Please Wait
8088
Makamin matsayin ubangijintaka yana da matakai da marhaloli mabambanta, kuma don a samu wannan amsar dole ne a ga dukkan martabobi da ma’anonin baki daya. Idan abin da ake nufi da kai wa matakin ubangijintaka shi ne zatin mutum ta canja da sauyawar abin halitta ya koma mahalicci to wannan al’amari a fili yake cewa batacce ne kuma ba zai yiwu ba. Sai dai wannan maganar zata iya yiwuwa tana nuni da wata ruwaya ce da aka karbo daga imam Ja'afar Sadik (a.s) wacce yake fada cikinta cewa; “ibada jauhari ce, badininta ubangijintaka ce” ma’anar wannan maganar shi ne isuwa zuwa ga matukar bauta da narkewa cikin zatin Allah, ba ana nufin mutum ya koma ubangiji ba.
Makamin matsayin ubangijintaka yana da matakai da marhaloli mabambanta, kuma don a samu wannan amsar dole ne a ga dukkan martabobi da ma’anonin baki daya. Idan abin da ake nufi da kai wa matakin ubangijintaka shi ne zatin mutum ta canja da sauyawar abin halitta ya koma mahalicci to wannan al’amari a fili yake cewa batacce ne ba zai yiwu ba, kuma saken zuci ne kawai da ba shi da wani tushe, kamar yadda ya zo a kur’ani mai girma cewa Fir’auna ya yi da’awar ubangijintaka sai ya kama hanyar tabewa kamar yadda yake a fadinsa madaukaki: Sai ya ce ni ne ubangijinku mafi daukaka, sai Allah ya rike shi da azabar karshe (lahira) da ta farko[1] (duniya).
Sai dai abin da ake kawowa a bahasin irfani a babin tajallin siffofin Allah da makamancinsa wannan wata maganar ce daban da ta saba da waccan, kuma tana da alaka da ruwayar da aka karbo daga imam Sadik (a.s) cewa: “ibada jauhari ce, badininta ubangijintaka ce[2]” kuma shigen irin wannan maganar ta zo a kalaman masu irfani da suka yi bayanin sa dalla-dalla.
Wannan maganar a cikinta akwai nuni da mafi daukakar matsayi da martabobi da mutum yake kaiwa zuwa gare su, bayan ya narke cikin zatin Allah sai kuma ya wanzu ciki da wanzuwar Allah, kuma matsayin wanzuwa bayan narkewa ba yana nufin mutum zai canja ya koma zuwa Allah ubangiji ba, ko kuma ya kai ga matsayin ubangijintaka, sai dai abin da ake nufi da narkewa da sabewa (yin saba da fita) daga zatinsa shi ne mutum zai zama mahallin tajallin (bayyanar) siffofin Allah ne.
Saboda haka ba yadda mutum zai iya kaiwa zuwa ga matsayin ubangijintaka ta kowane hali, sai dai yana iya narkar da zatinsa sai ya bayyana da siffofin ubangiji da yake bayyanar da su ga wannan mutum da ya narke, kamar dai yadda arifai suke cewa “matukar samuwa ta wanzu (to shi ma zai wanzu)” ba zai yiwu ubangiji ya zama cikin bawa ba, da nufin cewa bawa yana nan dai bawa, ubanigiji kuma yana dai ubangiji, ba zai yiwu a hada su biyu ba.
Kuma an yi nuni da wannan matsayi a wasu ruwayoyin daga cikin akwai hadisin nan na kudsi shahararre da yake cewa: “Bawa ba ya gushewa yana kusanta zuwa gare hni da nafiloli da ibadoji har sai na so shi, idan na so shi sai in zama jin sa da yake ji da shi, da ganin sa da yake gani da shi, da hannunsa da yake riko da shi, da kafarsa da yake tafiya da ita” [3].
Kamar yadda komawa da karanta ruwayoyin da ziyarorin da kuma kalaman da suke zuwa daga ma’asumai da matsayinsu yana nuna mana wannan matsayi mai girma, sai dai ta wata fuskar kuma akwai wasu mutane masu gazawa ga fahimtar irin wannan kalamin wadanda suke ganin sa shisshigi ne a addini, sai dai mu zamu yi bayanin wannan ruwayar wani lokacin.
Daga irin wannan akwai maganar wasu arifai da ta zo don bayanin matakai da matsayoyi cikin bayani na falsafa da hikima, daga cikinsu akwai Mulla Sadra a littafinsa “Ikazun na’imin” (farkar da masu bacci) da ya yi bayanin tafiyar masu irfani zuwa ga Allah madaukaki, yayin da ya kai ga matsayin tauhidi sai yake cewa:
“An ce wannan tauhidin shi ne suturta fuskar bauta da fuskar ubangijintaka, da boye falakin zatinsa yayin samun ranar girma da daukaka, sai ubangiji ya kasance a zahiri bawa kuwa ya kasance a boye…, kuma zai iya yiwuwa a samu canja siffar mutum da siffar Allah ban da zati, don haka duk sa’adda wata siffa (ta bawa) ta dauke ta gushe sai wata siffar (ubangijintaka) ta maye gurbinta, sai gaskiya (ubangiji) ya kasance jinsa, da ganinsa, kamar dai yadda hadisi mashhuri ya yi bayani, sai mutum ya yi tasarrufi a cikin halittu da abin da Allah ya so” [4].
Haka nan ne Mulla Ali ya rubuta a game da wannan lamarin yana mai cewa:
A lokacin ne sai bawa ya zama kamar fainsa (s.a.w) cewa: Allah ya halicci Adam (a.s) a bisa surarsa, kuma matsayin surar abu shi ne matsayin fuska da inuwa daga hakikanin zatin abu da ma’abocin fuska da inuwa, kamar dai yadda imam Sadik (a.s) ya ce: Bauta Jauhari ce, badininta shi ne ubangijintaka. Da wannan ne ya yi nuni da matsayinsa a halarar ubangiji yayin da ya ce: duk wanda ya gan ni to ya ga hakku (ubangiji), kuma imam Sadik (a.s) yana fada game da fadin Allah madukaki: duk wani abu mai halaka ne sai fuskarsa. Cewa; mu ne fuskar. Da wannan ne zamu ga alkiblar masu irfani sarkin muminai imam Ali (a.s) yana cewa: sani na da haske, shi ne sanin Allah. Domin matsayin haskensa (a.s) daga halarar zatin Allah yake, wanda yake zati ne na hasken haskaka mai rinjaye kan komai, kuma shi ne matsayin surar abu kuma fuskarsa[5].
Hakika ma’abota irfani sun yi magana a baitocinsu da kalamansu game da wannan lamari, daga cikinsu akwai sayyid haidar amuli yayin da ya rubuta musamman game da matsayin wilaya ta musamman a irfani yana mai cewa: wilaya ta musamman ita ce narkewar bawa a cikin gaskiya, waliyyi shi ne wanda ya narke a cikin hakku (ubangiji) kuma ya wanzu da shi.
Ba ana nufin narkewa ita ce rasa bawa baki daya ba, sai dai abin da ake nufi da wannan shi ne fuskacin da yake bawa zata narke cikin fuskancin ubangijintaka, domin kowane bawa yana da fuskacinsa a halarar ubangiji da ita ce aka yi nuni da ita a fadinsa maduakaki “Kowa yana da fuskacinsa da yake jibintarta”, aya. Wannan kuwa ba ya samuwa sai dai cikakken fuskanta zuwa ga janibin fuskacin ubangiji sake babu wani kaidi da sharadi, don da wannan ne fuskancin hakirkarsa ta ubangijintaka zan ta karfafa sai ta yi rinjaye kan fuskacin halittarsa har sai ta rinjaye ta, ta narkar da ita baki daya, kamar dai wata kwayar gawayi ce da aka sanya ta cikin wuta.
A bisa haka ne mutum kamili ya kasance shi ne mai alamta siffofin Allah baki daya, kuma idan mutum ya kai kololuwar kamalar karshe to zai iya kasancewa halifan siffofin Allah a duniya, domin siffofin Allah suna bayyana ga mutum a martabar narkewa. Wannan kuwa ba yana nufin magana ne kan ubangijintakar mutum ba, wannan yana nuna bayyanar alamtuwar Allah ne a mutum, wannan kuwa ba yana nufin sun hade da Allah ba, ko kuma mutum ya canja ya koma ya sauya zuwa ga Allah ba, kamar yadda muka yi nuni da haka a baya.
[1] Annazi’at: 24, da 25.
[2] Misbahus shari’a, s 7, mu’assasar al’a’alami lil matbu’at, 1400 k.
[3] Awalil la’Ali, j 4, s 103, manshurati sayyidus shuhada, kum, 1405 k.
[4] Mulla Sadra, Ikazun na’imin, s 58, anjamane hikmat wa falsafeye iran.
[5] Nuri, almaula Ali, ta’alikat alal mafatihul gaib, s 742, muassasar tahkikate farhangi.