Please Wait
Dubawa
12745
12745
Ranar Isar da Sako:
2014/10/23
Lambar Shafin
fa7883
Lambar Bayani
97075
- Shiriki
Takaitacciyar Tambaya
Shin matsayin Imamai ya fi na Annabawa?
SWALI
A cikin littafin Hukumatul Islamiyya Imam khomeni (r.a) yana cewa: Hakika matsayin Imamai ya kai kololuwar da ba wani mala’ika kuma ba wani Annabi Marsali da ya isa ya kamo wannan matsayin. Hukumatul Islamiyya shafi na 25, ya zamu dauki wannan maganar?
Amsa a Dunkule
Ruwayoyi masu yawa sun nuna fifikon matsayin ilimin Imamai (a.s) a kan Annabawa, dalili kan wannan maganar shi ne kadaitakar haske da kadaitakar badinin Imamai (a.s) tare da Manzon Allah (s.a.w), saboda shi Manzon Allah (s.a.w) ya fi baki dayan Annabawa, sannan kuma ilimin Imamai an samo shi ne daga Manzon Allah (s.a.w) kuma daga mabulbula (mabubbuga) daya, don haka nema ake fifita su a kan sauran Annabawa sannan a tunanin musulunci an yadda cewa mutum ya fi mala’ika, don haka ba mamaki in an fifita matsayin Imamai ma’asumai a kan mala’iku, “E’’ tabbas an yi bahasi kan fifita Imamai a kan mala’iku, wannan maganar za a tattauna ta filla-filla a nan gaba.
Amsa Dalla-dalla
Tabbas maganar khomeni (k.s) an samo ta ne daga cikin hadisan da aka ruwaito masu yawa a cikin manyan littattafai, cikinsu akwai:
An karbo daga Ahmad bn Muhammad ya karbo daga Muhammad dan Husaini daga Mansur dan Abbas daga Safwan bn Yahya daga Abdullahi bn Muskan daga Muhammad bn Abdilkhalik da Abu Basir ya ce: Abu Abdullahi (a.s) ya ce: “Ya Muhammad wallahi akwai sirrin Allah a wajenmu da ilimi daga ilimin Allah, wallahi makusancin mala’ika ko Annabin da aka aiko ko muminin da aka jarrabi zuciyarsa da imani ba su iya daukansa, wallahi Allah be kallafawa wani ba sai mu be kuma sa wani ya yi masa bauta da haka ba sai mu”([1]).
Tun daga nan ba makawa sai an karanta mas’alar fifikon matsayin su da iliminsu tare da dogaro da ruwayoyin da ‘yan shi’a suka dogara da su kan abin da suka tafi a kai na wannan Akidar kafin mu kutsa cikin binkicen matsayin Imamai zamu nuna wata fa’ida wato, fifikon mutum a kan mala’ika cewa kowa ya yarda da haka a tunanin musulunci, don haka ba mamaki in an fifita matsayin Imamai ma’asumai a kan matsayin mala’iku Na’am, an yi bahasi kan fifita Imamai a kan mala’iku ta fuskoki masu yawa, zai yiwu a karanta hakan ta bangarori masu yawa ba tare da sabawa tushen musulunci ba, kai sanin matsayin Imamai na da alaka mai karfi da hakikanin manufar musulunci wacce ta wajaba kowanne musulmi ya san ta da kuma sanin kebance-kebancen cikakken mutum, domin tabbatar da wannan maganar zai yiwu mu wuce ta kan nukudodin nan masu zuwa don isa ga hakikanin wannan mas’alar:
Fa’ida ta farko: Tabbas ma’asumai goma sha hudu duk kaninsu hakika daya ce, a wani bayanin kuma: duk kansu haske dayane wannan kadaitakar hasken na mutanen gidan Manzon Allah (s.a.w) tabbas ruwayoyi da yawa sun bayyana haka, a wani lokaci nuni ya zo kan ma’abota kisa’i su biyar cewa haskensu abu daya ne, a wata ruwayar ishara ta zo kan cewa hasken baki dayan , Ma’asumai (a.s) abu daya ne.
Cikin wadannan ruwayoyin akwai:
A - Allah (a.s) ya ce: “Ya Muhammad na halicce ka na halicci Aliyu da Fadima da Hasan da Husaini daga nau’in haske na na kuma bijiro da wolayarku ga ma’abota sammai da kassai, duk wanda ya karbe ta to a waje na yana cikin muminai duk wanda ya yi musunta, to a wajena yana cikin kafirai Ya Muhammad da bawa daga cikin bayina zai bauta min har ya zama kamar tsohowar salka, sannan ya zo min yana musun wilayarku da ban gafarta masa ba, har sai ya tabbatar da wilayarku”([2]). Wannan hadisin na cikin hadisan mi’iraji wanda Allah Ta'ala ya zantar da Manzonsa (s.a.w) da shi a lokacin da ya yi mi’iraji.
B- Akwai: “Ya Muhammad tabbas na halicci Aliyu da Fadima da Hasan da Husaini da Imamai daga haske daya, sannan na bijiro da wilayarsu ga mala’iku duk wanda ya karbe ta zai kasance cikin makusanta, duk wanda ya yi musunta yana cikin kafirai, Ya Muhammad da bawa daga cikin bayi na zai bauta min har sai ya sare, sannan ya hadu da ni alhalin ya yi musun wilayarsu da na shigar da shi wuta..([3]). A cikin wannan ruwayoyin akwai nuni kan cewa hasken baki dayan Imamai (a.s), abu daya ne.
2- Fa’ida ta biyu: Lallai baki dayan Ahlulbaiti (a.s) sanada matsayin wilaya([4]). Ma’ana su ne halifofin Manzon Allah (s.a.w) bugu da kari ga shugabancin Al’umma da shugabancin ilimi, tabbas suna da tasiri da iznin Allah tasiri na boye a kan bayi, kuma suna ganin rayuka da zukatan bayi, suna yin tasarrafi a cikin su tasarrafi na Takwini (na zartarwa da kin zartarwa).
Allama Dabadaba’i (r.a) ya fada a wannan fagen cewa: in ka ce: Idan Imamanci shi ne shiryarwa da izinin Allah Ta’ala ita ce shiryarwa zuwa gaskiyar da ke manne da shiryuwa ta zati kamar yadda aka tsamo haka a maganar Allah Ta’ala “shin wanda ke shiryarwa zuwa gaskiya shi ne ya fi cancanta da a bi shi” aya baki dayan Annabawa Imamai ne yanke, saboda bayyanar cewa Annabtar Annabi bata cika sai da shiryarwa daga wajen Allah ta hanyar wahayi ba tare da an samo daga wajen wani ba ta hanyar koyarwa ko nusarwa da kwatankwacin su ba, to shin wanda aka ba wa baiwar Annabta ya zama wajibi a ba shi baiwar Imamanci kenan, da wannan zai zama Ishkalin ya dawo wajenku dai.
Na ce: Abin da ya tabbata a cikin bayanin da ya gabata wanda aka gano shi a cikin ayar shi ne shiryarwa da gaskiya ita ce Imamanci wacce take lazimta shiryuwa da gaskiya, amma akasin haka wato: ya zama duk wanda ya shiryu da gaskiya zai shiryar da wani, wannan bai tabbata ba ballanata ya zama ko wanne Annabi saboda shi shiryayye ne sai ya zama Imami, ba a sami wannan daga cikin ayoyi ba, tabbas Allah Ta’ala ya fadi wannan shiryuwar (ta annabta) ba tare da ya hada ta shiryar da wani da gaskiya ba([5]).
Zai yiwu ace wilaya kala biyu ce: wilaya Ta shiri’a (ta nuna hanyar tsira da fada wa mutane abin da Allah ya yi umarni da wanda ya hana) da wilaya Takwiniyya.
Wilaya Ta shri’a tana nufin: Hakkin shar’antawa (sa doka umarni da hani) na Allah ne kawai, bai danka wannan a hannun wani daga cikin bayinsa ba, har Annabi Muhammad (s.a.w)([6]). Shi ma mai gargadi ne da bada bishara da isar da sako da bayanin hukunce - hukunce([7]).
Amma wilaya Takwiniyya tana nufin: ikon zuciya da iya tasarrufi a cikin halittar Allah da izinin Allah tasarrafi na takwini (na kun fa yakunu) (kamar dawo da rana bayan ta fadi da tsagewar wata, da tada matacce dss).
Daga nan fa to tabbas baki dayan mu’ujizozi([8]). Da karamomin wilayan Allah Ta’ala suna zuwa ne daga wannan wilayar Takwiniyya, daga cikin wadannan mu’ujizozin ne mu’ujizar Annabi (s.a.w) ta zo kamar tsagewar, wata tsagewar bishiya ([9]). Da tsagewar kasa([10]). Da tsagewar teku([11]). A kissar Annabi Musa (a.s) da Fir’auna da tsagewar dutse a lokacin Annabi Salihu (a.s)([12]). Da warkar da makaho da mai albaras da raya matattu da Annabi Isa (a.s) ya yi([13]). Da cire kofar khaibara da Amirul muminina (a.s) ya yi cikin ban ala’ajabi([14]). Duk wadannan misalan ba zai yiwu a fassara su ba sai dai ace wilaya Takwiniyya ce ta cikakken mutum.
Fa’ida ta uku: wilaya ta kusanci da Allah da narkewa a cikin sha’anin Allah Ta'ala ([15]). Kusanci da Allah na tabbata ne ta hanyar yi masa biyayya (s.w.t) da siffantuwa da dabi’un da Allah ke so: abun nufi shi ne mutum koda ba zai iya ba kai ba zai taba yiyu wa ba kuma mustahili ne ma ya zama Allah, amma zai iya zama yana tare da Allah. Duk lokacin da ya hadu da tabbatacciyar mabulbula da babubbuga ta Allah, ya kuma kusanci Allah ya keta hijabobin duhu ya sami daman keta hijabobin haske ba kuma zai ga zatinsa da ayyukansa da siffofinsa ba, (wato ba tare da ya ga zatin Allah ba dun da ba zai yiyu ya ga Allah da ido ba) sunayen Allah da siffofin sa ne zasa dinga bayyana a tattare da shi ([16]). A wannan lokacin mutum zai iya yin tasarrafi a cikin maklukat ta sanafi Takwini ta hanyar yin amfani da kudrar da Allah Ta’ala ya ba shi, wanda shi kudrarsa - (Allah mabuwayi) - ba ta da geji.
Ya zo a Hadisin kudsi cewa: “Bawa na ka yi min da’a har in saka kwatankwacina (in zamar da ka kamar ni) ”([17]). An ruwaito: “Ya dan Adam ni mawadaci ne ba ni da bukata, ka bini a cikin abin dan na Umarce ka, zan mai da kai mawadaci ba zaka talauta ba, ya kai dan Adam ni rayeyye ne ba na mutuwa, ka bini a cikin abin da na Umarce ka zan mayar da kai rayeyye ba zaka mutu ba, ya dan Adam hakika ina cewa abu kasance sai ya kasance, ka bini a cikin abin da na Umarce ka sai kace wa abu kasance sai ya kasance”([18]).
Fa’idar ta hudu: Tabbas matsayin wilaya ya saba da matsayin Annabta ta fuskoki da yawa, amma a matsayin martabar wilaya ta fi Annabta daukaka.
Bayanin haka: waliyi a matsayin “Narkewa cikin sha’anin Allah” yana ganin hakikanin ainihin abubuwan Allah sai ya bada labarin su. Wannan ma’arifar ita ake kira da “Annabtar data game ko gamammiyar annabta” wani lokaci kuma a kan kira ta da “makamin Annabta” wani lokaci kuma a kan ce “Annabtar shar’antawa”. Shi Annabi ta bangaren ”Annabtar ma’ana” yana ba da labarin zatin Allah da siffofinsa da ayyukansa, ta bangaren “Nubuwatut Tashri’i” wato “Annabta ta shar’antawa” zai Isar da hukunce- hukunce da dabi’antuwa da halayya mai kyau ya kuma dinga koyar da hikima da al’amuran siyasa. Allah Ta’ala ya fada a littafinsa mai girma: “A lokacin da ya kai karfinsa sai muka ba shi hukunci da ilimi, haka muke sakawa masu kyautatawa”([19]) ma’anar ita ce mutumin da ya kai matsayin kyautatawa to za ya sami matsayin Annabta kamar yanda yake a mashayar Musa (a.s) ko da bai kai matsayin Annabi Musa (a.s) ba wato matsayin Shari’a([20]).
A bisa wannan asasi koda mu ba zamu iya kaiwa matsayin Annabta da matsayin manzancin shari’a ba, sai dai zai yiwu sanadiyyar bauta wa Allah da wuce marhalolin kamala zamu iya kaiwa ga matsayin kusancin sallolin Nafilfili da kusancin sallolin Farillai, sanadiyar haka sai mu samu matsayin Annabta da matsayin wilaya.
A kowane hali zai yiwu mu rairayo bambance -bambancen dake tsakanin matsayin wilaya da matsayin Annabta a cikin al’amura masu zuwa:

- Wilaya tana da wani gefe na cancanta, Annabta tana da yanayin halayya! Abin da ake nufi Annabta tana kallon bangaren zahirin wilaya, wilaya kuwa tana kallon badinin Annabta.
- Saboda Annabawa sun narke a cikin kadaitar zati don haka suna ganin hakikanin abubuwa na gaibu ana tashinsu a lokacin baka’i bayan narkewa a cikin zatin Allah, suna wattsakewa bayan shafe komai sai su bada labarin wadannan abubuwan bisa hakikaesu, amma a kowanne halin tushen Annabta dai bangaren gaskiya ne da Jibintarsu.
- Mai wilaya masanin shari’a ne da hakika gaba daya, ma’anar hakan; shi mai ganin zahiri da badini ne, sai dai da’irar Annabawa da Manzanni ta kebanta da shari’a da zahiri kawai.
- Mai wilaya yana ganin ayyukan badini da badinin mutum, daga nan ne ya wajaba ayi masa da’a ba tare da kaidi ko sharadi ba.
- Annabi da Manzo suna samun ilimi ne ta hanyar mala’ika da sauran hanyoyin wahayi, amman mai wilaya iliminsa daga wajen Allah ne, nan take ake kwararo masa daga badinin hakikanin Annabi Muhammad (s.a.w)([21]).
- Annabta da Manzanci an iyakance su da waje da lokaci don haka suna yankewa, sabanin wilaya, saboda wilaya tana daga cikin sunayen Allah Ta’ala([22]). Sunayen Allah wanzazzu ne tabbatattu([23]).
Natija (sakamako) shi ne; cawa tabbas wannan sunan yana bukatar mai bayyana shi, don haka wilaya ba ta yankewa ([24]) kuma cikakken mutum mai kamalar shi mabayyanar (wato mazhirin) wannan madaukakin suna mai kamala wanda shi ma (mutumin) ya kasance yana da wilaya cikakkiya, amma Manzo da Annabi ba sa daga cikin sunayen Allah Manzanci da Annabta siffofi ne da Allah ya bayar na wani lokaci wanda suke yankewa in lokaci ya wuce.
- Wilaya ta kunshi Manzanci da Annabtar shari’a, amma Annabtar da ta game (gamammiya) ba ta shafi ta shari’a ba, sanadiyyar haka ne ma ake ce mata falakin da ya kewaye Al’umma.
- Mai bada Annabta da Manzanci, sunan zahiri ne wanda ya rataya da tajalli, mai bada wilaya kuwa sunan badini ne wanda ke bada ma’anar ado.
- Wilaya badinin Annabta da Manzanci ne samun wannan al’amarin ya ginu ne a kan wilaya([25]).
Natija:
Daga abin da ya shude ta bayyana cewa:
Daga abin da ya shude ta bayyana cewa:
- Wilayar Manzon Allah ta fi Manzancinsa daukaka, wilayar Annabi ta fi Annabtarsa daukaka.
- Zai yiwu mai wilaya ba shi da matsayin Annabta, amma ya fi Annabi, ya kuma fi shi ilimi gwargwadon wilayarsa. Daga nan ne muke ganin khadir (a.s) yana zargin Musa (a.s) inda ya ce: “Tabbas ba zaka iya hakuri da ni ba” ya kara zarginsa da cewa: “shin ban gaya maka ba zaka iya yi hakuri dani ba”. A karshen lamari dai ya ce masa: wannan ce rabuwata da kai”([26]) daga nan muke ganin sayyid Masihu (a.s) zai yi ko yi da Imam Hujja (A.F) a lokacin bayyanarsa ([27]), tare da cewa Annabi Isa (a.s) Annabi ne yana cikin Ulul Azmi, ainihin Magana duk da khadir da Imam Mahdi (A.F) ba su sami darajar Annabta da matsayin kawo shari’a ba, amma su biyyun idan mun kalli wilaya Takwiniyya to fa suna gaba, khadir yana gaba da Musa (a.s) Imam Mahdi (A.F) ma yana gaba da Isa (a.s), daga nan ne za mu ga Amirul muminina (a.s) yake cewa: “Ina ganin hasken wahayi da na Manzanci ina kuma shekar kamshin Annabta, tabbas na ji rurin shaidan lokacin da aka fara saukar wa da Annabi wahayi” tabbas Manzon Allah (s.a.w) ya ce masa: “Tabbas kana jin abin da nake ji kana ganin abin da nake gani sai dai kai ba Annabi ba ne”([28]).
Mas’udi ya ruwaito daga Imam Hasan (a.s) ya ce bayan shahadar Amirul Muminina (a.s) “Wallahi wani mutum ya rasu a cikin daren nan, mutanen farko ba su gabace shi ba sai da fifikon Annabta, ‘yan baya ma ba zasu riske shi ba”([29]).
An karbo daga Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “Tabbas Allah na da bayin da su ba Annabawa ba ne Annabawa ma suna burin samun matsayinsu da kusancinsu a wajen Allah (t.a”)([30]). A wannan ruwayar ta karshe ban da bayyana fifikon wasu salihai a kan Annabawa duk da cewa su din ba Annabawa ba ne, akwai bayyana sirrin wannan fifikon kamar yadda ya ce: “Da kusancin su a wajen Allah Ta’ala” hakan na nuna fifikon su a kan Annabawa, wannan ne abin da ya bayyana sanadiyyar bayanin daya gabata, wanda a ciki mu kace kamalar kusanci ba wani abu ba ne sai wilaya Takwiniyya.
Wa kazalika, Kamar yadda ayar da zamu kawo yanzu take cewa: “kafirai na cewa kai ba Manzo ba ne ka ce Allah ya isa ya zama shaida tsakani na da ku, da wanda aka bawa ilimin littafi”([31]). A cikin wannan ayar mai albarka Allah mahalicci ya yi ishara ga shaidu biyu na farko zatin Allah mai tsarki dayan kuma wanda ya san ilimin litttafi. Ba kokwanton cewa Allah (s.w.t) ya shaida da mu’ujizozi, cikin mu’ujizozin akwai kur’ani mai girma, sai dai wa ake nufi a ayar nan da “wanda yake da ilimin littafi’’ me ya kebanta da su wanda suka sa ya zama mai bada shaidar gaskiya kan Manzancin Annabi (s.a.w)?
A takaice Aliyu bin Abi Dalib da Imamai masu tsarki (a.s) ne wadanda suke da matsayin wilaya Takwiniyya.
Don wannan al’amarin ya bayyana sosai zamu yi nuni ga kissar Annabi Sulaiman da kawo gadon Bilkisu wannan ne abin da ayoyin suka nuna 20 - 41 a suratul Namli:
Kissar ta fara da cewa Allah yake cewa: “Sulaiman ya nemi tsuntsu bai gan shi ba, sai ya ce me ya sa banga Alhudahuda ba ko ba ya nan ne! sai Alhuda-huda ya zauna ba tare da ya dade sosai ba, sai ya ce na san abin da ba ka sani ba, na zo maka daga Saba’i da tabbataccen labara “ har zuwa inda kissar take cewa sai Sulaiman ya ce: “ka tafi da wannan littafin nawa ka jefa musu sannan ka bada baya ka duba amsar me zasu bayar “ har Annabi Sulaiman ya nemi gadon Bilkisu “ya ce ya ku jama’a waye zai zo min da gadonta kafin su zo su mika wuya a gareni? Wani ifritun Aljani ya ce ni zan zo maka da shi kafin ka tashi daga zaman fada, ina da karfin yin haka, kuma ni amintacce ne. wanda ke da wane bangare daga ilimin littafi ya ce ni zan zo maka da shi kafin kiftawar idonka, lokacin da ya ganshi a gabansa sai ya ce wannan falalar Ubangiji na ce” abu ne a fili cewa wanda ya kawo gadon Bilkisu daga Yaman zuwa Falasdin cikin irin wannan saurin” kafin kiftawar idonka” ba kokwanto cewa yana da wilaya Takwiniyya kamar yadda ruwayoyi ke cewa Ismullahil A’azam a ma’anar da kur’ani ya kawo “ Yana da ilimin littafi “ kur’ani ya bayyana cewa wannan mutumin sanadiyyar wannan ilimin da yake da shi ya sami damar yin wannan aikin da ya sabawa al’ada, saboda ya sami darajar matsayin wilaya Takwiniyya, shi ya sa ya iya yin wannan babban aikin.
An karbo daga Manzon Allah (s.a.w) kamar yadda yake a cikin hadisin Abu sa’idil khudri ya ce: Na tambayi Manzon Allah (s.a.w) waye wanda yake da wani dan bangare daga ilimin littafi wanda aka kawo shi a kissar Sulaiman sai ya ce: wasiyyin dan uwana Sulaiman dan Dawuda ne, sai na ce: ayar “wanda yake da ilimin littafi“ waye wannan wanda take maganarsa? Sai Annabi (s.a.w) ya ce: Dan Uwana Aliyu bin Abi Dalib (a.s)([32]).
Akwai bambanci tsakanin “ilimi daga cikin littafi” wanda yake nufin ilimin wani babgare daga cikin littafi fa kuma wanda yake da “lilimin littafi” wanda yake nufin ilimin gaba daya” wanda hakan ke nuna bambanci mai nisa tsakanin asif da Aliyu (a.s)([33]).
Saboda haka muke karanta ruwayoyin masu yawa cewa Ismul A’azam harafi 73 ne, Asif na da harafi daya sai ya ambace shi ya dauko gadon Bilkisu har ya taba shi da hannunsa, sanan kasa ta koma yadda take cikin kiftawar ido harafi daya ne kawai a wajen “Asif dan Barkaya ya yi irin wannan aikin da ya sabawa al’ada a wajenmu mu Imamai muna da harafi 72 daya harafin nawajen Allah Ta’ala shi kadai ne ya kebanta da shi a ilimin gaibun dake wajensa([34]). Daga nan ne zamu ga Imam Sadik (a.s) yana fadan kissar Asif dan Barkaya: “A wajen mu wallahi akwai ilimin littafi gaba daya”([35]) yana nufin idan Asif dan Barkaya ya sami wani bangaren ilimin littafi to a wajenmu mu mutanen gidan Annabi (s.a.w) akwai ilimin littafi gaba daya.
Daga abin da ya wuce ya bayyana cewa wadanda suke da Ismul A’azam (masu wilaya takwiniyya) suna da fifiko a cikin wannan matsayin, kuma cikinsu akwai wanda ke da harafi daya, wasu kuma suna da harafi 72, wadan nan sun fi wadancan Imam Ja’afar Sadik ya yi magana a kan aya ta 43 a suratul Ra’adi: “mu yake nufi, Aliyu ne na farkonmu, kuma shi ne wanda ya fi mu bayan Manzon Allah (s.a.w)([36]). Don karin bayani kan wannan maudu’in da baki dayan bangarorinsa a duba littafin Nagarshi Irfani, Falsafa wa kalami be shaksiyyat wa kiyam Imam Husaini (a.s)([37]).

[1] Sikatul islam kulaini kafi J. 1 sh 402.darul kutubul islamiyya Tehran.
[2] Majlisi, Muhammad Bakir, Biharul Anwar J. 36 sh 216.
[3] Adreshin da ya gabata 281 da 223.
[4] Amirul muminina (a.s) yana cewa: “sunada kebance – kebance na hakkin wilaya “Nahjul Balaga huduba ta 2.
[5] Daba’daba’I Muhammad Husain, a cikin Almizan J. 1 sh 275 da 276.
[6] A iyakokin wannan hanin da da’irar cancanta Annabi (s.a.w) za a samu wasu karattuka da bayanin su za a same shi a rushen su.
[7] Suratul Jasiya, 13, Ra’ad, 8, Isra’i 106, ka duba Ibnu Arabi Muhibbud Dini, futuhatul makkiyya (j 4) J. 3 sh 69.
[8] A. Mu’ujizar zance ita ce tsararrun kalmomi da bayani daga wajen Allah da Manzo (s.a.w) da Imamai (a.s) wanda ke kusshe da masaniya mai zurfi da da kaskiyar da zata gigita hankula masana, akwai banbanci tsakanin mu’ujiza ta aiki da ta magana, shi ne ita mu’ujiza ta aiki tana da zamani da waje iyakantacce kuma mafi rinjaye ana yin ta ne don mutane game gari run da tana damfare da abubuwan ake ihsasin su (ji da gani da tabawa da ci da shinshina). Amma mu’ujiza ta magana ba ta da lokaci na musamman tana wanzuwa tsahon dukkanin zamuna, kuma ta danfara da mutane na musamman.
B. Tsagewar wata na daga cikin mu’ujizar Ma’aiki (s.a.w).

[9] Amirul mumina ya yi ishara kan haka a hudubarsa kaasi’a a cikin Nahjul Balaga.
[10] Suratul kasas aya ta 76 - 81.
[11] Suratul Bakara aya ta 50.
[12] Suratul shamsu aya ta 11 - 15.
[13] Suratul Ali Imran aya ta 49.
[14] Amirul mumina (a.s) ya fada a cikin wasikar da ya yiwa Usman bn Hanif Gwamnansa na Basara: “wallahi ban cire kofar khambara na yi jifa da ita ba a bayana har tafiyar zira’I arba’in da karfin jiki ko motsin karfin abinci ba, sai dai an karfafani da karfin Allah da nafsun da take bada hasken Ubangijinta” kalli Dabari Imadudden, Bisharatul musdafa sh 191, sheik saduk a cikin Amali majalisi 77 sh 513.
[15] Fana’I kala-kala ne: Fana’in zahiri shi ne fana’in ayyuka na Danshagar Ahmad, Diwan Hafiz sharhin irfani sh 144-145. Isharat wat Tanbihat na Ibnu sina, sharhin khoja Nasiruddeen Dusi J.3 makamatul irfani, sh 390, Imam Khomeini (ra) Arba’una Hadisi sh 382.
[16] Imam Hasan yana cewa: “Duk wanda ya bautawa Allah, Allah zai bautar masa da komai” Tafsirin Imam Hasanul Askari J. 1 SH 327. Biharul Anwar J. 68 sh 184.
[17] Asrarul salati na miraza Jawadaga J. 1 sh 4, (mukaddima) khu’iul musahhili, an nakalto ruwayar kamar haka: “Ya bayyana ka so ni zan soka kwatankwacina” Amuli, sayyid Haidar Jami’ul Asrar wa manbai’ul Anwar sh 363.
[18] Almajlisi, Muhammad bakir a cikin Biharul Anwar J. 9 sh 376. Dailami Hasan dan Hasan, a cikn Irshadul kulub ilassawab J. 1 sh 75, Inbi Fahad al-hilli a cikn Uddatud Da’i, sh 310.
[19] Suratul Yusuf 22.
[20] Ka duba Hasan zada Alamuli, Mumiddal Himam sh 657.
[21] Ka duba Yasribi, yahaya a cikin Falsafatul Irfan sh 181, Yahya Yasribi.
[22] Surar Shura sh 29, Huwal waliyyul Hamid. {shi ne shugaba mai yawan gobiya}.
[23] “Mahaliccin sammai da kassai, kai ne majibincina a duniya da lahira” suratul Yusuf 101.
[24] “Abin da ke wajen ku zai kare abin da ke wajen Allah wanzanjje ne” suratul Nahli, 96.
[25] Insannul kamil Fi Nahjul Balaga sh 84 - 86.
[26] Suratul kahfi 64 -78.
[27] Majlisi muhamma bakir, a cikin Biharul Anwar J. 9 sh 195, Tafsirn Numunah J. 4 sh 205 makarimush shirazi, nasir tafsirul amsal j 4 sh 205. Kashani, sayyid Abbas khashani, makhazin J. 1 sh 286.
[28] Nahjul Balaga huduba ta 192.
[29] Al-mas’ud Muruj Zahab J. 2 sh 414.
[30] Ibni hanbal a cikin Musnad Ahmad bn Hambali J. 5 sh 343, Riyadussalikin J. 6 sh 393, sayyid Ali khan, sharhul Asma’il Husna sh 552, mulla Hadi sabzawwari, Futuhat J. 13 sh 137 Ibnu Arabi.
[31] Suratul Ra’adi aya ta 43.
[32] Ihkakul Hak, na Alkadi Nurullah Ashshus tari J. 3 sh 280-281.
[33] Shirazi, Makarim Nasir a cikin Tafsirul Amsal J. 12 sh 7, musawi hamdani sayyin Muhammad Bakir a cikin Tarjamatul mizan J. 11 sh 532.
[34] Kulaini, Muhammad Yakub a cikin kafi J. 1 sh 230.
[35] Kulaini, Muhammad Yakub a cikin kafi J. 1 sh 229.
[36] Majlisi muhamma bakir, a cikin Biharul Anwar J. 1 sh 229.
[37] Da alkalamin kasim Tarkhan In tisharat Jaljarag.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga