Please Wait
18576
- Shiriki
Fatawar Jagoran Juyin musulunci mai girma sayyid Kham’na’I game da mu’amalar banki a daulolin da ba na musulunci ba ita ce:
a- Bayar da Riba garesi haramun ne; Wato karbar dukiya daga bankin a kan cewa rance ne da sharadin dawo da kudin da ya haura hakan yawa, haramun ne. Sai dai idan ya matsu sosai kwarai matsuwa da ta halatta ya karbi haram din, sai dai gudun kada ya fada cikin aikata haramun mutum yana iya niyyar ba zai dawo da karin da aka dora masa ba, ko da kuwa ya san cewa zasu nemi ya kawo wannan kudin karin[1].
b- Ya halatta a karbi kudin riba (kudin ruwa) da na ribar ciniki daga bankunan Daulolin da ba na musulunci ba[2].
Kuma Sayyid Kham’n’I ya bayar da fatawa game da Takardar Canji kamar haka: Ba matsala game da kudin da ake ajiyewa a akawunt da mutum yake dibar su yayin da yake bukatar su, amma dukiyar da ake ajiye ta a akawunt - ba tare da an samu wani kudi da mai akawunt ya zuba ba – idan ta kasance da sunan rance ne, kuma ya zama akwai ribar kasuwa, to asalin bashin da aka bayar ya yi, sai dai karbar dadi kan hakan cin riba (kudin ruwa) ne kuma haramun ne[3].
[1] Taudhihul Masa’I na marja’o’I, j 2, shafi: 935, s 1911.
[2] Abin da ya gabata: shafi: 936, s 1917.
[3] Amsar Ofishin Jagora ga Tambaya 369, Maudu’i: Takardun Canji da Kudin ruwan Banki.