Please Wait
Dubawa
7287
7287
Ranar Isar da Sako:
2012/07/23
Takaitacciyar Tambaya
Shin hadisin da ke cewa: “Mutane (musulmi) zasu rbu zuwa bangarori saba’in da uku (73)” ingantacce ne kuwa?
SWALI
Ina son bayani kan yanzu bangarori nawa ne yanzu cikin muulunci? na samu hadisi game dashi da ke cewa: “Mutane (musulmi) zasu rbu zuwa bangarori saba’in da uku (73)” ingantaccene kuwa? Shin akwai karin bayani cikakke da zai gamsar?
Amsa a Dunkule
Malaman hadisi daga sunna da shi’a sun kawo hadisin “rabuwar mutane” ta bangarori masu sabawa juna. Kuma dukkan wadannan hadisai da Shi’a, sunna suka kawo yana labarto rabuwar musulmai bayan manzo (s.a.w), ruwaya ce a yadda take, idan zamu dauki daya daga ruwayoyin Shi’a daga wadannan hadisai masu yawa ta inganta ta bangaren isnadinta (saduwar sanadi)
Amsa Dalla-dalla
Bayan tafiyar kowane annabi daga annabawan Allah (s.w.t), canji da tsananin bakin ciki na samun mabiyansu na ainihi masu bin ainihin hanyar da suka shimfida musu. Sanin manzo (s.a.w) da abin da zai faru ga al’ummarsa bayansa ya sanya shi fada musu abubuwan da zasu faru ta hanyar ruwayoyi da dama (kamar hadisin da ke Magana kan rabuwar al’ummarsa) ta yadda zaka samu malaman hadisi daga shi’a da sunna duk sun kawo hadisin “rabuwar al’umm” ta hanyoyi da dama[1]. An rawaito wannan hadisi ta wurare da yawa cikin manya manyan litattafan shi’a kamar Alkhisal na sheikhus Saduuk da tafsirul iyashy da Ihtijaj na dabrysy[2]. Kari da cewa wadannan hadisai sunzo ta bangarori masu ma’ana; abin nufi sunyi tarayya wajan ma’ana daya, sabanin da sukayi shi ne a salon maganarsu cikin kalmomi da lafuzza da aka yi amfani da su.
Wadannan ruwayoyi duk sun labarta mana cewa manzo (s.a.w) ya bada duk labarin abubuwan da zasu faru ga al’ummarsa bayansa da rabuwar da zasuyi zuwa kaso saba’in da uku (73). Daga mafi ingancin sanadi a wadannan ruwayoyin shi ne hadisin da Kulainy ya rawaito cikin Al’kafy daga Imam bakir (a.s) daganan zamu duba tare da binciken sanadinsa (tushensa) da mataninsa (karfinsa):
Tushen (Sanadin) Hadisin
Muhammad dan Yahaya ya karbo daga Ahmad dan Muhammad dan Isa shi kuma daga dan Mahbubu daga Jamil dan Salih daga baban Khalid Al’kabuliyyi daga baban Ja’afar wato Imam Bakir (a.s) . wannan hadisi ta bangaren sanadinsa ya kasu zuwa bangarori biyu ; daga ciki akwai ingancinsa ta samun salsala ta sanadi daga manya manyan masu rawaito hadisai daga shi’a[3] wato mafiya yawan masu ruwaya na shi’a sun kawo shi , idan kuwa masu ruwayoyi sun kawo shi ta tushe daya ta hannun wadanda a zamaninsu su ne manya kuma masu girma wajan ruwaya, Muhammad dan Yahaya na daga cikin wadannan manya manya harma Najashi na fada game da Muhammad dan Yahaya cewa: Muhammad dan Yahaya ya kasance dattijon malaman hadisi a zamaninsa wajan dangantaka, daukaka da yawan hadisai[4], kuma Najashi ya kara fada game da Muhammad dan Isa “abu Ja’afar (a.s) Allah (s.w.t) ya yi masa rahama shi ne mafi girman mutanen zamanisa kuma mafi daukakarsu, fuskarsu sannan kuma mafi saninsu a ilimi”[5]. Haka nan Hassan dan Mahbub yadda ya samar da litattafai da dama na mazaje kuma yana daga cikin ma’abota ijma’i[6]. Hadi da Jamil dan Salih da baban Khalid Alkably shima na daga manya manyan masu girma[7]. Don haka hadisin ta bangaren sanadi ya inganta kuma ya sadu (zuwaga wanda yai shi wato Imam Bakir (a.s).
Nassin (Ainihin) Hadisin
An rawaito wanna hadisi cikin tafsirin aya ta 29 suratuz zumar inda Imam (a.s) yake cewa “hakika yahudawa sun rabu bayan annabi Musa (a.s) zuwa bangarori saba’in da daya (71), kaso daya daga ciki su ne yan al’janna, sauran kason duk yan wuta ne, hakama bayan annabi Isa (a.s) kiristoci sun rabu zuwa Bangarori saba’in da biyu (72), ka so daya daga ciki su ne yan al’janna, sauran kason duk yan wuta ne, hakanan ma bayan manzo (s.a.w) Al’umma (musulmi) zasu rabu zuwa bangarori sabain da uku (73), kaso daya daga ciki su ne yan al’janna, sauran kason duk yan wuta ne, daga saba’in da ukun , sha uku (13) na nuna sun yarda da wilayarmu[8], sha biyu (12) daga ciki basu sallama mana (yadda ta dace) ba, daya ne kawai suka sallama mana, wadannan dayan su ne yan aljannar, sauran sittin din na daga sauran mutanen da basu da wilayarmu, wadanda suke a wuta”[9].
Ta hakan sanadin hadisin ingantaccene kuma hujjar ainihinsa (tushensa) nada fadin dalili, sannan hadisai da dama na karfafar wannan hadisin musamman ma wadanda sukazo da irin wannan lafazi. Kuma akwai daga litattafai da yawa da suka kawo ruwayoyi kan wannan kamar: Firkatun-najiya shi’ar Imam Ali (a.s)[10]. domin neman karin bayani da zai gamsar kan ilimai a wadannan duba;

- Tambaya ta 487 (mauki’iy:528) (sabubban samun bangarorin musulunci)
- Tambaya ta 7550(mauki’iy:9819) (dalilan faruwar mazhabobi da bangarori).
[1] Attaba taba’iy Muhammad Hassan Almizan bolume 3 page 379 Kum maktabatun nashrul islam Kum 1417 AH , Ja’afari Yakuub Tafsirul kauthar bolume 3 page 443 ba shekara.
[2] Allama majlisy , Muhammad Bakir , biharul anwar bolume 28 page 4 mu’assasatul wafa’a Beirut 1404 AH.
[3] Barnamij Dirayatun nuur, musdlahat ilmul Hadith.
[4] Annajashy, rijalunnajashy page 351, daftar intisharatul islamy , Kum 1407.
[5] Ainihin littafin.
[6] Rijall khashy page 556.
[7] Rijalun najashy page 127 , rijalul khashy page 10, intisharat jamiatu mashhad 1348.
[8] Ya kusata ya zama nuni zuwa bangarorin shi’a wadanda ba mabiya imamai sha biyu (12) ba.
[9] Kulainy, Muhammad dan ya’akub, Alkafy bolume 8 page 224 darul kutubul islamiyya Dahran 1368.
[10] Biharul anwar bolume 8 page 2 babin rabuwar Al’umma bayan manzo (s.a.w).
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga