Please Wait
Dubawa
13041
13041
Ranar Isar da Sako:
2009/10/20
Takaitacciyar Tambaya
Shin annabi yana sada zumunci ga abulahabi?
SWALI
Shin annabi yana sada zumunci ga abulahabi?
Amsa a Dunkule
Duk wani aiki da kan karfafa alaka tsakanin ‘yan uwa na jini, a na kiransa sada zumunci. Musulunci ya baiwa sada zumunci matukar mahimmanci sosai ta yadda ya hana katse shi ko ga kafuri ne. Sai fa in kafurin makiyi ne, mai kulle-kulle don yakar Musulunci. Idan haka ne Musulunci bai tilasta yin zumunci dashi ba ko yin zumunci da shi. Anan bayan da suratul Masadi ta sauka a kan Abulahabi da matarsa za a ga yadda Annabi (s.a.w) ya katse dangantaka da su sakamakon hakan.
Amsa Dalla-dalla
Zumunci yana nufin saduwa da damfarawu da juna; Abinda ake nufi da zumunta, su ne makusanta, Duk wani aiki da a kan karfafa alaka tsakanin yan uwa na jini a na kiransa sada zumunci. Musulunci ya bai wa sada zumunci matukar mahimmanci sosai. An ruwaito daga Imam Sadik (a.s)., cewa wani mutum ya zo gunsa ya ce: “Ina da dangi da ba bisa tafarkina suke, shin suna da hakki akaina? Sai ya ce: (a.s). Sosai kuwa! Babu abinda zai tsinka shi. Idan kuma bisa tafarki daya kuke ya na da hakki biyu a kanka, hakkin zumunta da na Musulunci”.[1]
Yana cewa (a.s). a wata ruwayar: “Kada ka yanke zumuncinka koda kuwa an yanke naka. Kana Imam Ali har-ila-yau ya ce: Ku sada sumuncinku koda su sun katse muku”.[2]
Sai dai tambaya a nan ita ce: Shin Musululci yana karfafa yin zumunci ko da da kafuri ne, da mushriki mai adawa mai yakar Musulunci?
Shin Manzon Allah (s.a.w) yana dabbaka wannan sunnar ga baffansa Abulahabi wanda ya kasance -bisa bakinciki- mushriki ne da ya na ce bisa yin shirka da tursasawa ga Annabi (s.a.w) da musulmi ta hanyar ci musu zarafi matuka da kuma aikata wasu laifuka da ba zasu kirgu ba ko kuma a’a?
Amsa anan ita ce: A’a. Ga hujja.
1. Allah Ya ce: “Baya yiwuwa ga Annabi da wadanda suka yi imani su nemi gafara ga mushrikai ko da sun kasance ma’abuta kusanci bayan ya tabbata a garesu cewa su ‘yan wuta ne”[3]
Kuma a bayyane yake cewa neman gafara da yin addu’a ga wani na daga cikin matakai na neman gafara.
Ruwaya ta nuna mafi karanta daga cikin matakan sada zumunci shi ne mika gaisuwa; assalamu alaikum[4] ko basu ruwan sha.[5] Ma’ana aikata hakan kan tabbar da sada zumunci. Kana ya zo aruwaya cewa duk wanda ya gaza saduwa da danginsa, to sai ya sadu da su ta hanyar yi musu addu’ar fatan alheri da neman gafara a garesu. Kana za’a iya fahimta a ayar mai girma ce wa baikamata ga Annabi (s.a.w) ya nema wa mushrikai irin su Abulahabi gafara ba, domin adwarsu ga Annabi da debe tsammani daga shiriyarsu.
2. Allah (s.w.t) Ya ce: “Nenam gafar Ibrahima ga babansa bai kasance ba sai na wani wa’adi, a sadda ya bayyana a gareshi cewa makiyin Allah ne sai ya baranta daga gareshi. Hakika Ibrahima mai yawan komawa ne ga Allah mai kuma juriya.[6]
Ayar tana nuna Annabi Ibrahima (a.s), ya nemi gafara ga baffansa, ya na kuma daya daga cikin hanoyoyi na sada zumunci. Amma a sanda ya bayyana a gareshi cewa baffansa makiyin Allah ne sai ya baranta daga gareshi; ya dai na hulda da shi.
Abulahabi ya fara adawar tasa ce ga Annabi (s.a.w) a shekara ta uku bayan aike a sanda Annabi ya karkatar da kiransa ga danginsa na kusa. Har a lokacin Annabi (s.a.w) bai riga ya baranta daga baffan nasa ba. Amma bayan da adawarsa ta bayyana kuma ta ci gaba da habaka da yin gaba da yakar Annabi da sakonsa. Bayan saukar surar Tabbat-yada tana zargin Abulahabi da matarsa, sai Annabi (s.a.w) ya katse hulda da shi.
3 An ruwaito daga Imam Assajad (a.s). a salati ga Annabi (s.a.w) yana fadi a cikinsa; “Kuma ya zage yana addu’a zuwa gareKa har ya bude kansa. Ya yaki danginsa domin samun yardarKa* Ya katse zumuncinsa don raya AddininKa* Ya nesantar da makusanta don jayayyarsu* Ya kusantar da na nesa don amsar kiransu ga reKa* Ya kaunaci na nesa dominKa* Ya yi kiyayya da na kusa domiKa.[7]
Marigayi Sayyid Ali khan a sharhin Sahifa Sajjadiya ya fassara kalmomin kamar haka: “Ya katse zumuncinsa katsewa, ya yi watsi da su, ya kyale su ya daina yi musu kyautayi, Manzon Allah (s.a.w) ya yi hakan ga jama’arsa da danginsa da iyalinsa Kuraishawa da banu Abdulmudallib, wadanda suka karyata shi suka yakeshi don su bushe hasken Allah Sai ya yakesu ya kashe masu yawa daga cikinsu a Badar da Uhudu kuma a ka kame mutane masu yawa daga cikinsu, ba tare da ya tausayawa wani ko sassauta masa ba domin zumunci. Fushi ya ke don Allah don neman yardarSa[8].

[1] RaiShahari/Muhammadi Mahdi/ Mizanulhikma /j4/sa84.
[2] Wasa’ilush Shi’a /j11/ sh 175.
[3] Attauba 113/ RK. /Dabadaba’e/ Muhammad Husaini/ Almiza’an/ j9 da 10 /sh 282/ Manshurat Zawil Kurba /BJ/ BT.
[4] “Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “Ku sada zumuncinku a nanan Duniya koda ta hanyar mika gaisuwa ne“ Biharul Anwar /j71 /sh104.
[5] Imam Sadik (a.s). yana cewa: “ku sadar da zumunci koda ta hanyar bada rowan sha ne” Biharul Anwar /j74 /sh117.
[6] Attauba: 114 / “Hakika kyakkyawan kuyi ya kasance a gareku daga Ibarahima da wadanda suka yi imani da shi a yayin da suka cewa jama’arsu lalle mu mun barranta da ku da abinda kuke bauta wa da ba Allah ba. Kuma gaba da kiyayya sun bayyana tsakanimmu da ku har abada har sai kun yi imani da Allah Shi kadai, har sai sanda Ibrahima ya ce wa baffansa zan nema maka gafara amma ba zan iya kare maka komai daga gurin Allah Ba. Ubangiji gareKa muka dogara a gunka zamu maida lamura makoma tana gareKa Mumtahana: 4.
[7] Sahifa Sajadiya (a.s). /sh 48/ tarjamar Injiniya Yasir Arab / dab’in farko 1380, Intsharat Kalbi.
[8] Alhusen Madani Shirazi /Sayyid Ali Khan Rayadussaliken /j1/ sh 456,466. Dab’e 6/ Jama’atul Madrasataini.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga