Please Wait
19069
Daya daga cikin ni'imomin ubangiji a ranar lahira ga wadanda suka yi imani da kyakyawan aiki shi ne sakamako da aljanna da ni'imomin ta. Ba bambanci wuri shiga aljanna tsakanin mace da namiji daga cikin ladar da sakamakon da ubangiji zai ba ‘yan aljanna akwai {hurul'in} wanda Kur’ani da ruwayoyi su kai nuni da hakan.
Ga cewar mafiya yawan masu tafsirai shi ne, aure a aljanna ya sha bamban da na duniya. Auren hurul'in na nufin kyauta daga Allah wanda zai ma bayin sa.
In muka lura da Kalmar huru da ain ya hada mace da namiji ne wato kalmace mai fadin da ma'ana so sai ma'anar ta shi ne dukkan ma auratan aljanna, mata muminai za a ba maza masu imani, haka maza muminai za a ba mata masu imani[i].
Wata ni'imar ubangiji ga ‘yan aljanna akwai yara kyawawa masu yi ma su hidima, a nan ma ba bambanci tsakanin mace da mamiji.
Daya daga cikin manyan ni'imomin da Allah madaukaki zaiba bayinsa masu tagawa da imani a ranar kiyamashi ne aljanna da ni'imomin ta masu yawa kuma tabbatattu. Sai dai yarda Allah tafi kowace kyauta daraja. Abin da zai sa mutum shiga aljanna shi ne imani da kyakyawan aiki awannan duniya duk lokacin da imani mutum ya karu kuma kyawawan aiyukan shi sukai yawa, matsayinsa a aljanna zai daukaka sannan ba bambanci tsakanin mace da namiji kowa ne zai iya kai wannan matsayin. Allah madaukaki na cewa; {dukkan wanda ya aikata kyawawan aiki mace ce ko namiji kuma ya yi imani tabbas za su shiga aljanna ba tare da hisabi ba kuma za a azurta su} [1].
Dokokin da hukunce hukuncen da ke kiyama da wadanda ke wannan duniyar ba zata yiyu a hada ba, saboda haka a cikin ayoyi ko ruwayoyi in ana maganar ci da sha da kuma mata kyawawa da gefen koramu da kar kashin itatuwa, saboda kwakwalen mu su fahimci dadin da ke aljanna ka dai amma dadin da ke cikin aljanna ba zata yiyu a hada su da na duniya ba. [2]
Ta hanyar ayoyi da ruwawoyi za mu amfana da cewa dukkan abin da ‘yan aljanna su ka bukata za a ba su[3]. Za mu iya nuni cewa daga cikin ni'imomin aljanna akwai hurul'in.
Wurare da dama a cikin ayoyin Kur’ani mai girma ana kiran ma auratan aljanna da hurul'in. [4]
Rur jam'ine na hura'a ma'anar sa shi ne macen da farin idanun ta sukai yawa kuma bakin sa ya yi baki so sai ko kuma da ma'anar matar da ke da bakaken idanu kamar na barewa, ain jam'ine na Kalmar {aina} da ma'anar manyan idanu.
A cikin Kur’ani hurul'in. an suranta su da kamar lu'u lu'u[5]. abayyane ya ke cewa hurul'in wasu halitune ba kamar matayain duniya ba[6]. Allah madaukaki na cewa: {za mu aura masu hurul'in[7]} ayoyi da yawa suna[8]. nuni da a bokan zaman mutum a aljanna: {mala'iku kyawawa da sigar mace da namiji matashi masu cikakken kyau}.
Ga cewar mafiya yawan masu tafsirai shi ne, aure a aljanna ya sha bamban da na duniya. Auren hurul'in na nufin kyauta daga Allah wanda zai ma bayin sa. [9]
In muka lura da Kalmar huru da ain ya hada mace da namiji ne wato kalmace mai fadin da ma'ana so sai ma'anar ta shi ne dukkan ma auratan aljanna, mata muminai za a ba maza masu imani, haka maza muminai za a ba mata masu imani[10].
Daga karshe abin lura a nan shi ne ‘yan aljanna suna da masu yima su hidima wadanda yara ne kyawawa su ne masu yima ‘yan aljanna hidima, yara ne maza kyawawa duk lokacin da ka dube su tsakayi zaton lu'u lu'u ne da aka kewaye da abubuwa, masu kyau[11]. An suffanta su da lu'ulu'u[12] kewayyaye[13].
A bayyane ya ke cewa wannan ayar na tabbatar da samuwar yara kyawawa wanda an yi su ne kawai domin hidima ga ‘yan aljanna.
Sakamakon karshe na wannan tattaunawa shi ne: dukkanin ni'imomin aljanna Allah ya tana dai su ne ga mazaje da mataye masu imani da kyawawan aiki, {hurul'in} a matsayin abokan zama na gari da kuma {yara} masu kyawan fuska a matsayin masu hidima ga ‘yan aljanna ka dai.
Karin bayani: tambaya ta 848.
[1] Gafir, 40.
[2] Askandri, Husain, ayoyin rayuwa, jildi na 5,shafi na 302.
[3] Fusilat,31.
[4] Dukhan,54; tur,22,waki'a,22 da 23.
[5] Waki'a aya ta 23-24 mizan jildi na 18, shafi na 228.
[6] Tafsir Almizan: j 18; s 228.
[7] Dukhan, 54.
[8] Safat,47; rahaman,58, rahman 70-72.
[9] Biharul anwar, jildi na 8 shafi na 99; tarjamar almizan, jildi na 18 shafi na 228.
[10] Didar yar{kiyama cikin kalam da wahayi9}, tafsir mizan.
[11] Insan: 19.
[12] Tur: 24.
[13] Insan: 19.