Please Wait
11838
A game da zamowar Allah yana warkar da marasa lafiya na kiristoci kuma yana lura da su, wanna yana samuwa ne a dalilin kwararowar ni’imarsa ta gaba daya, da tausayinsa, wanda ya shafi dukkan mutane, don su samu damar zabar hanyar sa’ada, da Imani, da isa ga kamala. da samun ilimin Allah a karkashin inuwar amfanuwa da ni’imomin Allah.
A dalilin hakan ne Allah ya halicci mutane ne a cikin ‘yanci, kuma ya ba su damar yin zabi, don ya jarraba su, kuma don irin zabinsu, ya bayyana a fili, don a tantance mumini, da mai tsarkin niyya daga barin waninsa.
Kari akan haka kuma shi ne cewa, wasu kiristocin suna da jahilci mai zurfi game da addinin musulunci, a bangaren ilimi ma suna da rauni, har ga matsayin da zai yiwu, mu ce zasu samu tsira, matukar sun kiya ye dokokin girmama dan Adam. Kuma ku sani su kiristoci ba wai dukkansu ne suke zaune a kasashen Europe ba, a’a, zaka samu kiristoci masu yawa, wadanda suke rayuwa a garuruwan takalakawa, a cikin kauyuka da fako, a cikin kasashen afurka, da Asiya matalauta, wadanda kuma suke fama da yaduwar cututtuka da talauci, kai har ma su kasashen da suka ci gaba din, zaka samu cewa kiristoci ba su tsira ba, daga cututtuka masu barna irin su kanjamau, da mashassharar tsuntsaye, da sauransu.
Za a iya yin tsokaci da nazari game da mahallin da wannan tambaya ta zo da shi a cikin kaso biyu.
ALIF: Gamewar kwararowa da baiwa ta Allah.
Hakika kyaututtuka da baiwa masu yawa na Allah, subhanahu wa Ta’ala, cikakku ne kuma kammalallu ne, idan aka yi la’akari da fitowarsu daga fagen kibriya’un Allah, ba su bukatan wani linzami ko sharadi, kuma Allahu subahanahu, ya sanar da kowa ta hanyar falarsa da yalwar samuwarsa, dukkan mutane daidai wadaida suke, a wanan bangaren, idan kuma har aka samu sabani a wajen wadan nan kyaututtuka da baiwar, to wannan saboda yanayin cancantarsu ga karban ne. Wannan yana nufin wasu mutane a cikin fagen shari’a, kuma a saboda rashin samuwar sharuddan da suka wajaba da shimfidar da ta dace, baza su iya tarban wadan nan ni’imomin, da soyayyar Allah, wadanda suke kwararowa ba. Kamar misalin, matanen da suka isa wani babban matsayi na kekashewar zuciya da bata, ta yanda ba zai yiwu su iya karbar shiriya, da ruhin imani, da jazba ta Allah ba.
Domin yanayin ludufi da sha’anonin rububiyar Allah shi ne cewa ya tsara ni’imomin ne ga ‘yan Adam, don su iya amfanuwa dasu ta bangaren addinin Allah.
wanda su ne zasu dabe su da kansu, don shi mutum a bisa dacewa da asalin halitta da fidirar da Allah ya kage su a kai, an tilasta su da su nemi zubowar ni’imomin Allah, masu jiki da na ma’ana, wadanda Allah ya sanya su a kusa da hanunsu, don su yi amfani da su wajen sauke nauyin aiyukan da ke kansu, na addini. don su zamo a cikin masu imani da tsoran Allah, kuma don su isa ga sa’ada da nasara.
Alhali kuma za mu ga wasu mutane, ba su amfanuwa daga wadan nan ni’imomin sai dai don amfanin duniyarsu, suna manta lahirarsu, ba su yin wani tunani, sai na yanda zasu isa ga burace buracensu, masu dogon zango, da masu fadin gaske na duniya, [1] kadai.
kuma kamar yadda Allah yake labartawa ne akansu da cewar:
”wanda ya zamo yana son mai gaggawa ce sai mugaggauta masa a cikinta da abin da muke so ga wanda muke so sai musa sanya masa wutar jahannama zai shige ta yana abin zargi? Wanda kuma ya so lahira kuma ya yi aikinta alhali yana mumini, to su wadanan aikinsu ya kasance abin godewa. Ko wadansu…?”[2]
A saboda haka shi Allah (subhanawu wataala) a dalilin gamammiyar rahamarsa yana sanya ni’imomin sa, masu jiki da na ma’ana, a karkashin zabin bayinsa masu yawa, kuma da yawa ya kan bayyana mu’ujujizin da hujojin sa a gaban bayinsa da suka fi sabonsa don su fuskanci Allah (subhanahu). Kamar yanda a bisa dacewa da wasu ayoyin Kur’ani, za mu ga ‘yan Adam a wasu lokuta su kan koma ga Allah, a cikin wasu lokuta na rayuwansu, don neman biyan bukatarsu, da warware mushkilolinsu, shi kuma Allah yakan fuskance su da idon rahma. To a wanan bankaren babu wani banabnci tsakanin mutane. sai dai muhimmin abu kawai shi ne yadda dan Adam zai ci gaba da godewa wadanan ni’imomin a daukacin rayuwarsa. ” ka ce waye yake tserar taku daga duhun nan kasa da teku kuna kiransa cikin kankantar da kai da rage murya mun rantse idan ka tserar da mu daga wanan mun rantse tabbas za mu zamo cikin masu godiya. Ka ce Allah ne zai tserar da ku daga gare ta, da dukkan bakin ciki sanan kuma ku ne kuke hada wani da shi[3].
Ashe ke nan abin da aka tambaya a cikin wanan tambayar, na zamowar cewa Allah yana warkar da marasa lafiya na kiristoci, kuma Allah yana kyautata musu, hakan baya faru ne a sabo da su kiristoci ba ne ba, sai dai don gamammiyar watsowar rahamarsa ce da alheransa, wacce take shafar dukkan mutum, don su samu damar zaben hanya mai kyau ta jin dadi, da imani, da isa ga kamala, da samun ilimin Allah, cikin inuwar amfanuwa da ni’imomin Allah. Hakan ya zo ne, saboda Allah ya halici mutane ne a cikin yanci, ya kuma ba su damar yin zabe don ya jarrabasu, don Yanayin aikinsu da zabinsu gare shi, su bayyana, don a tantace mumini, da mai tsarkin niyya daga waninsa.
BA: wasu kiristoci jahilai ne masu zurfin jahilci, [4] duk da cewa addinin musulunci shi ne addinin gaskiya kuma sassaukar shari’a wanda lafiyayyen hankali yana karbar sa, kuma yanayin na’am da shi, kuma hakika Allah (subhanahu) ya saukaka hanyar isa ga hakikarsa kuma ya sanya shi mai yiwuwar fahimta, duk da hakan, muna ganin yana kyautatawa a cikin rayuwa ga wadanda ba su san hakikarsa ba, don zurfin jahilcin su, da zamowar su masu rauni a tunani, to, abu ne a fili cewa Allah zai lullubesu gamammiyar ludufinsa da tausayinsa, domin rashin gaskatawar su da musulunci ba domin sakaci da ganganci ne ba. Idan suka zamo masu kiyaye hakkin dan Adam, to, Allah madaukakin sarki, ba zai azabtar da su da azabar wutar jahannama ba, domin ita azaba don kafirai ne, masu zunubi, masu sakaci a cikin kafirci da zunubin su,.
Wan nan yana nufin cewa sun kafircewa addinin musulunci, to, amma wanda sakon musulunci bai isa gareshi ba, ko kuma ilimomin da suka isa gareshi dan kadan ne, yanda baza ta iya zamo masa hujja ba, don karbar wannan addinin, wadanan suma ana daukan su a matsayin wadanda ba su da sakacin jahilci, kuma suma suna daga cikin masu tsira, wadanda zasu shiga aljannah, indai sun kiyaye hakokin dan Adam.
Duk da wanan bamu dauka cewa duk labarin da ya zo a cikin wanan tambaya gaba dayan sa ingantance ne dari bisa dari, domin kiristoci ba wai a turai ne kadai ba.
Ana samun kiristoci masu yawa suna rayuwa a matalautan kasashe, da cikin kauyuka, da kungurumin bakin daji, a kasashen Africa da asiya, matalauta wadanda cututtuka suka da talauci suka yadu a cikinsu.
Kai, hatta ma a kasashen da suka ci gaba, zaka ga kiristoci ba su tsira daga cututtuka masu barna ba, irin su kanjamau da mashassharar tsuntsaye da dss.
Kuma, tarihin kiristoci yana cike da bala’oi, da yakukuwa a ciki da waje, wadanda suka lankwame rayukan miliyoyin kiristoci, yakin duniya na daya da na biyu kawai, idan muka duba ya ishe mu, wadanda a kasashen kiristocin, aka gwabza su.
Don karin haske a duba wadannan durussa da suke tafe.
- Jahannama da wadanda ba musulmi ba, tamabaya ta 2089 (lambar dandali 372)
- (Adalcin Allah da rashin sanin shi’anci ga mutun) tambaya ta 5788 (lambar dandali: 7202)
- (Tuban musulmai da wadanda ba musulmai ba) Tambaya ta 1606 (lambar dandali ; 1626)
[1] A duba littafin tafsirul mizan, wallafar sayyid Muhammad Husain, tabataba’ijuzu’i na 44-48 bugun maktab annashril islamiy, kum, bugu na biyar, shekara ta 1417, hijira kamariyya.
[2] Suratul isra’I 18-20
[3]Suratul isra’I 18-20
[4]Jahili mai zurzurfan jahilci ana daukan sa ne, daidai da mutumin da hakikar gaskiya bata iso gare shi ba, ko kuma ta zo gareshi a tauye, ko ta gaba-baya, saboda haka kwakwalwarsa bata iya riskar hakika ba, ta yadda ya dace.