advanced Search
Dubawa
22806
Ranar Isar da Sako: 2006/05/31
Takaitacciyar Tambaya
Me ake nufi da gaskiya, kuma wace hanya ce zata kai ga samun hakikanin gaskiya?
SWALI
Me ake nufi da gaskiya, kuma wace hanya ce zata kai ga samun hakikanin gaskiya?
Amsa a Dunkule

Gaskiya tana nufin hanya matsakaiciya, wato ana nufin maganar daidai da bin hakika, gaskiya ita ce sanya komai da hikima bisa mahallinsa da ya dace da shi.

Sannan bin gaskiya da tafiya kanta bisa tafarkinta a fagen tunani yana nufin tanadin makamin ilmi da mantik da yin ado da tufafin yakini da nisantar duk wata yin 'yar rufe a magana da camfi, da nisantar biyayyar mutane maimakon bin gaskiya, da fadin daidai.

Amma a matsayin aiki gaskiya tana nufin bincike da yi wa kai hisabi, da yin bauta, da kaskantar da kai ga Allah, da jin tsoronsa madaukaki, da tuna mutuwa da tsoron lahira, da shiga tafarkin gaskiya, kuma yana daga abin da aka sallama ne cewa wanda duk gaskiya ta bayyana gare shi, to hakika ya gane ta ne kuma ya san masu gaskiya ne. Imam Ali (a.s) yana cewa: "Ka san gaskiya zaka san masu ita".

Amsa Dalla-dalla

Da farko dole ne mu tsaya don sanin ma'anar gaskiya domin mu samu damar zuwa ga marhala ta biyu ta yin ado da tufafin gaskiya domin mu kasance daga ahalinta. Magana ta zo daga imamai ma'asumai na shiriya (a.s) cewa: "hakika gaskiya tana da daci, karya kuwa sako sako take[1]. A wata ruwayar suna cewa: ka fadi gaskiya ko da tana da daci[2].

Ima Sajjad (a.s) yana yi wa dansa Imam Bakir (a.s) wasiyya da cewa: ka yi hakuri kan gaskiya ko da tana da daci (komai dacinta)[3].

Da wannan ne a dunkule zamu iya sanin cewa biyayyar gaskiya tana da wahala, sai dai akwai kamalar mutum a cikinta da daukakarsa, kuam bin karya yana da sauki da zaki, sai dai yana kai mutum zuwa ga wuta da lalacewa ne. Ya jefa shi cikin halaka, kuma muna iya bayar da misali don karin fahimta da misali mai sauki cewa: hanyar gaskiya kawai matafiya ce ta cikin duwatsu masu tsauri da hawa da sauka, yana da wahala ga jikin mutum matuka, sai dai yana da sakamako mai dadi, kuma karshensa mai zaki ne da rai zata ji dadi da shi, ta samu nutsuwa zuwa gare shi.

(alhakku) Gaskiya a lugga:

(alhakku da larabci) A lugga tana da ma'anar gaskiya kuma tana zuwa da ma'anoni daban daban, tana zuwa da ma'anar abin da yake yankakke bisa yakini wanda babu kokwanto cikinsa, da kuma abin da ba za a iya inkarin sa ba, da ma'anar daidaito da yakini.

(alhakika da larabci) Hakika kuwa tana zuwa da ma'anar gaskiya, ko hakki, ko tabbatarwa, kamar yadda ake cewa wane yana da tabbatarwa a cikin maganarsa mai karfi mai kwari shiryayya[4], kamar yadda ake amfani da ita da ma'anar Kalmar tsakiya, kamar tsakiyar hanya wato tafiya a tsakiyarta, muhakkik yana nufin mai tabbatarwa a zance da gaskiyar ra'ayi, alhaakku kuwa yana nufin tsakiyar abu[5].

Haka nan ya zo a littafin furukul lugawiyya cewa: alhakku shi ne sanya abu mahallin hikima, kuma ba ya kasancewa sai mai kyau ne[6].

Idan muka lura da wadannan ruwayoyi masu daraja muka kai ga natijar da suke bayarwa zamu fahimci cewa gaskiya tana nufin tsakiyar hanyar shiriya da ba ta karkata zuwa ga wani bangare ba, kuma tana da ma'anar sanya komai a mahallinsa da ya dace na gaskiya. Kamar yadda Imam Ali (a.s) yake cewa: asasin hikima shi ne lizimtar gaskiya[7].

Haka nan ya ce: asasin hikima shi ne lizimtar gaskiya da bin wanda ya dace (mai cancanta) [8].

Haka nan Imam Ali (a.s) ya yi nuni da wannan tafarki na ilimi a maganarsa wacce ya kamata kowa ya dogara da ita don kai wa zuwa ga hakikanin gaskiyar lamurra, kuma bai dace ba mutum ya dogara da abin da ya shahara ya yadu kowa ya san shi wurin sanin gaskiya bisa dogaro da maganar mutane ko kimar su,  domin gaskiya tana iya yiwuwa mutane su yarda da ita ko su ki ta, kuma daga cikin wannan irin kalamai masu daraja muna iya duba wasiyyar nan ta Imam Kazim (a.s) ga Hisham yayin da ya ce masa: ya kai Hisham, da akwai kwakwa a hannunka sai mutane suka ce daimon ne, da wannan bai amfane ka ba, alhalin ka san cewa kwakwa ce. Haka nan da akwai daimon a hannunka sai mutane suka ce kwakwa ce da wannan bai cutar da kai ba, domin kai ka san cewa daimon ne[9].

Ubangiji madaukaki yana fada a littafinsa madaukaki cewa: a wannan rana ma'auni shi ne gaskiya, duk wanda ma'auninsa ya yi nauyi to wadannan su ne masu rabauta[10].

Don haka ne idan rayuka suka ka kasance sun doru kan ayyukan gaskiya to zasu yi nauyin ranar alkiyama, amam idan suka rasa gaskiya to zasu yi sako sako rana kiyama, amma wadanda suka samu yin nauyi,n to karshen su shi en rabauta da dawwama ranar kiyama, amam wadanda ma'auninsa ya yi shafal shafal to wadannan su ne za a azabtar.

Don haka ne dole ne mutum ya shirya wa kansa ya dawo da ita zuwa ga alheri, ya yi mata tanadin alheri da gyara, kuma ya duba ya ga shin aikinsa yana kan hanya ko kuwa? Kan gaskiya ne ko kuwa? Kuma ya fara da gaskiya ne ko kuwa?

Kamar yadda shugaban wasiyyai Imam Ali (a.s) ya fada ne cewa: ku yi wa kawukan ku hisabi kafin a yi muku hisabi[11]. Shin kun sayar ne ko kun saya, kun samu riba ne a wannan cinikin ko kuwa kun samu faduwa ne?.

Haka nan ya fada yana mai bambancewa tsakaninsa da amru dan aas cewa: abin mamaki ga dan nabiga, yana raya cewa mutanen Sham suan cewa ina da raha, hakika ya fadi karya kuma ya yi magana da zunubi… amma wallahi ba abin da yake hana ni yin wasa sai tuna mutuwa, kuma ba abin da yake hana shi fadin gaskiya sai mance lahira[12].

Sakamakon bincike: hakika bin gaskiya da saurarawa gare ta a fagen tunani yana nufin yin shiri da makamin hankali da yin ado da kayan yakini, da nisantar duk wani yin jirwaye da sake saken tunani, da nisantar bin mutane sai dai bisa asasin don suna kan gaskiya da fadin gaskiya. Amma a fagen aiki, to ya kamata ne a yi wa rai hisabi, da yin bauta da rusuna wa Allah da jin tsoron sa maduakaki, da tuna mutuwa da tsoron ranar lahira, da shiga tafarkin gaskiya da bin hanyar daidaito, kuam yana daga abin da yake sananne cewa da gaskiya ta bayyana ga mutum to zai san mutanenta. Imam Ali (a.s) yana cewa: ka san gaskiya zaka san mutanenta (masu ita) [13].

Domin samun karin bayani:

1- Jawadi amuli Abdullah, hikmati nazari wa amali dar nahjul balaga (hikimar aiki da ta zazari a nahajul balaga) darasi na bakwai.

2- husaini terhrani Muhammad Husain: nur malakuti kur'an, mujalladi na farko, bahasi na uku.

3- jawadi amuli Abdullah, hayati arifaneyye Imam Ali (a.s) (rayuwar Imam Ali (a.s) ta irfani) fasalai na biyar.

4- nahajul balaga, huduba: 214 – 141- 216 – 220 – 9 – 157 – 201 – 91.

5- nahajul balaga, bangaren wasiku: 15 – 17 – 79 – 53.

 


[1]  Imam Ali (a.s) nahjul balaga, hikima: 376.

[2]  Almajlsi, muhamad Bakir: biharul anwar; 2 / 157 / 74.

[3]  Abin da ya gabata, 52 / 174 / 70.

[4]  Bandar rigi Muhammad, tarjameye farhange munjid attullab.

[5]  Sabah ahmad, farhange jami'.

[6]  Al'Askari abul hilal, alfurukul lugawiyya.

[7]  Al'amudi abdulwahid, gurarul hikam.

[8]  Abin da ya gabata.

[9]  Alharrani alhasan, tuhaful ukul, almaktabatul islamiyya, s 406, didiba'I Muhammad Husain, Ali wa falsafeye ilahi, s 33.

[10]  Surar a'araf: aya 7.

[11]  Nahajul balaga, huduba : 90.

[12]  Abin da ya gabata: huduba 84, jawadi amuli Abdullah, hikmate nazari wa amali dar nahjul balga, s 109 da 144.

[13]  Dabarasi, fadhl bn Hasan: majma'ul bayan: 1 / 211.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa