani lamari da ya gagari babaan Hasan!” kuma wannan ba abin mamaki ba ne hakika an rene shi a gidan annabta kuma ya sha ta mashayar masaniyarta kuma fitilar haskenta ta lullube shi, wata rana an ce wa Ada’u shin a cikin sahabban Manzo (s.a.w) akwai wanda ya fi Ali sani? Sai ya ce a a wallahi ban san shi ba, an karbo daga Abi Sa’idul Khudri daga dan Abbas yana cewa: idan wani abu ya tabbata gare mu ta hanyar Ali (a.s) ba ma barin sa mu dau na waninsa. Ibni Abbas ya ce: ma fi yawan abin da na sani na tafsiri a wajen Ali (a.s) na koyo. Kama ya ce Ali ya san ilimin da Manzon Allah (s.a.w) ya sanar da shi kuma Manzon Allah (s.a.w) Allah Ta'ala ne ya sanr da shi ilimi, don haka ilimin Annabi (s.a.w) daga Allah ne ilimin Ali (a.s) daga Manzon Allah (s.a.w) Allah ne ilimin na kuma daga Ali (a.s) ne. kuma ilimi na da ilimin sahabban Manzo (s.a.w) idan aka kwatantana shi da ilimin Ali bai wuce digo daya a cikin koguna bakwai ba. hakika an bawa Ali dan abi dalib kaso a cikin goma na ilimi kuma na rantse da Allah ya yi tariyya da mutane a cikin sauran kaso dayan cikin goman, wannan ne ya sa kowa yake bukatuwa zuwa gare shi. Shi kuma ya wadatu daga kowa. [13]
Daga nan ne zaka fahimci cewa ba zai yiyu a san sunayen halifofi uku daga cikin malaman tafsiri ba, saboda dakatawar su cikin da yawa daga cikin tafsirin ayoyin Ambato mai hikima da aka tambaye su a lokacinsu, kari a kan karfafawar da yawa daga cikin muhakkikai kan cewa fitattun masana tafsiri a zamanin sahabbai mutum hudu ne: Ali dan abi dalib (a.s) sa Abdullahi dan mus’udu da ubayyu dan ka’abi da Abdullahi dan Abbas. [14]
Hakika masana hadisi sun nakalto wasu tarin hadisan da suke fassara ayoyin Ambato mai hikima daga sauran sahhabi. [15]
Mihmmancin tafsirin sahabbai
Yana daga cikin abin da ya kamata a fadaka a kan sa shi ne kokaci ko matakin faroka wanda ya kasance a zamanin manzanci ya kasance lokacin ne na tarbiyya da koyarwa, musamman ma bayan hijirar Manzo (s.a.w) zuwa madina, hakika Manzo (s.a.w) ya kasance ya maida hankalinsa kuma ya tafiyar da rayuwarsa wajen tarbiyantar da sahabbansa masu girma da koyar da sau ladubba da masaniya da sunnoni da hukunce- hukunce kuma yana kokari ya mayar da su al’umma madaidaita don su kasance shedu kan mutane. Hakika Manzo (s.a.w) ya zo ne don {ya karanto musu ayoyin sa yana tsarkake su kuma yana sanar da littafi da hikima alhali da can sun kasance cikin bata mabayyani}. [16]. Babu shakka cewa shi amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ya gudanar da abin da ya kamata ya aiwatar na rantse da Allah a cikin sahabbansa akwai wadanda suka dosana daga iliminsa mai kwarara, lalle akwai wasu jama’a daga malamai da suka gaji iliminsa kuma suka dauki hikimarsa zuwa wasu gungu daga mutane. Da yake Manzo (s.a.w) shi ne makoma tilo a lokacin rayuwarsa al’umma ta kasance tana komawa zuwa gare shi don ta dosana daga iliminsa mai kwarara don haka ba sa jin cewa suna bukatuwa zuwa tafsiri, sai dai wasu daga cikin sahabbai haka ma wasu dada cikin makusanta daga sahhabi sun yi hasashen kimar tafsirin Annabi (s.a.w) don haka sai suka fara bibiyarsa amincin Allah ya kara tabbata a gare shi da kiyaye abin da suka samu daga gare shi na daga tafsiri, kowa bisa gwargwadon iyawar sa al’amarin da ya sa suka gadar mana tushe isashhe na tafsiri ba na wasa ba.[17] kuma za‘a iya ganin kima da darajar wannan tafsiri cikin manuniyar da zamu jero.

- Hakika da yawa daga cikin sahhabi sun ji tafsiri daga wahen Manzo (s.a.w) ba tare da wasida ba, duk da cewa wannan tafsirin gabaki dayansa be zo gare mu ba, kuma ba wanda ya sami damar kammala cikikken littafin tafsiri in ba Imam Ali (a.s) ba wanda ya rubuta littafin guda da ke kunshe da cikekken tafsirin Kur'ani, amma duk da haka ana ganin dan abin da wasu daga cikin tsurarun sahabbai suka fitar a matsayin taskar ilimi babba a fagen ilimomin Kur'ani mai girma. [18]
Shafiwu dan salma ya ce: na ji ibni mas’udu yana cewa hakika na dauki sura saba’in da wani abu daga bakin Manzon Allah (s.a.w). [19].
An karbo daga Katadata daga Anas Dan Malik cewa Manzon Allah (s.a.w) ya ce da babana hakika Allah ya umarce ni da in karantar da kai sai ya ce ashe yanzu Allah ne ya ambata maka sunana? Sai ya ce Allah ne ya fada mini sunanka sai baba na ya fara kuka. [20]

- Wasu daga cikin sahhaban Annabi (s.a.w) sun kasance suna lazimtarsa a lokacin da Kur'ani yake sauka sai suka san sababan saukar ayoyi da yanayoyin da suke kewaye da saukar ayoyin. [21]. mu’ammar ya rawaito daga wahabu dan Abdullahi daga baban dufailu ya ce na halarci Ali yana huduba, alhali yana cewa: ku tambaye ni kafin ku rasa ni na rantse da Allah ba za ku taba tambaya ta wani abu ba face na baku amsarsa, ku tambaye kan littafin Allah na rantse da Allah babu wata aya face na san cewa da daddare a saukar da ita ko da rana ko a kwari ko a kan dotse aka saukar da ita.[22]
- Mutane sun kasance suna magana da yaren larabci mai fasaha a lokacin Manzo (s.a.w) al’amarin da ya sa ya yi musu kyakkyawar shimfidar fahimtar Kur'ani, daga nan ne Manzon Allah (s.a.w) tuni ya tabbatar da abin da larabawa suke fahimta tun a farko bisa al’adarsu. [23] an karbo daga Ali (a.s) ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya aika ni zuwa yamen ina matashi ya ce: sai na ce: ka aika ni wajen mutanen da wani abu zai iya faruwa tsakninsu kuma ni ban iya hukunci ba sai ya ce da sannu Allah zai shiryar da harshen ka kuma ya tabbatar da zuciyarka. [24] an karbo daga abi ubaida daga baban yazidu ya ce: Inbi Abbas ya kasance idan aka tamabaye shi idan ya zama tambayar ta shafi Kur'ani sai ya bada amsa idan ba a cikin ba ne kuma ya zama ya sami wani ahadisi daga Manzon Allah (s.a.w) sai ya bada amsa idan kuma be samu ba sai ya bada amasa da ra’ayinsa. [25]
- Lazamtar sahhabai ga Manzon Allah (s.a.w) da kuma kiyayewar su ga abin da yake zuwa daga gare shi na da tasiri mai girma cikin masaniyar su kan abubuwa masu yawa da daga rayuwar sa ta ilimi da ta nazari al’amarin da ya saukake musu fahimtar kar’ani mai gairma da sanin manufofinsa.
Don haka za’a iya cewa lalle sahabbai sun dauki nauyi mai girma kan Kur'ani mai girma da bangarori biyu kamar haka:-
- Kiyaye Kur'ani da kare shi daga canjawa da jirkatawa.
- Yin tafsirin Kur'ani da yin bayanin sa ga mutane da warware kullin cikinsa.[26]
Kebance-kebancen tafsiri a lokacin sahabbai
Tafsirin lokacin sahabbai ya kebantu da lamuran da ba dukkan su ne suka samu a cikin sauran tafsirai ba.
Na daya: saukinsa ta hanyar da bai wace wasu ‘yan kalmomi ba wajen warware abubuwa masu rikitarwa ko kawar da rudani, a cikin bayani gamsashe da mai warakarwa tare da kamala da cikar ma’ana idan aka tambayi dayan su kan ma’anar “wanda be yi karambanin yin zunubi ba” sai ka ga ya amsa cikin gaggawa yana mai cewa “wanda bai aikata sabo ba” ba tare da ya koma zuwa tsago kalma ko bayyana wani dalili ko sheda da makamancin haka ba, wannan lamari ne da mafassara duka saba da shi kuma idan aka tambaye shi kan sababin saukar aya sai ko kuma abin da ta kunsa baki daya sai ya amsa kai tsaye ba tare da kai-kawo ba kuma cikin sauki ba tare da murdiya ba kamar yanda marubutan baya suke yi.
Na biyu: kubutarsa daga jayayyar ta sabani bayan kadaitakar majingina da mafuskanta da sanadi a wancen zamanin don a zamanin farko babu sabani tsakanin sahabbai kan zabar majingina, kuma ba su yi hannun riga ba a mafaskunta da hadafi, dukkanin bangarorin sahabbai sun hadu kan layi daya madaidaici mikakke dodar babu wani abu da zai sa a sami sabani da cin karo a cikin ra’ayi musamman ma da ya zama Manzo (s.a.w) ne ya ladantar da su bisa lazimtar shiriya.
Na uku: wufitar sa daga tafsiri da ra’ayi da ma’anar dankakawar da ba a jigina ta da Ambato mai hikima ba, na daga wani irin makahon bangarencin ko kuma yin ojoro a cikin lamari wanda manyan zababbun sahabai suka kasance suna nisantarsa.
Na hudu: Tsaftatar sa daga kissoshin isra’iliyanci daga cikin akwai kissoshin isra’iliyanci wanda ba su da wata mafaka da zasu labe don su kutsa cikin musulmai hakika wannan lokaci ya wofinta daga dasisar yahudawa, al’amarin da ya rika jijjuyawa lokaci bayan lokaci, kuma dasisar siyasa ma ta taka rawa wajen yada kissoshin yahudawa. [27]
Na biyar: tabbacin rashin tsammanin shakku da daukar tsammace-tsammace da bayyana madogara kura-kuru dinta da yalwatar hanyoyin yin bayani da dalilan tafsirin da ake gabatarwa a wancen zamanin saboda saukinsa da amincimsa daga kullin ko murdiya da ta shiga cikin sa a zamanin da ya biyo baya. [28]
Na shida: Tafsirin wannan marhalar ya kasance a karkashin inuwar ilimin hadisi da ilimin nakaltowa kuma tafsiri bai zarce sama da kasancewarsa ilimin nakalto ruwaya Annabi (s.a.w) ta tafsiri ba, ba tafsiri da ma’anar da ake nufi ta yanzu ba (ta isdilahi ko yaren ilimi) kuma wannan salon na tafsiri ana kiransa tafsiri da abin da aka samo daga Manzon Allah (s.a.w) ta wannan dalilin ne sabani ya yi karanci a cikin sa.[29]
Na bakwai: A cikin sahabbai babu wanda ya hada cikakken littafin tafsiri saboda kwanakin rayuwar Manzon Allah (s.a.w) ba su bada damar yin haka ba ta wani bangaren da kuma rashin bukatuwar al’umma musulmi - wandanda suke ba su dade da kafawa ba - zuwa sanin dukkani wani loko da banbarorin Kur'ani ba kari kan yadda tunanen mutane yuke kasa a wannan lokacin ta yadda tunaninsu bai ka ga risker abubuwa masu zurfi na Kur'ani da murdaddau abububuwan da ke cikin sa ba ballatana su yi nutso cen cikin kogonsa. [30]
Na takwai: Sahabbai ba sa ganin akwai bukatuwa ga fadadawa wajen ba da amsa ba, hakika sun kasance suna isuwa da takaitawa suna nisantar kutsawa cikin binciken falsafa da kalam da irfani da ilimi dss..... ba su cakuda kua’ani da sakamakon wadancen iliman ba, duk da cewa an dan tsittsinci maganganu na adabi kamar yadda hakan ya zama shi ne hanyar Abdullahi dan Abbas ta tafsiri, sai dai hakan wani kokari ne da be kai matsayin bin tafrkin adabi cikakke ba. [31]
Yana daga abin da ya kamata a ambata cewa lalle wadannan siffofi kyawawa ba su gushe abin dogaro a tsaka-tsakin mafassa ba, kai suna ma daga cikin abin da ya sa wasu tafsiran suka yi fice da shi, kuma ba a taba dauke hannu daga kansu ba duk da canje-canjen tunani da ci gaban da aka samu a fagen tafsirin Kur'ani mai girma.

[1] Ibni manzur Muhammad dan karam, a cikin lisanil arab j 1 sh 519-529 bairut bulnon.
[2] Al-ragin isfahani, Husain dan Muhammad , mufaradatu alfazul Kur'ani shafi na 476 bairut, darul kalam, bugu na farko.
[3] Alkasimi, Muhammad jamaluddin, kawa’idul hadis sh 49 bairut kutubul ilmiyya 1414. Abu rayya shekh Mahmud alhadis walmuhaddisun, sh 129. Darul kutubul arabiyya; abu rayya shekh Mahmud adhwa’u alas sunnal muhammadiyya sh 348. Misra darul ma’arif, 1406.
[4] Ibni silah usman dan aabdurrahaman, ma’arifati anwa’I ulumul hadis (mukaddimar ibni silahi) tahkikin utar, nurud dini, sh 293 suriya darul fikri 1406.
[5] Alkhudri bak, Muhammad , usulul fikihi, sh 224, misra, maktabatul tijariyyal kubra, 1389.
[6] Marwati, saharab, fajuhishi, firamune tarikhi tafsiri kur’an, sh 84, Tehran, nasri ramz, bugu na farko 1381.
[7] Absa aya ta 24- 29.
[8] Shadibi, abu ishak, almuwafakat, j 2 sh 139, daru ibni affan, bugu na farko 1417.
[9] Surar an’anmi aya ta 14.
[10] Dabari, Muhammad dan jariri, jami’ul bayan fi tafsiril Kurani j 7 shafi na 101, bairut darul ma’arifa buguna daya 1412. Da suyudi , jalaluddin , alitkan fi ulumul kur’an j 1 sh 373 bairut darul kitabul arabi, bugu na biyu, 1412.
[11] Al’tkan fi ulumin Kurani j 2 sh 466; zahabi, Muhammad Husain, altafsir wal mufassirun j 1 sh 63, bairut, daru ihya’il turasil arabi, ba tarihi,; zarkani, Muhammad abdul’azim manahilul irfan, fi ulumul Kur'ani j 1 sh 482, bairut daru ihya’I turasul arabi, ba tarihin bugawa.
[12] Al’tkan fi ulumin Kurani j 2 sh 466.
[13] Altafsiri wal mufassirun, j 1 shafi 63 – 64.
[14] Fajuhish firamune tarikhi tafsir Kur'ani shafi, 87 – 88.
[15] Amin, Ahmad, fajrul islam, shafi 202, darul kutubul arabi, 1412. Da fajush, firamone tahihi tafsiri Kur'an. Sh 88.
[16] Ali Imran aya ta 164.
[17] Fajush, firamone tahihi tafsiri Kur'an. Sh 88.
[18] Masdarin da ya gaba ta shafi na 89.
[19] Ibni hajar askalani, Ahmad bini Ali , fatahul bari fi shahi sahihul buhari, j 9 sh 48 bairut darul ma’arifa, 1379.
[20] Alkushairi, nishaburi, muslim dan hajjaju, musnadus sahihul mukhtasar da nakaltowar adadi zuwa adali, zuwa Manzon Allah (s.a.w) (sahihu muslim) wanda ya yi takkiki shine abdul baki, Muhammad fu’ad, j 4 shafi 1915. Bairut daru ihya’il turasul arabi, ba tarihi.
[21] Fajush, firamone tahihi tafsiri Kur'an. Sh 89.
[22] Ibni abdul barri, yusif dan Abdullahi, al’isi’ab fin ma’arifatil ashab, tahkikin bijawi, Ali dan Muhammad j 3 sh 1107, bairut darul jalil bugu na daya 1412.
[23] Fajush, firamone tahihi tafsiri Kur'an. Sh 90.
[24] Shadibi, Ahmad dan Muhammad , musnadi Ahmad bini hambal tahkikin shakiri, Ahmad dan Muhammad j 1 sh 459, kahira, darul hadis nugu na daya 1416.
[25] Alisaba fi tamyizus sahaba, j 4 shafi 130, Ahmad da Ali da hajar askalani, (ya rasu 852) tahkikin adil , Ahmad dan abdul maujud, da Ali Muhammad mu’awwadh, bairut darul kutubul ilmiyya, bugu na daya 1415/ 1995.
[26] Fajush, firamone tahihi tafsiri Kur'an. Sh 99.
[27] Altafsiri wal mufassirun, j 1 shafi 63 – 64.
[28] Ainihin Masdarin da ya gaba ta.
[29] Argunun asmani, jastari, dar Kur'an, irfan wa tafsiri irfani, shafi 98; dahiri habibullah, darsahaye az ulumu Kur'an j 2 sh 24, kom, darul uswah, bugu na daya 1377.
[30] Mutawalli, Abdulhamid Mahmud, adhwa’un ala manahiji ba’adhul mufassirun, min zawaya ulumul Kur'an sh 95, islamiyya. 1420; Argunun asmani, jastari, dar Kur'an, irfan wa tafsiri irfani, shafi 98.
[31] Masdarin da ya gaba ta shafi na 98 - 99.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga