Please Wait
26816
Akwai sabani mai yawa kan cewa shedan aljani ne ko mala'ika, da mahanga daban-daban.
Asalin wannan sabanin yana komawa zuwa ga halittar annabi Adam (a.s) ne yayin da Allah ya ba wa mala'iku umarnin su yi sujada sai dai shedan ya ki yin sujada.
Wasu suna cewa shedan (iblis) yana daga cikin mala'iku, kuma suka kafa dalili da cewa: a ayar an togace shedan daga mala'iku ne da fadin cewa (dukkan mala'iku sun yi sujada sai dai Iblis) don haka iblis yana daga jinsin mala'iku ne.
Amsa: Togace shedan daga cikin mala'iku ba ya iya nuna cewa shi yana daga cikin jinsinsu ne; sai dai yana iya nuna cewa Iblis (saboda yawan ibadarsa shekaru masu yawa) ya kasance cikin mala'iku; amma saboda girman kai da taurin kai da tsaurin kai sai Allah ya fitar da shi daga cikin aljanna.
Akwai wasu bayanai da zasu iya karfafa wannan maganar kamar haka:
1- Ubangiji madaukaki yana fada a surar Kahf cewa: "Shedan (Iblis) yana daga jinsin aljanu ne".
2- Ubangiji, yana nuni da cewa mala'iku ba sa yin sabo, don haka mala'iku halittu ne ma'asumai da ba sa taba yin sabo, girman kai, taurin kai, alfahari, tsaurin kai, da sauransu.
3- A wasu ayoyin Kur'ani ya zo cewa akwai iyaye da kakannin shedan, kuma wannan yana nuna cewa akwai haihuwa daga shedan da tsakanin aljanu, yayin da su kuma mala'iku babu wannnan game da su, domin su halittu ne rauhanai da ba sa ci, ba sa sha, da sauran abubuwan sauran halittu.
4- A wasu ayoyin Kur'ani Ubangiji madaukaki ya sanya mala'iku a matsayin 'yan sakon Allah, wadanda kuwa yake aikawa don wani lamari ba yadda za a samu wani sabo ko kuskure ko zunubi tare da su, yaya kuwa shi shedan zai zama daga cikin mala'iku tare da cewa ya yi wannan sabon mai girma.
Hada da cewa, akwai haduwar malamai da ittifakin su da kuma ruwayoyi da suka zo mana daga ma'asumai masu daraja da suke nuna cewa shedan ba ya daga cikin mala'iku. Kuma kamar yadda muka sani mafi kusancin ma'aunin gane gaskiya shi ne hadisi.
Dalilin asali na kawo wannan tambaya shi ne batun halittar annabi Adam (a.s) ne, yayin da Allah madaukaki ya yi nufin halittar mutum, kuma ya nemi mala'iku su yi masa girmamawa da ladabi, sai suak yi tambaya da neman bayani daga Allah madaukaki suka ce: shin mu ba mu ne muke yi maka tasbihi muna tsarkake ka ba? To don me za a halicci mutum? Yayin da Allah madaukaki ya yi musu bayanin halittar mutum, ya gaya musu cewa mutum shi ne halifan Allah a bayan kasa, sai suak amsa kiran ubangijinsu suna masu kaskan da kai, suka yi sujada ga Adam (a.s), suka karbi umarnin Allah madaukaki, kuam suka tsarkake kira da amsawa da girmamawa da yin sujada ga Adam (a.s).
A cikin mala'iku ko kuma mu ce wadanda suke sahun mala'iku akwai iblis wanda shi ma ya yi ibada tsawon lokaci ga Allah madaukaki, amma a cikin zuciyarsa akwai wani abu wanda in ban da ubangji madaukaki babu wanda ya sani sai shi. Wannan sirrin kuwa ya dade da boye shi, amma a bisa lamarin annabi Adam (a.s) sai lamarin sa ya fito fili, aka yaye sirrinsa, kafircinsa ya fito fili. Shi tun da can ya kasance kafiri ne, sai dai wannan bai bayyana ga saurna halittun Allah ba, kuma girman kansa da jiji da kansa ya bayyana a fili ta hanayar kin yin sujada ga annabi ada (a.s), ya fito fili daga mayafin lullubin kafirci.
A lokacin a Allah madaukaki ya bayar da umarni ga mala'iku da su yi sujada ga Adam sai duk suka yi biyayya ban da shi iblis sai ya ki yin sujada da kin biyayya ga umarnin Allah ya ki yin sujada. Dalilin sa kuam shi ne cewa an halicce shi da wuta, shi kuwa annabi Adam an halicce shi da kasa ne, yaya kuwa zai yi sujada alhalin shi ne ya fi daukaka?
Kai ka ce iblis ya gafala daga mene ne hakikanin annabi Adam (a.s), kai ka ce bai ga cewa shi ne Allah ya busa wa ruhinsa ba, kai ka ce bai ga yadda ubangijinsa ya ba shi daga falalar ruhinsa ba, shi a zatonsa wuta ta fi taushi sai ya yi kiyasi ya fada cikin kuskure, sai da wannan ba shi ne mahallin bahasinm ba, shi kawai ya duba bangaren halittar jiki ce ta mutum, sai ya fagala daga wancan matsayi babba na da Adam wanda yake busawar ruhin Allah ne. sai aka kore shi daga rahamar Allah da aljannarsa. Wannan kuwa tun farko abin da ya jawo masa shi ne yin alfahari, sannan na biyu ya yi girman kai daga karshe ya ki biyayya ga Allah, sai kuma ya samu tabewa.
Tun farko tambaya a nan ita ce: shin shedan yana daga cikin mala'iku ne ko kuwa? Kafin bayani ya kamata mu san wadannan abubuwan a takaice, domin mu iya sanin amsar daidai mai karfi, don haka sai mu fara da binciken wadannan kalmomin kamar haka:
a) Shedan b)Iblis c) Mala'ika d)Aljani
a) Shedan: Shedan tana nufin mummunar halitta mai tawaye da shisshigi da taurin kai da girman kai ga umarnin Allah, wannan kuwa ya hada mutum da aljan, kuma ana gaya wa duk wani ruhani asharari mai sharri wanda wannan ne asalin kiran kalmar shedan ga wata halitta. Don haka shedan ya hada duk wani abu mai karkata ga barin tafarkin shiriya da ya hada da mutum da wanda ba mutum ba. Kuma a kur'ani da ruwayoyi haka ya zo, hatta da mutumin da ba shi da halaye masu kyau kamar hassada an gaya masa shedan[1].
b)Iblis: Wannan suna ne da ake gaya wa wannan samammen da ya fara sabo ta hanyar kin yin sujada ga annabi Adam (a.s), ya yi alfahari da girman aki ya ki bin umarnin Allah madaukaki sai aka kore shi daga aljannar Allah madaukaki.
Yana da sunan "Azazil"[2] kuma kalmar Iblis lakabinsa ce da tana nufin wanda ya yanke kauna, kuma a bisa zahiri tana nufin wanda ya yanke kauna daga rahamar Allah ne.
c) Mala'ika: Yana da kyau mu kawo wasu daga siffofin mala'iku domin mu samu kaiwa ga samun amsar cewa; domin su mala'iku ba sa yin sabo, don haka shedan ba zai iya kasancewa daga cikin mala'iku ba[3].
Mala'iku su halittu ne da Allah ya yi musu kyakkyawar sheda a cikin Kur'ani mai girma yayin da yake cewa: "Su bayi ne masu girma, ba sa rigon sa da magana kuma suna aiki da abin da ya umarce su"[4], don haka a cikin mala'iku ba a taba samun wani abu sabanin gaskiya, kuma ko da yaushe suna masu shagaltuwa da ibada ne da biyayyar ubangijinsu. Su halittu ne ma'asumai da ba sa yin sabo. Su masu tsarkin zuciya ne da har abada ba sa yin sabo. Mafi muhimmanci shi ne biyayayrsu ga Allah da rusunawarsu gare shi. Suna masu nuna kaskan da kai, da gajiyawarsu game da abin da suka sani, da rahsin alfahai da girman kai, domin suna da yakini cewa duk wani abu da suke da shi daga Allah madaukaki ne, kuma idan ya so a cikin sakand daya ya kasance iradarsa ta ta'allaka da wani abu da bai sani ba, to duk abin da ya sani zai kasance rashin sani ke nan.
Wannan mafi muhimmancin bambancin tsakanin mala'iku da shedan yana iya bayyana a cikin lamarin halitta da sajada ga Adam (a.s). Domin mala'iku sun riga daga cikin zukatansu sun san cewa ba su san ilimin sunaye ba, wato sun san cewa su ba su gane ba. Amma shedan sai ya yi girman kai ya dauka cewa shi ya san komai, kuma bai san cewa yin sujada ga Adam (a.s) ya kasance sakamakon ilimi ne da Allah madaukaki ya bai wa annabi Adam (a.s) shi ne ba, kuma kwakwalwarsa mai duhu ba zata taba samun damar sanin wadannan ilimomin ba. Sai girman kansa da takamarsa suka hana shi ganewa, daga karshe kuma wannan ya kai shi ga kasa yin sujada!.
Da wannan bayani ne zai zama a fili yake cewa tun da mala'iku ma'asumai ne, kuma ba sa yin sabo, kuma tun da sabo ba zai yiwu gare su ba, to dukkan ayyuikansu zasu kasance biyayya ce ga Allah. Kuma idan biyayya ta kasance wajib ga wata halitta, to ba zai yiwu ya yi sabo ko kafirci ko girman kai ba. (wannan kuwa wani dalili ne na hankali game da bambancin shedan da mala'iku, daga karshe ke nan zamu iya cewa mala'ika yana kishiyantar shedan ne).
d) Aljani: Aljan wani halitta ne da aka boye shi daga ganin mutum, kur'ani ya yi bayanin samuwarsa, kuma ya yi bayanin wasu lamura da suak shafe shi kamar cewa daga wuta aka halitta shi; haka nan ya yi bayanin cewa an halitta mutum daga tabo ne, ko da yake halittarsa kafin halittar mutum ne[5].
wasu suna ganin cewa aljan yana daga halittar da take ruhi ce maras jiki, sai dai dalilai sun zo cewa ba maras jiki ne gaba daya ba, domin abin da aka halitta daga wuta to yana da wani nau'in jiji wanda kusan rabi ba jiki ba ne, wato ana iya cewa jiki ne mai taushi da laushi[6].
Daga ayoyin kur'ani zamu fahimci cewa aljani yana kama da mutum ta fuskancin cewa yana da nufi da irada da riska, kuma yana iya yin ayyuka masu wahala, sannan akwai muminai da kafirai a cikinsu, akwai salihai da fasidai , kuma suna rayuwa suna mutuwa kamar dai mutum, akwai maza da mata a cikinsu, sannan suna aure su hayayyafa da yawa a tsakaninsu.
Amma maganar asali ita ce cewar shin iblis mala'ika ne ko kuwa, a nan an samu sabani tsakanin malamai, kuma ta yiwu sabanin ya taso ne daga riko da bayanin da ya zo a wasu ayoyin kur'ani mai daraja.
Wasu suan cewa shedan mala'ika ne, kuma sun kafa hujja da ayar kur'ani da fadin Allah madaukaki yayin da yake cewa: "Kuma yayin da muka ce da mala'iku ku yi sujuda, sai suka yi sujada sai iblis"[7]. Domin a wannan ayar an toge shedan kuma daga mala'iku ne aka toge shi, don haka shi yana daga cikin mala'iku ne.
Amma bisa gaskiya shi ne cewa iblis ba ya daga cikin mala'iku, akwai ruwayoyi masu yawa da suak zo daga imaman shiriya cewa akwai ma ijma'I a kan hakan cewa iblis yana cikin aljanu ne ba daga cikin mala'iku ba, kuma akwai dalilai da suke karfafar hakan da zamu yi nuni da wasu a nan.
1- Allah yana cewa: "… Iblis ya kasance daga cikin aljanu", wato shi aljani ne ke nan[8].
2- Ubangiji yana cewa: "Ba sa sabon Allah abin da ya umarce su, kuma suna aikata abin da ya umarce su"[9], a nan an kore duk wani sabo daga mala'iku baki dayansu, wato abin da zamu fahimta a farko shi ne; fadin cewa babu wani mala'ika da yake nuni da dukansu baki daya, sannan na biyu babu wani sabo da wani mala'ika zai yi.
3- Ubangiji yana cewa: "Shin zaku rike shi masoya shi da zuriyarsa sabanina, alhalin suna makiya gare ku"[10], wannan yana nuna cewa a tsakanin aljanu akwai wata zuriyar wasu jama'a da suke haihuwa, yayin cewa mala'iku su halitta ce da ba su da irin wadannan abubuwan.
4- Ubangiji yana fada cewa: "Mai sanya mala'iku 'yan sako", wato Allah yana sanya wasu 'yan sako daga cikin mala'iku[11]. Kuma mun san cewa sabo da kafirci ba ya halatta ga wani dan sako.
Amma game da amsar dalilin masu ganin cewa toge iblis yana nufin shi yana daga cikin mala'iku, dole ne mu ce da su: toge iblis daga mala'iku ba ya iya nuna cewa shi yana daga cikin jinsin halittar mala'iku. Abin da kawai zamu iya fahimta shi ne cewar iblis yana cikin sahun mala'iku da yake rayuwa a cikinsu, kuma an yi umarni da ya yi sujada kamar yadda aka umarci mala'iku. Don haka ma wasu suke cewa togaciya a wannan ayar togaciya ce yankakka, wato abin da aka toge wani daga cikinsa a wannan jumlar babu shi[12].
Game da siffar shedan kuwa suna cewa ya yi ibada kusan shekaru dubu shida ne, don haka irin wannan abin halitta da ya shagaltu da yin ibada tsawon wannan lokacin babu mamaki idan ya kasance daga cikin mala'iku.
An tambayi Imam Sadik (a.s) game da cewa shin iblis yana daga mala'iku ne ko kuwa yana daga cikin halittun sama ne, sai ya ce: Shi ba ya daga cikin mala'iku kuma ba ya cikin sauran halittun sama; sai dai shi aljani ne; amma yana tare da mala'iku ne. mala'iku ma sun yi tsammanin ko shi ma yana daga ikin irinsu ne, amma sai Allah madaukaki ya nuna musu cewa ba haka ba ne. wannan kuwa ya ci gaba har sai da Allah ya tona sirrinsa game da lamarin yin sujada ga Adam (a.s) [13].
Karin bayani sai a duba:
1- Dabarasi: Majma'ul bayan: j 1, s: 163, ayar bakara ta 34.
2- Dibadiba'i: Muhammad Husain: tafsirul mizan, j 1, s: 122, da j 8, s: 20.
3- Jawadi Amuli Abdullah: Tafsirul maudu'I Kur'an Karim: j 6, halittar Adam.
4-Misbah Yazdi Muhammad Taki: ma'ariful kur'an, 1-3, s: 297.
5- Tafsiru namune: j 1, ayar 34 bakara, da j 11, s: 8.
[1] Ragib Asfahani: Mufradat, kalam shedan.
[2] Dabarasi: majma'ul bayan, j 1, shafi: 165, Bairut.
[3] Harafin alif da lam a ayar yin sujada ga Adam (a.s) tana nufin dukkan mala'iku ne aka umarta da yin sujada ga Adam (a.s).
[4] Anbiya: 26 – 27.
[5] Shi kuwa aljani mun halicce shit un farko daga wuta mai kuna. Hijr: 27.
[6] Tafsiri Namune: j 11, s: 79 – 80.
[7] Bakara: 34.
[8] Kahfi: 50.
[9] Tahrim: 6.
[10] Kahfi: 50.
[11] Fadiri: 1 – Hajji: 75.
[12] Don karin bayani ana iya duba: Majma'ul bayan, surar Bakara: 34.
[13] Dabarasi: majma'ul bayan: j 1, s: 163, bugun Bairut.