advanced Search
Dubawa
12248
Ranar Isar da Sako: 2006/05/17
Takaitacciyar Tambaya
Shin addini ya dace da siyasa?
SWALI
Shin addini ya dace da siyasa?
Amsa a Dunkule

Addini ya zo ne domin rabautar mutum har zuwa karshen duniya, don haka ba yadda zata yiwu ya kasance bas hi da wani mataki game da abin da al’ummar duniya take bukata daya hada da jagorancin hukuma. Ta wani bangaren kuma yanayin dokokin musulunci sun tilasata wajabcin samar da hukuma ta yadda idan babu hukuma ba zasu iya rayuwarsu ba.

Amsa Dalla-dalla

Kyakkyawan tunani gaaddini a bias mas’alar komawa zuwa ga addini a matsayin asalin doka ga siyasa wani abu ne bias dabi’a yake doruwa bias hankali. Addinin day a zo domin ya wanzu har zuwa karshen duniya da dukkan bukatun mutne ba yadda zai yiwu ya kasance ya yi shiru game da wasu abubuwan masu muhimmancin kamar siyasa da hukumar al’umma. Don haka ne zamu ga zamu ga imam Ridha (a.s)  ya yi Magana game da dalilin hukuma yana mai cewa: mu ba mu taba samun wata al’umma ba da ta rayu ba tare da jagora ba, da kuma zata samu ci gaban rayuwa, domin suna bukatar mai tafiyarwa a lamuran su na duniya da na lahira, kuma ba ya daga hikimar Allah madaukaki ya halicce mutane sannan ya bar su ba tare da ya sanya musu jagora ba, kuma da yake ya san cewa dole ne mutane ba makawa sai dai su zauan tare da jagora, wanda zai tsayar da lamurran su, kuma ya jagorance su don yaki da makiyansu, kuma ya raba musu dokiyoyin kasa, kuma ya tsayar da sallar juma’a da jam’I a cikinsu, kuma ya kare abin zalunta daga zaluncin azzalumi”[1].

Ta wani bangare kuwa nau’in yanayin tsarin hukucin musulunci ya kasance ne da babu makawa bisa tsrinsa a samu hukuma, kuma musulunci in babu hukuma to ba zai iya tafiyar da lamurransa ba, don haka ne zamu ga Imam ridha (a.s) ya yi nuni da tsayar da sallar jam’I da juma’a a cikin bayaninsa, a wata ruwayar yana mai cewa: “Idan da ubangiji bai sanya wa mutane jagora amintacce mai kiyayewa ba, kuma wanda ya kasance abin nutsuwa da shi, to addinin Allah zai kawu ne, kuma hukunci da shari’a zasu canja, bidi’a zata karu a cikin addini, marasa addini kuwa zasu sanya hannu kan addinin alla har sai ya samu tawaya da shubuhohi game da musulunci da yada ta a tsakanin musulmi” [2].

Don haka ne dole ne ga musulmi har ma da wadanda ba musulmi ba sananne ne cewa musulunci yana da tsari na musamman na hukuma da irin hukumar da Annabi (s.a.w) ya yi a madina ta zama misali ne ga wannan hukumar, kuma babu wani mai kokwanto a kan haka,ta yadda yayin da “Ali abdurrazak” a shekara 1343 h>k, a kasar Misira ya yi musun samun hukumar musulunci a littafin “Musulunci da Asalin Hukunci[3]” yayi da’awar cewa ko da sau daya Manzon Allah (s.a.w) bai yi da’awar kafa hukumar musulunci ba[4], sai malaman sunna na duniya suka kafirta shi. Wannan kuwa ya yi shi ne yayin da Kamal Atatuk ya kafa hukumar da babu ruwanta da addini a Turkiyya ne bayan ya musanta Daular Usmaniyya,  su kuma masu goyon bayan Daula a Misira suka sanya sarki Fu’ad a matsayin halifan musulmi ne ya yi wannan rubutu. Domin ya yin nuna ya tasirantu da tunanin rashin addini  a hukuma tunanin yammacin duniya, kuma ya rubuta ne da daukar tunanin malaman faslasar siyasar turai.

A bisa gaskiya shi wannan Ali abdurrzak ya yi wannan da’awar abubuwa biyu ne a maganar da da suka hada da maganar cewa Manzon Allah abin da ya kafa a Madina ba hukuma ba ce, kuma kai wannan abin da ya faru a addini ba ma addini ba ne ke nan.

A maganar farko yana cewa abin da Manzon rahama ya kafa a madina bai yi kama da abin da ake cewa da shi hukumar addini ba a yau. Amma magana ta biyu yana cewa sha’anin annabta ba shi da wata alaka da shugabanci.

A bisa amsar farko dole ne ya gane cewa idan yana ganin abin da ya faru a madina ba hukuma ba ce, to dole ne mu san cewa ash eke nan babu wata hukuma da aka taba yi a cikin al’ummun duniya, don haka dole ne ya kawo wani bayani gamamme game da ma’anar hukuma domin mu ga mene ne wannan hukumar da Annabi ya kafa shin ana kiranta hukuma ko kuwa.

Muna iya cewa hukuma ita ce riko da iko domin tafiyar da lamurran al’umma. Wannan kuwa ya hada duk wani irin salon jagoranci wanda ya hada da sanya dokoki da zartar da hukunci da gudanarwa[5]. Ta wani bangaren kuwa muna iya cewa kalmomin iko, suna nuna hukuma[6], da karfin hukunci[7], a bisa wani tsarin tafiyar da rayuwar al’umma[8].

Don haka muna iya cewa abin da Manzon Allah (s.a.w) ya kafa a madina shi ne hukuma da ma’anarta cikakkiya, domin ya yi riko da ikon tafiyar da lamuran al’umma. Kuma an rubuta littattafai masu yawa game da lamarin hukumar Annabi (s.a.w)[9]!.

Amma batun cewa hukumar addini ce Manzon Allah sa ya kafa wannan muna iya nuna shi ta cikin wasu dalilai kamar haka:

1- Hukuncin musulunci da ya kasance in babu hukuma ba zai yiwu a gudanar da su ba kamar kotu da zartar da hukunci, da tsarin dukiya a musulunci da aka gudanar da wannan hukumar.

2- Dalilai masu yawa da suka zo a shari’a suna masu bayanin matsayin Manzon Allah (s.a.w) a matsayin jagoran al’ummar wannan hukumar[10].

3- Idan kuwa annabci da manzanci sun yi hannun riga ne da hukuma to yaya muka ga mai tsira da aminci ya kafa hukuma ya kuma kashe lokutansa wurin ganin ya samar da ita? Shin a nan an samu gafala ne daga asalin aikin sakon manzanci ko kuwa? Idan kuwa aka ce Manzon Allah (s.a.w) ya yi amfani da wannan tsarin na kafa hukuma ne wurin isar da sakon Allah, to wannan yana nuna karfin alaka tsakanin hukuma da sakon addini, kuma wannan yana amsa mana tambayar cewa shi ne dalilin da ya sanya bai ba wnai daga mataimakansa ba kamar Imam Ali (a.s) domin shi ya yi hukuma shi kuma ya ci gaba da isar da sakon Allah.

A kowane hali dai Ali abdurrazak ya kawo wannan lamarin kusan shekaru 70 da suka gabata ne kuma tun wannan lokacin ne aka samu wannan tunani yana yawo cikin al’ummar musulmi da yanayi daban-daban, kuma wannan muna iya kawar da shi idan muka koma asalin tushen da wannan tunanin ya samo asali muka koma yammancin duniya muka ga asasin wannan tunani muka mu ba shi amsa, wanda tunani ne da yake komawa cikin koyarwar addinin kiristanci da ya rayu a yammancin duniya[11].

Karin bayani sosai:

1. Mahdi Hadawi tehrani, wilaya wa diyanat, cibiyar al'adu ta Khaniye Khirad, Kum, bugu na biyu, 1380.

 

 


[1] Majlisi: biharul anwar; j 6, shafi; 60.

[2]  Abin day a gabata.

[3] Islam ba rishehaye hukumat.

[4] Ali abdurrazak, al’islam ba usulul hokum, shafi; 80.

[5] Gobernment.

[6] Sobereignty.

[7] Authority.

[8] Structure.

[9] Jehshiyar (wafati: 331 h). alwuzara wal kuttab.

[10] Adilleye wilayate ma’asumin: su’al 218.

[11] Din ba masihiyyat, su’al 212.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa