Please Wait
22287
Musulunci yana da kalmomi da suka hada da "kasa" da kuma "yanki" da "al'umma. Kasa a tunanin fikirar musulunci wuri ne guda daya, kuma dukkan iyakokin da ake da su ba su da wani tasiri wurin rusa kasancewar kasar musulunci da musulmi abu guda ne. kuma wannan kasa a bisa koyarwar musulunci dole ne ta kasance karkashin jagorancin shugaba daya ma'asumi (a.s), kuma wannan shi ne babban buri da hadafin hukumar Imam Mahadi (a.s).
A lokacin boyuwr Imam Mahadi (a.s) idan an samu damar kafa wannan kasa ta musulunci dunkulalla guda daya kuma aka samu maslahar musulunci wurin tafiyar da wadannan kasashe a matsayin kasa daya, to ya hau kan malami ya tafiyar da ita a yadda take dunkulalla.
Kuma idan wani yanki ne kawai aka samu damar tafiayarwa ta hannun malami to bisa maslahar musulunci da ta dace, haka nan dai ya hau kan malami ya kafa hukuma bisa wannan yankin. Don haka ne bisa asasin tsarin siyasar musulunci kasa dukkanta abu guda ne.
Amma kuma idan ya kasance kasashe a rarrabe suke ko a yanayin garuruwa ne, to bisa maslaha ya kasance wani nauyi na tilas da ya hau kan malami ya tafiyar da wannan yankin bisa dogaro da siyasar da take gudana.
A yau a bisa taswirar siyasar wannan zamani kasashe sun rarrabu gida-gida, kuma sun sanya musu wasu iyakoki da suka kafa dauloli daban-daban masu bambanta da juna, kuma kowane wuri yana da tasa hukumar. Wadanda suke rayuwa a wannan yankunan suan da zama ne a matsayin 'yan kasa[1], saura kuwa 'yan waje[2] (wadanda ba 'yan kasa ba), hukunce-hukunce wasu sun shafi 'yan kasa ne, wasu kuwa sun shafi 'yan waje ne.
Shin wadannan dokokin suna da wata kima da ake la'akari da ita, to yaya suke ne a bisa mahangar musulunci?
A amsar wannan tambayar muna iya cewa: Musulunci yana ganin kansa a matsayin addinin duk duniya, kuma duk duniya yana ganin kasarta ne kuma dole ne a karbe shi a nan. Kuma duk inda aka samu mafi yawan mutanen wurin musulmi ne, to ana kiran wannan wurin kasar musulunci, daya bangaren kuwa wanda kafirai suak fi yawa ana kiran sa kasar kafirci. Don haka babu wata iyaka a musulunci sai iyakar akida, kuma akida ce kawai take da iyaka a bisa tsarin siyasar musulunci, kuma wannan shi ne musulunci kawai.
"Addini a wurin Allah shi ne musulunci"[3], musulunci yana da ma'anar doron kasa maimakon kasa[4], ya kawo ma'anar al'umma ne maimakon 'yan kasa[5]. Wato musulunci bai yarda da bambanci tsakanin al'ummu da kasa da mutane ba, abin da ya yarda da shi kawai shi ne akida.
Kasar musulunci abu guda ne, kuma wannan iyakokin ba su da wani tasiri a cikin kadaitakar kasar musulunci.
kuma wannan kasa a bisa koyarwar musulunci dole ne ta kasance karkashin jagorancin shugaba daya ma'asumi (a.s), kuma wannan shi ne babban buri da hadafin hukumar Imam Mahadi (a.s).
A lokacin boyuwr Imam Mahadi (a.s) idan an samu damar kafa wannan kasa ta musulunci dunkulalla guda daya kuma aka samu maslahar musulunci wurin tafiyar da wadannan kasashe a matsayin kasa daya, to ya hau kan malami ya tafiyar da ita a yadda take dunkulalla.
Kuma idan wani yanki ne kawai aka samu damar tafiayarwa ta hannun malami to bisa maslahar musulunci da ta dace, haka nan dai ya hau kan malami ya kafa hukuma bisa wannan yankin. Don haka ne bisa asasin tsarin siyasar musulunci kasa dukkanta abu guda ne.
Amma kuma idan ya kasance kasashe a rarrabe suke ko a yanayin garuruwa ne, to bisa maslaha ya kasance wani nauyi na tilas da ya hau kan malami ya tafiyar da wannan yankin bisa dogaro da siyasar da take gudana.
Karin bayani:
1. Mahdi Hadawi Tehrani, Wilayat wa Diyanat, Mu'assar Al'adun Khaneye Khirad, Kum, bugu na biyu, 1380.