Please Wait
8140
Wannan lamarin ba zai yiwu ba ga hukumar duniya ta Imam Mahadi (a.s) saboda dalilin faduwar wadancan hukumomin yana komawa zuwa ga zaluncin wadannan hukumomin ko kaucewarsu ga asasin adalci, ko kuma saboda yaudarar mutane ta hanyoyin isar da sako wacce ta haifar da bambanci tsakanin mutane da hukumarsu, wadannan abubuwan dukkaninsu ba zasu yiwu ba ga hukumar lokacin Imam Mahadi (a.s) ta duniya.
Faduwar hukumomi da rushewarsu yana yiwuwa ta fuskoki biyu ne:
a) Gushewar jiga-jigan hukuma yana kasancewa saboda zalunci da danniya da tatsiya wacce masu hukuma a hannu suke yi ne, da ninsantar su daga hanyar kwarai da adalci sakamakon karkacewa, ko kuma sakamakon juyin al’umma da kawar da hukumomi, ko kuma saboda kasa ta samu harin wasu daga waje suka kayar da hukuma, don haka ne zamu ga mafi yawan dauloli da suka fadi a tarihi sun samu irin wadannan dalilai ne. Misailn abin da ya kawar da daular Umayyawa a hannun Abbasawa zamu ga zalunci ne da rashin adalci da ya bayyana karara a lokacin daular umayyawa.
Ko kuma faduwar daular abbasawa a hannun Magol, ko sasanawa a Iran wacce ta fadi ta rushe saboda yakin nan na harin sojojin musulmi, wannan kuwa saboda zalunci da tatsiya da ya kai ga hatta da al’umma ta ki taimaka wa wannan hukumar saboda rashin dogaron al’umma, don haka sai al’umma ta ki taimaka mata da kare ta, kai al’umma ta kasance tana zaune cikin hakuri ne tana jiran wanda zai zo ya tseratar da ita daga dannniyar azzalumai ne ma. Haka nan ma lamarin yake game da tsarin shahin shahinci yayin da ya fadi a hannun al’ummar da ta kasance tana tsananin kishin adalci da samun ‘yanci da ‘yantuwa, bisa jagorancin marigayi jagora Imam Khomain (k.s).
Don haka ne sai muka samu hukumomi azzalumai sun fadi ta daya daga wadannan hanyoyin; imma dai ta hannun juyin al’umma ko kuma ta hanyar yakin masu hari daga waje da rushewar masu kariyar cikin gida.
b) Na biyu daga abin da yake kai wa ga faduwar hukuma shi ne yaudarar al’umma da fadar da su ta hanyar isar da jita-jita da watsa labaran karya har sai hukuma ta rusu, kamar yadda aka jarrabi hukumar Imam Ali (a.s) da wannan yakin na yada jita-jita da karerayi da makiya masu gaba da Imam Ali (a.s) suka rika yadawa, hada da yaki da hare-haren da makiya suka tilasta masa a wannan zamanin wanda ya kai ga cire wa al’umma tunani da lura da hankali cikin lamurran da suke kaiwa su komo, hada da cewa Imam Ali (a.s) kansa bai yarda da abin da ya faru na karbar sha’anin hukuma wanda ya gabata kafin zuwansa ba, ta yadda mafi yawan jagororin al’umma da zabubbun mutanen al’umma sun samu karkacewa daga adalci, sun karkace daga hanyar, sun samu ruduwa da duniya, lamarin da ya sanya aikin kawo canji da gyara da tsayar da adalci da fuskantar wadanda suka zama a saman jagorancin al’umam (da suka karkace daga karkarta ya zama abu mai wuyar gaske) har wannan kokarin canjin ya haifar da matsaloli da wahaloli da bala’o’i masu yawa da tayar da fitina don yakar Imam (a.s). Sannan a sakamakon duk wadannan abubuwan da aka kawo na tsanani da tsanantawa sai ya kasance al’umma ta kasa gane hakikanin gaskiya, sai ta ki daukar mataki mai karfi ga wannan gabar da yakin jita-jita[1], wanda daga karshe ya kai ga shahadar Imam Ali (a.s) da kawo karshen hukumarsa.
Amma idan mun duba hukumar duniya ta Imam mahadi Allah ya gaggauta bayyanarsa, zamu ga babu abin da yake kawar da hukumomi ya kayar da su na farko tabbas.
Haka nan abu na biyu shi ma babu shi, domin a wannan zamanin mutane zasu kai kololuwar samun wayewa da hankali da tunani, da samun matukar fahimta da wayewar da sanin makamar siyasa, kamar yadda hukumarsa zata kasance ta kame lamarin isar da sako da shiryarwa, da gudanar da hukuncin musulunci, da aiwatar da dukkan abubuwan alheri na musulunci kamar umarni da kyakkyawa, da hani daga mummuna, don haka sai a rasa wani sabani tsakanin al’umma da hukumar Imam mahadi (a.s), daga karshe sai dalilin rushewar hukuma na biyu ya kawu ke nan.
Sai dai shedan zai wanzu yana mai kulle-kulle, yana yi wa mabiyansa waswasi masu biyayya ga tafarkinsa, kuma yana samun damar yaudarar wasu, sai dai galibin mutane zasu kasance ba su karkata ba, suna masu watsar da wasa da hankali da shedan yake yi da makircinsa[2].
[1] Dr. Sayyid Mukaddam Shahidi, Ali (a.s) a harshen Ali (a.s), ko kuma rayuwar Imam Ali na ofishin al’adun musulunci, 1379 H.Sh, shafi: 64 – 160.
[2] Duba Littafin “Mahdiye inkilabe buzurg” na Nasir Makarim Shirazi, da Ibrahim Amini, Dadgustare Jehan. Domn samun karin bayani.