Duk da kasancewar Zahara (a.s) ta bar wannan Duniyar a lokacin da take da Karancin Shekaru ne, ba ta yi tsawon Rayuwa ba, a Bangare daya ke nan, a Daya bangaren kuma Hadisan da aka karbo daga wajenta ba su da yawa, gashi ta yi shekaru goma na Yaranta, to, ta yaya za a iya suranta cewa ta kai irin wannan matsayin da irin wannan darajar?
A takaice dai mene ne ya taimaka mata, Alhali tana yarinya mai shekaru goma sha takwas, ta kai matsayin da yake dai dai da na Annabawa ne, wasu irin kamala take da su har ta cancanci wannan matsayin? Don Allah a bamu amsa mai gamsarwa.
Ba shakka cewa Kur’ani ya bayyana a Fili cewa Annabi Isa (a.s) an ba shi Matsayi mai Girma Alhali ma yana cikin Tsumman Goyo: ’sai Ta yi nuni a gare shi sai sukace ta yaya zamu yi Magana da wanda yake cikin Tsumma, sai ya ce ni Bawan Allah ne ya bani Littafi kuma ya sanyani Annabi kuma ya sanya ni mai Albarka a duk inda nake kuma ya yi mun wasiyya da Salla da Zakka matukar ina Raye” [1]
Haka ma a wani wuri a cikin Kur’ani zamu ga Fadar Allah Madaukaki inda ya ce: Kuma zai yi Magana da Mutane Alhali yana cikin Zanin Goyo da kuma Lokacin da yake Dattijo kuma zai zamo a cikin Salihai”[2]
Har ma Kur’ani ya yi Bayani balo balo a game da al’amarin Annabi yahaya (a.s) a inda Allah Azza wa Jalla ya ce: ya kai Yahaya ka riki Littafin nan da Karfi kuma mun ba shi Hukunci tun Yana Dan Yaro”[3]
Daga wadannnan Bayanan za a Fahimci cewa babu wani abin Mamaki game da samun Matsayi mai Daraja tun a Farkon Rayuwa, kai, tun A Ranakun farko ma, ko kuma a shekarun farko, kamar al ‘amarin Annabi yahaya (a.s), to, idan muka Tafiyar da wannan Ka’idar ga Shugaban Matan Halittu, wannan Maccen, Mutumiyar Allah zamu ga babu wani Rudewa ko Nisantarwa da zamu hadu da su game da samun da Sayyida Zahara ta yi ga Mukami mai daraja da daukaka, ta yanda a dalilin takawarta da tsantsenin ta samu matsayi irin na Annabawa, amma dai tabbas ita ba Annabiya ba ce, wannan matsayin babu wani mutum mai Adalci, mai girmama Kur’ani wanda ya yi imani da wajabcin jagorancin Kur’ani, da zai yi Shakkar samuwarsa gare ta.
Ta yanda Kur’ani ya fada a fili a cikin ayar tsarkakewa cewa nufi ne na Allah, na tsarin halittar samuwa, ya nufi tsarkake Ahlul Baiti (a.s) a cikin su kuma akwai Zahara (a.s) daga barin dukkan Datti da Dauda, wanda kuma ita ce Hususiyyar Annabawa, wacce da ita ce suka samu Makami, na Annabci suka zamo Gaskatawa ne ga Fadar Allah madaukaki: Allah shi ne ya san inda zai Sanya Sakonsa”[4] sannan kuma Allah Madaukaki ya fada a cikin Littafinsa mai gima: Iyaka kawai Allah yana nufin ya Tafiyar da Dauda ne ga barin ku Ahlul Baiti kuma ya Tsarkake ku Iyakacin Tsarkakewa”[5]
Kuma Dukkan Musulmi masu Tafsiri na dukkan Mazhabobi da Dariku sun yi Ijma’i a kan cewa wannan Aya ta Kunshi Sayyidah Zahara (a.s) to, shin akwai wani Matsayi da yake a saman wannan?
Amma game da Abubuwan da suke Sabbaba samun irin wannan Matsayin, Wasunsu daga Mutum ne shi kansa, wasu kuma daga Tarbiyya ne, wani abun kuma wanda shi yafi Muhimmanci shi ne Ludufin Allah.
To, amma babu lokacin kawo dukkan wadannan sharhohin a nan.
za a iya nemansu a mahallinsu.
Wasu binciken da suke da alaka da wannan bayanin:[6]
- Matsayin Imaman Shi’a idan an Kwatanta da Matsayin Annabawa 9198 (lambardandalin: 9188).
- Ma’anar Hadisin da ke cewa ba domin Fatima ba da …. 13495 (lambar dandalin: 13230).
- Bangarori na matsayin Fatimatuz Zahara (a.s), 2837 (lambar dandalin: 3348).
[1] Maryam 29-31
[2] Ali imran 46
[3] Maryam12
[4] An’am 124
[5] Ahzab 33