An fara Shafin nan na islam kuest a shekarar annabi mai daraja (s.a.w) a ranar aiko ma’aiki mai tsira da aminci da harsuna uku kawai (farisanci, larabci, ingilishi).
Hadafin wannan shafin na islam kuest shi ne amsa dukkan mas’alolin musulunci ta hanyar sakon yanar gizo.
An fara shi da himmar wasu daga cikin samari da matasa masu tunani da riko da addini a kasar musulunci ta Iran.
A yau wannan shafin na islam kuest yana da yare goma sha hudu ne da sama da tambayoyi da amsoshi dubu daya, wannan kuwa duk da himmar gomomin marubuta da matarajama yarurruka da dubunnan mutane suke amfana daga gare su kowace rana, kuma ya zama wani wuri ne da ake koma masa a yau domin sanin amsoshi a fagen ilimomin musulunci, ga kuma tsarin shafi wanda yake da yiwuwar amfani da shi ta hanyoyi masu yawa ga masu dubawa da masu amsawa bisa kokarin da kwararru masu imani suke yi dare da rana, kuma su sanya shi don amfanin masu bukata.
Cibiyar Rawaki Hikmat tana shirye yanzu ta sanya duk wannan ilimin mai kima da daraja a kyauta a hannun duk wata cibiyar amsa tambayoyi a shafin yanar gizo.
Muna fatan mu iya kasancewa wakilai na musamman gare ku a shafin yanar gizo don sanar da ku wannan mazhabi mai haske na Ahlul-baiti (a.s), kuma mu ba ku amsoshin dukkan tambayoyi masu yawan gaske da muke fuskanta cikin sauri da zurfafawa.
Mahdi Hadawi Tehrani