advanced Search
Dubawa
5453
Ranar Isar da Sako: 2016/07/15
Takaitacciyar Tambaya
Ya Ma’aunin Ubangiji ya ke wajen zabar wasu gungu daga cikin mutane domin ya ba su mukamin Annabta?
SWALI
Magana kan cewa Allah madaukaki na yi wa wasu daga cikin mutane wahayi ko kuma cewa ya zabe su ya fifita su da wahayi kan sauran mutane; shin akwai wata magana a cikin Kur\'ani da ta zo kan haka? Kuma saboda me ya fifita su? Bisa wane ma’auni? Shin su ma mutane ne kamar kowa ba su da banbanci da sauran mutane?
Amsa a Dunkule
Nufin Allah da iradar sa na da tsari da kaidoji (ko dokoki), kuma ayyukan sa ba mara sa ma’ana da manufa ba ne, ballantana ma bisa tsarin na hikima da ilimi da tausayi yake zaratar da komai. Don haka ne ma yake zabar wasu daidaiku daga ma’abota kamaloli na gari (kamalolin da Allah yake so) daga cikin mutane domin ya ba su matsayin Annabta, wasu daga cikin wadannan siffofin na nagarta sun hada da:- Ikhlasi, Tsayuwa Kan Addini Gaskiya, Sallam Wa Allah Ta’ala, Gode Masa, Tsarkakakkiyar Zuciya, Tsayawa Kyam A Lokacin Jarrabawa, Gaskiya, da sauransu.
 
Amsa Dalla-dalla
Asalin tarinin wannan jigo yana komawa ne zuwa cewa Allah madaukiki ya zabi wasu daga cikin mutane da yake saukar musu da wahayinsa kuma ya fifita su kan sauran mutane saboda wannan lamari mai mihimmnaci. Tabbas wannan zabin ya kasance biya asasi wasu ka’idoji. Kafin mu ambaci wasu daga cikin wadannan ka’idijin ko siffofi na kamala ya zama lalle mu waiyayi abubuwa masu zuwa:-
Na daya. Bisa koyarwar addini; Na daya. Abin da Allah ke so kuma yake nufi shi ne ke gudana a cikin al’amaran duniya kuma shi ne ke zartar da komai kuma shi ke hukunta kowa. na biyu; Allah ya sanya wa ko wane irin abu dokoki da sunnar da yake gudana a kan ta wanda ko wani abu na gudana ne bisa tasa dokar. Don haka abubuwan da Allah ke nufin ya aiwatar ya sanya shi bisa tsari da ka’odoji. kuma ayyuka mahalicci ba su taba zama marasa dalili ko hadafi ba. ballantana ma ayyukansa sun kasance bisa hikima[1] da da ilimi[2] da ludufi[3].
Na biyu: Akwa ayoyi da yawa a cikin Kur'ani da suka dauke da magana kan jiga-jigan lamura na asasi da suke da tasiri ga mutum tun daga duniyar gina asasin rayuwa; kamar su: halitta, samarwa, shiriya, bata, rahama, falala, fifiko, mulki, hukuma, buwaya, kaskanci, aiko mala’iku ga wasu mutane (samar da alaka ta musamman tsakanin Allah da wasu daga cikin bayi) zabar wasu mutane.....
Kuma ko wane daga cikin wadannan abubuwan da aka anbata na da yana bukatar kulawa da tsari na musamman daga ubangiji wanda zabin nubangije ke kunshe cikinsa.
Bari mu bada misalin wannan. Ya zo a cikin Kur'ani cewa {Allah na halittar abin da ya so kuma ya na zabar wadanda ya ga dama, kuma zabi ba a haunnu su (su bayi) yake ba wato bayi ba su da zabi a gefen zabin Allah, tsarki ya tabbata a gare shi ya buwaya daga abin da suke siffanta shi da shi}[4].
Ko kuma fadin sa madaukaki dangane da shiriya: {hanyar shiruya a hannun Allah ta ke (shi yake nuna wa bayinsa ita), amma kuma wasu sun kauce mata da Allah ya ga dama da ya shiryar da ku baki daya (amma tilastawar ba ta da amfani)}[5]
Ma’anin zabar annabawa
Allah madaukakin sarki yana zabar bayinsa da yake ba su kulawa ta musamman bisa ilimi da da hikima da rahama. Amma wannan zabin ba zai zama ya dace da kowa ba, domin Allah shi ne karshen kamala kuma mahallicci kuma yalwata rahamarsa da nau’o’in ni’imominsa zuwa ga bayinsa na daga cikin siffar da ke damfare da zatinsa mai tsarki. Kuma yana so shi ma dan’adam ya kai ga samun kamala, kuma samun wannan rahama daga wajen ubangiji na bukatar cancanta da yananyi na musamman ga mutmuni da za a bawa wannan babar baiwa.
Tabba Allah yana zabar mutane bisa irin nasa ma’aunin na ubangijintaka domin su yi babban aiki mihimmi kamar a aiko shi a matsayin Manzo ( dss. A tsawon dubban karnoni manzanni da dama sun shude wadanda ba kawai sunan su yazo a cikin tarihin dan adam ba ne, kai hatta ma tasirun su ya wanzu karnoni da dama sun zama maja ragamar al’ummar da suka zo bayansu tsawon karnoni wadanda da su ake koyi ba tare da sun yi amfani da dukiya wajen tabbatarda samuwar su a cikin zukatanm mutane ba ta hanyar wayo da dubara don su jawo mutane zuwa gare su har su zama su kowa ya fi so ba.
A nan zamu kalli ayoyin Kur'ani da hadisai don mu Ambato wasu daga cikin ma’aunan da bisa asasin su ne Allah Ta'ala ya ke zabar annabawa daga cikin mutane kuma yake fifita su kan wasu.
  1. Sallamwa Ubangiji
Ma’anar musulunci shi ne sallamawa ubangiji kan duk wani yanayi da aka zaba masa na daga hukunci da kaddara da kuma ko me aka shar’anta masa na daga umarni da hani[6]. Dangane da sallamawa (ubangiji) mutane sun kasu zuwa darajoji da matakai mabanbanta, don me kuwa mika wuya da imani ba za su zama bisa darajoji mabanbanta ba? Imam Ali (a.s) yana cewa a wannan fagen: ”zan yi bayani wani mataki da musulunci yake da shi wanda ba wanda ya yi shi kafin ni kuma ba wanda zai yi shi a baya na, musulunci shi ne mika wuya, kika muya shi ne gasgatawa, gasgatawa shi ne yakini, yakini kuma shi ne aiwatarwa kuma aiwatarwa ita ce yin aiki. Hakika mumini ya karbi addinin sa daga wajen ubangijinsa ba daga ra’ayinsa ba, ya ku mutane ku riki addininku ku riki addininku..”[7].
Ga misali zamu kawo: Annabi Ibrahim (a.s) na daga cikin zababbaun annabwan, lokacin da mahaliccinsa ya ce da shi ka mika wuya sai ya ce na mika, {na mika wuya ga Ubangijin talikai}[8]. Daga nan sai ya cimma matakin zabi sai aka zabe shi don haka sharadin cimma matakin zabi shi ne cimma matakin mika wuya. Annabi Ibrahim (a.s) ba bayahude ba ne muka ba banasare ba ne sai dai ya kasance mai bin madaidaiciyar hanya kuma musulmi.[9] Ya kasance mabiyin tafarki madaidaici kuma wanda ba wuce iyaka a cikinsa kuma ba gaza wa daga iyaka. kuma mai sallamawa da mai bin umarnin Ubangiji madaukaki (shi musulmi ne)[10], ya kasance tsarkakakke tun asalin halittarsa kuma ba ya daga cikin masu yi wa Allah shika, kuma Annabi Ibrahim (a.s) ya dora ‘ya’yansa[11] kan tafarkin tauhidi da musulunci kuma ya yi musu wasici da shi. Har ta kai ga cewa Ibrahim da Isma’il (a.s) sun kasance suna addu’a cewa Allah ya sanya su daga cikin musulmai kuma suka roki Allah ya fitar da al’umma musulma daga cikin zuriyyarsu.[12]
2 da 3.  Mai ikhlasi ma bin addini madaidaici
Abin da ake nufi da Ikhlasi shi ne tsarki da tsafta da tsarkaka daga rashin tsarki da mara sa tsarki[13]. Kuma abin da ya ke khalis (tsarkakakke) shi ne abin da ba shi da - kuma be gauraya da gurbataccen abu - mai jiki ko mara jiki ba. da wasu kalmomin ikhlasi na nufi bawa ya zama ya tsarkake nufin sa zuwa ga ubangijinsa.
A cikin Alkur'ani duk inda wata kalma ta (mukhlis) ko (mukhlisina) da kisirar (lam) ta zo to tana dauke da wannan ma’anar kuma a kan tsarkake niyya take magana, kuma tsarkake niyya shi ne kamar idan mutum ya ce na tsarkake addinin na ko ya ce Allah ya umarce ni da in yi ikhlasi cikin addini na.
Amma kalmar (muhklas) ko (mukhlasina) da fatahar (lam). Na farko: ta zo da ma’anar wasu bayi da aka siffanta da wannan difar. Na biyu: tana magana kan wasu bayain Allah kebantattu da nasa ne su, kamar yanda ya zo a kur’ani “bayin Allah” ko muka “bayin ka da ka tsarkake” kamar yadda aka siffata Annabi Musa[14] da Annabi Yusif[15] (a.s) a cikin Kur'ani da wannan siffar.
Kalmar “hanif” da “muslim” da “khalis” da “mukhlis” a ruwaya sun zo da ma’ana daya;[16]  don haka hanif na nufin hanya madaidaiciya mikakkiya dodar waccce ba wuce iyaka kuma ba gazawa, kuma “musilm” na nufin wanda ya mika wuya ya ji ya bi dukkanin umarni da hanin da suka zo daga Ubangiji , kuma ma’anar mukhlisi ita ce mutumin da ba wanda ya sa a gaba in ba Allah ba.[17]
Bisa la’akari da wannan tafsirin da ya gabata za mu iya ciro karin wata mahanga ko ma’auni kan tafsirin “hanif” da aka cire daga Kalmar “hanafa” tana nifin gujewa da nisanta daga bata da kuma karkata zuwa ga daidata wanda ke nufin kaucewa daga addinin bata zuwa na gaskiya, a Kur'ani an kira Annabi Ibrahim (a.s) da hanifi saboda kin yarda da ya yi ya zama mushriki da kuma fito na fito din da ya yi da addini shirka.[18]
4. kubutacciyar zuciya ta gari (mai kyau)
Daya daga cikin ma’aunin da Allah ke amfani da su wajen zabar bayi na gari shi ne zuciya ta gari[19] kuma an yabi Annabi Ibrahim (a.s) da wannan siffar kuma wannan ya sa Allah ya sanya shi daga cikin mabiya Annabi Nuhu (a.s). {hakika Annabi Ibrahim na daga cikin mabiyansa (Annabi Nuhu) a yayin da ya je wa ubangijinsa da zucuya ta gari}. [20] Tsarkakakkiyar zuciya kamar dai yanda ya zo a ruwayoyi yana nufin zuciya ta kasance mai kyau kuma ya zama ba wanda ke cikin zuciyar mutum sai Allah Ta’ala[21].
5. Godewa Allah
Godiya ita ce bayyana ni’ima a akidance da harshe kuma za a iya bayyana godiya ta hanyar aiki.[22] Misalin haka ya zo a cikin Kur'ani a yayin da ya siffanta Annabi nuhu da cewa shi bawa ne mai yawan godiya.[23] Imam bakir na cewa an kira Annabi nuhu da bawa mai yawan godiya saboda idan ya yi yammaci ya wayi gari ya kan ce: na wayi gari ina sheda wa da cewa duk abin da na yi yammaci da shi na daga ni’aima a cikin addinina da duniyata daga Allah ya ke shi kadai ba shi da abokin tarayya yabo da godiya mai yawa ta tabbata a gare shi a kan su (wadannan ni’imomin) baki daya. Daga nan sai Allah ya yi masa wahayi da cewa hakika ya kasance bawa mai yawan godiya”.[24]
6. Dakewa a cikin jarrabawa[25]
Allah yana so dan adam ya wanzu tsarkakakke bisa yadda aka halicce shi kuma ya ci gaba da bin hanyar samun kamala, amma ya zama ya wanzu kan dabi’ar sa ta halitta tsarkakakke. Allah ya san badinin ‘yan’Adam amma ya zama wajibi shi kansa dan adam din ya zama ya san kansa. Don haka ne ma ake jarraba shi don a banbance kuma a tantance tsakanin nagari da wanda ba nagari ba, don a sannan ne nagari zai fito sarari a gane shi. A sakamakon wannan jararrabawar ne ake tantance boyayyaun siffofin da mutum ke da su kamar; biyayya, sadaukantaka, kamewa da ilimi, cika alkawari da sauransu wadanda su ke bawa zahiri kima. Don haka jarrabawa na bayyana matsayin mutum ne a fagen aiki ba a wajen magana ba, kamar dai yadda ubangiji yake fadi a cikin al’Kur'ani mai girma: “shin mutane na tsammanin a kyale su don sun ce mun yi imani ba tare da an jarraba su ba”.[26] lalle abin da yake a sarari shi ne jarrabawa na bayyana matsayi da mabanbantan darajojin mutane, kuma jarrrabawa na haifar da canji a rayuwar mutane bisa gwargwadon martabar imaninsu, kuma jarrabawar annabawa ta fi tsanani da wahala fiye da ta kowa.
Allah na saukar da Jarrabawoyi da bala’o’i[27] ga zababbun bayinsa saboda ni’imar da ya yi musu, ko kuma a jarrabe su da damuwa ta rashin da su kuma suna ta fatan a basu har su tsufa kuma a kan jarrabce su da jurewa tuhumce-tuhumcen da guna-gunan mutane da tsegungumansu, da fille wa da kai da nisantar gari da dai sauransu...... manyan bayin Allah sun samu kansu cikin dukkanin wadannan jarrabawoyi kuma sun tsallake su ba tare da sun yi ko gezau ba kuma sun samu babban matsayi a wajen ubangiji.
7. kasantuwa tare da Allah  a ko wane lokaci
Daga cikin mutanen da Allah ya yaba a cikin Kur'ani wanda bayan haka sai ya bayyana karara cewa akwai, wandannan bayi ne zababbu na gari kuma masu yawan komawa gare mu “auwabina”  a wani wajen da lafazin “auwab” na mufaradi wanda Kalmar ke nufin mutumin da yake tsananin yawan komawa ga Allah a komai, Allah madaukaki ya fadi girman matsayin wasu bayi a cikin Kur'ani da ya kirasu da masu yawan komawa gare shi, a duk lokacin da wani abu mai girma mara kyau ya same su sai su koma zuwa gare shi, kamar irin su anabi Dawaud[28], da Sulaiman[29] da Ayyub[30] (a.s).
8. Tsage gaskiya
Gaskiya it ace kishiyar karya kuma abin da take nufi shi ne tsayawa kan gaskiya da kuma fadin gaskiya[31]. fadin gaskiya na da matsayi mai girma kuma sifface daga cikin siffofin masu girma ga dan’adam. Tun asali Allah Ta'ala na son ya ware masu gaskiya daga marasa gsakiya, sannan ya san masu gaskiya sannan ya yi musu sakayya bisa wannan siffar sannan Allah Ta'ala ya yabi wasu mutane da suke da wannan siffar kuma ya zabe su kan wani babban lamari kamar manzanci kuma saboda fadin gaskiyarsu ya kira su da masu gaskiya. Annabi Ibrahim babba misali ne mabayyani na wadannan bayin Allahn kuma shi abin koyi ne cikakke wanda yana daga cikin wadannan zababbu kuma masu gaskiya. {ku tuno da Annabi Ibrahim a cikin wannan littafin hakika ya kasance Annabi mai yawan gaskiya}.[32] wani misali na biyu na abin koyi kan gaskiya wanda shi ma ambatonsa ya gabata a Kur'ani shi ne Annabi Idris (a.s).[33]
 

[1] Surar shura aya 51
[2] Surar an’ami aya ta 124 da isra’I aya 55.
[3] Surar shura aya 19.
[4] Suarar kasasi aya ta 68.
[5]Surar nahali a ya ta 9.
[6] Taba’taba’I sayyid Muhammad  Husain , a cikin al’mizan fi tafsirin kur’an j 3 shafi 120, kum taftari intisharat islami, bugu na biyar 1417.
[7] Shehk saduk a cikin ma’anil akhbar, shafi 185, kum, tdaftri intisharat islami bugu na farko 1403.
[8] Surar bakara aya ta 130 da 131.
[9] Surar Ali Imran aya ta 67.
[10] Kummi, mashhadi, Muhammad  bin Muhammad  Ridha, tafsiri kanzil daka’ik wa bahrul gara’ib. j 3 shafi na 126. Tehran sazimani caf wa intisharat  wizaratu irshadi islami bugu na daya. Arusi huwaizi abdul Ali bin jumu’a tafsiru nurus sakalaini j 1 sh 352, kum, intisharat isma’iliyan, bugu na hudu 1415.
[11] Surar bakara aya 132.
[12] Surar bakara aya ta 128.
[13] A koma wa jigo: “tahsilu nabtu khalis” tambaya mai lamba 738.
[14] Surar Maryam aya 51.
[15] Sura yusif aya 24.
[16] Kulaini Muhammad  dan yakub kafi j2 sh 15, Tehran, darul kutubul islamiyya, bugu na hudu 1407.
[17] A koma wa sarwi, mazandarani, Muhammad  salihu bin Ahmad sharhin kafi (al-usul wa alraudha) j 8 sh 46 tehran maktabatul islamiyya bugu na daya 1382.
[18] A koma surar bakara aya ta 135, dan ahli aya ta 123.
[19] A koma jigo: “kalbus salim tambaya mai numba 14780.
[20] Surar safati aya 83 -84.
[21] Kummi Ali dan Ibrahim kummi j 2 sh 123 kum darul kitab bugu na uku 1404.
[22] A koma jigo mai suna “rah hai shikri guzari “ tambaya mai lamba 29982.
[23] Surar isra’I a koma za tafsirin suyudi, jalalud din a durrul Mansur fi tafsiril ma’asur j4 shafi 162, kum, kitab khone ayatul lahi mar’ashi annajafi 1404.
[24] Tafsirul kummi j 2 sh 14.
[25] Jigo mai take: “gardhu az imtihan ilahi” tambaya mai lamba 107; “falsafeh dard wa ranj dar zindagi auliya ilahi” tambaya mai lamba. 2056.
[26] Sura ankabut aya ta 2.
[27] “rah hai izmayishi insani dar didgahi Kur'an” tanabaya ta 4157.
[28] Surar saad aya 17.
[29] Surar saad aya 30.
[30] Surar saad aya 40.
[31] “jaye gahe sadakat wa rasti dar kur’an wa ruwayat” tamnaya ta 45934.
[32] Surar Maryam aya ta 41.
[33] Surar Maryam aya ta 56.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa