Please Wait
21642
Littattafan riwaya da na tarihi sun tabbatar cewa dan’adam wanda ke kan doron kasa bai kasance an same shi daga Habilu da Kabilu ba, shi dai an same shi daga dan Annabi Adam (amincin Allah ya tabbata a gare shi) na uku mai suna Shisu ko Hibatullah.
Amman auren ’ya’yan Annabi Adam akwai tunani biyu a wajen malaman musulunci mufakkirai, wadannan tunanukan sun dogara ne a kan dalilai na ayoyin Alkur’ani da ruwayoyi. Za mu ba da haske a kan tunanukan nan biyu:
- Dan’uwa ya auri ‘’yaruwarsa, hakan ya faru ne sanadiyyar rashin shar’anta haramcin ‘yan’uwa su auri junansu, har ya zamana wanzuwar jinsi na mutum ya dogara ne a kan yin hakan, saboda haka ba matsala a wannan auren.
- Auren sashen ‘ya’yan Annabi Adam (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ga sashe wannan korarra ne domin yadda lamarin yake shi ne, sun auri wasu mata ne na wani tsatson wadanda suke zauna a wani bangaren duniya. Bayan haka sai ‘ya’yansu suka zama ‘ya’yan baffani, sai aka halatta musu auren junansu. Wasu riwayoyi sun karfafa wannan fahimtar, saboda Adam (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ba shi ne mutum na farko da ya zauna a duniya ba, akwai wasu mutane sun riga shi zama a bankasa.[i]
Wannan fahimtar ta farko ta dace da zahirin wasu ayoyi na Alkur’ani mai girma.
[i]Amsa tambayoyin addini makirimush shiraziy sh. 453. Markazuddirasatul Islamiyya. Tambaya, ina so ku bayyana mini a takaice kissar auren Kabilu da Habilu yaya suke auri yar’uwansu mata
Littattafan riwaya har ma da na tarihi sun tabbatar cewa asalin mutum wanda ke doron kasa bai samu ta tsatson Habilu da Kabilu ba, shi dai wannan asali ya gangaro ne daga tsatso dan Annabi Adam na uku wato Shisu ko Hibatullah wanda shi ne wasiyyin Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ko a ce magajinsa. Hakika littattafai na riwaya har ma da na tarihi sun kawo cewar yayin da aka kashe Habilu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) Annabi Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zauna a cikin bakin ciki na shekara guda ba ya sakin fuska, sai aka zo masa aka ce masa. Allah (tsarki ya tabbata a gare shi) yana gaishe ka yana faranta maka rai. Sai suka ce a lokacin da shekarun Annabi Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) saka kai dari da talatin, wato bayan kashe Habilu da shekara biyar ke nan, matarsa Hauwa’u sai ta haifa masa Shisu (amincin Allah ya tabbata a gare shi), ma’anar Shisu shi ne kyautar Allah, abin nufi shi ne wanda ya maye gurbin Habilu, kuma ya kasance wasiyyin Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) kuma magajinsa.
Amma Kabila sai ya gudu daga garin da Adam yake a tsorace cikin firgici da razani, ba ya amincewa da duk wanda ya gani.
Bayan nan sai Iblis (Shaidan) ya ce masa, ai Habilu wuta yake bautawa, shi ya sa wutar ta cinye kurban (abin bauta, abin neman kusanci) to don haka kai ma ka gina gidan bautar wuta kai da ’ya’yanka za ka amfana. Saboda haka Kabilu ne ya fara assasa bautar wuta shi da ’ya’yansa, bayan haka kuma ’ya’yansa suka shagalta da busa sarewa, da kuntugi da wasa da goge da sauransu, suka narke a cikin shagala, shangiya, bautar wuta, zina da alfasha har ya zuwa lokacin da Allah ya yi fushi da su, ya dulmayar da su da ruwan Dufana lokacin Annabi Nuhu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) zuriyar Shisu ne kawai suka rayu.[1]
Amma labarin auren ’ya’yan Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana daga cikin abubuwa kullallu wanda an sami cin karo na riwayoyi a cikin littattafai na riwaya. Wasu malaman suna dogara da ayar farko ta suratunNisa’I,[2] suna cewar zuriyar Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Hauwa’u su ne suka wanzu a doron kasa ba tare da shigowar wani tsatso na uku ba. wannan maganar ta tabbatar da cewa ’ya’yan Adamu sun auri ’yan’uwansu mata, saboda da wasu matan suka aura ba ’yan’uwansu ba, da ayar Allah ba ta ce “daga su biyun ba”.
Wannan maudu’in ya zo a cikin sashin riwayoyi yayin da riwayoyin suka ba da haske a kan cewa auren ya kasance halas ne, saboda haramcin auren ’yar’uwa bai zo ba a lokacin abu ne a fili cewa wani abu ya kan zama halas saboda wata maslaha, ba ya nan kuma sai ya zama an haramta shi saboda wata maslaha.
Ya zo a cikin littafin ihtijaji na Allama Dabrisi, cewa Imam Zainul Abidina a wta tattaunawa da suke yi da wani Bakuraishe a inda Bakuraishen ya ce, bayan da Imam ya tabbatar masa cewa ’ya’yan Adam (amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun auri junansu, shin sun haihu? Imam Zainul Abidina (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ce, kwarai sun haihu,
Sai Bakuraishen ya ce, ai kuwa wannan aikin majusawa ne a yau, mai riwaya ya ce, sai Imam (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ce: “Tabbas majusawa sun aikata hakan bayan Allah ya haramta. Sai Imam ya ci gaba da cewa, “Kar ka kyamaci hakan, hukuncin Allah ya gudana shin Allah bai halicci matar Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) daga jikinsa ba (hakarkarinsa) sannan ya halatta masa ita ba? Wannan ai shari’a ce daga shari’ar da Allah ya saukar masa, sai daga baya Allah ya haramta hakan”.‑[3]
Wasu malaman sun fahimci cewa ’ya’yan Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ba su auri junansu ba (’yan’uwansu mata)[4] sai dai sun auri wasu ’ya’ya na wasu mutanen da suka kasance suna zaune a doron kasa (a wannan duniyar), tabbas wasu littattafai sun bayyana riwayoyin da suke ba da labarin cewa akwai wasu mutane mazauna wannan duniyar kafin saukuwar Annabi Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi).[5]
Kamar yadda wasu bayanai na ilimi suke yin nuni ga samuwar wasu al’umma miliyoyin shekaru kafin a halacci Annabi Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) saboda haka ya kamata mu amince cewar tun kafin Annabi Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) akwai wasu mutane, sun kusan shudewa, me zai hana zuriyar Adamu su auri matan wadannan mutane? Sai dai wannan fahimta ba ta dace da zahirin Alkur’ani ba, a bisa ka’idojin Usulul Fikihi duk lokacin da riwayoyi biyu suka ci karo da junansu, to dole ne a dora su a kan ma’auni na Alkur’ani, riwayar da ta dace da ayoyin Alkur’ani sai mu yi riko da ita.
Tabbatacciyar magana ita ce maganar farko, domin ta dace da zahirin Alkur’ani fiye da magana ta biyu, kamar yadda Allama Dabadaba’i (mai tafsirin Almizan) ya karfafa maganar farko tare da rinjayar da ita.[6]
Saboda karin bayani a koma wa Tafsirul Mizan j. 4. sh. 245. Tafsirul Burhan da Durrul Mansur da Kasasul Anbiya’u.[7]
[1] Mulisi, Biharul Anwar J. 11 sh. 220.
[2] Khalakakum min nafsin wahida, wa khalaka minha zaujaha wa bassa minhuma rijalan kasiyran wa nisa’a.
[3] Tarjamar Tafsirin Almizan J. 4 Sh. 236.
[4] Ilalushshara’iu an karbo daga Abi Abdullahi (amincin Allah ya tabbata a gare shi) an tambaye shi yaya tsatson Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) na zuriyarsa ya fara, domin wasu mutane sun ce, Allah ya yi wahayi ga Adamu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya aurar da ‘ya’yansa mata ga maza, duk asalin wannan halittar daga ‘yan’uwa ne maza da mata sai Abu Abdillah (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ce, subhanAllah Allah ya tsarkaka daga haka, duk wanda ya ce Allah ya sanya asalin zababben halittarsa da masoyansa, har ma da manzanni da muminai maza da mta daga haramun, kuma wai Allah ba zai iya sanar da su ta hanyar halal ba, bayan Allah ya riki alkawarinsu a kan halal da tsarki wAllahi batansa a fili yake.
[5] Tauheed sh. 277, J. 2 db Tehran: Sharh nahj Balaga na bn Misam j. 1 sh. 173 Alkisal, J 2. sh. 652. 14. Saboda karin bayani a komawa maudhu’in shekarun mutum a Alkur’ani da littafi mai tsarki, tambaya 516.
[6] Tafsirul amsal j. 3 sh. 249 – 244, Tafsirul Mizan j. 4 sh. 245 – 253.
[7] Ka komawa bangaren ba da amsa na ofishin sanarwar Musulunci tambaya yaya nau’in tsatson dan’adam ya ci gaba tare da cewa farkon halitta bai kasance b face mutane biyu `yan’uwan juna (habila da kabila).