advanced Search
Dubawa
10692
Ranar Isar da Sako: 2007/02/22
Takaitacciyar Tambaya
mece ce mahangar musulunci a kan samuwar halittu masu rai a sauran duniyoyi?
SWALI
mece ce mahangar musulunci a rayuwa cikin sauran duniyoyi?
Amsa a Dunkule

Akwai tunanin cewa a cikin sauran duniyoyi shin za a samu halittu masu rai ko hankali, daya daga cikin tambayoyin da dan Adam ke neman bayanin su, amma har yanzu bai samu ba. Wasu bayanai a Kur’ani na nuni da samuwar wasu halittu masu rai a duniyar sama, daga ciki akwai:

  1. Bayanin [min dabbatin} wato babu wata dabba. Wannan na nuni da ikon ubangiji na halittar sammai da kasa da nau'in halittu masu motsi a tsakanin su wadanda suka watsu a ciki in ya so shi mai iko ne a kan dawo da su[1].
  2. Bayani a kan wanda ke cikin sammai da abin da ke cikin sammai:

Duk wanda ke cikin sammai da kasa a gare shi yake bukata, kowane lokaci cikin aiki yake[2].

Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin kasa daga masu motsi da mala'iku, suna ma Allah sujada kuma ba su girman kai gare shi[3].

Sammai bakwai da kasa da abin da ke cikin su suna tsarkake shi[4].

3. bayanin gabas da yamma:

 Rantsuwa da ubangijin gabas da yamma cewa mu masu iko ne[5].

4. bayanin talikai[6]:

Godiya ta musamman ta tabbata ga ubangiji mai raya halittu[7].

A cikin ayoyin da mukayi bayani a kan su aya ta farko[8] da ayar da talikai tazo a ciki ne kadai a kuma takaice ke nuni da samuwar halittu masu rai a sauran duniyoyi[9].

Allama taba taba'i [r. a] a cikin tafsirin aya ta farko ya ce: a bayyane wannan ayar na nuni da samuwar halittu a cikin sama kamar yadda suke a duniyar kasa…"[10].

Mai tafsire namune ya rubuta: wannan ayar na tabbatar da samuwar halittu masu rai a cikin sama, koda yake ya zuwa yanzu masana ba su tabbatar da hakan ba sai dai suna cewa tabbas akwai halittu masu rai a sama, amma Kur’ani a fili ya tabbatar da hakikar samuwar halittu masu rai da yawa cikin duniyar sama[11].

Ya zo a hadisin imam Ali {a. s]: taurarin da ke cikin sama garuruwane kamar garuruwan da ke kasa, tsakani gari dagari {taurari da taurari} akwai ginshikin da ya hada su[12].

A kan tabbatar samuwar halittu masu rai a cikin sauran duniyoyi da aya tai bayani ya kamata a lura da wasu abubuwa kamar haka:

  1. Kalmar sama" da sammai" ya zo da ma'anoni da dama a cikin Kur’ani: bangaren sama, duniyar sama, …[13].

Yana tabbatar da cewa wannan ayar na nuni da samuwar wasu halittu masu rai a wasu duniyoyin, wani lokaci haka yake cewa Kalmar sammai tana nufin duniyoyin sama a ayoyin da aka yi bahasin wannan kalma, sai dai zai iya yiwuwa Kalmar sammai a wannan ayar tana nufin dabakokin yanayin da yake gewaye da duniya ne wanda yake nufin dabakokin samammu da suka kama tun daga kananan halittu kamar kwayoyin zarra da bairos, har zuwa manya kamar tsuntsaye masu tashi a sararin sama da suke a warwatse da sararin samaniya.

  1. In dan a ka lura cewa har ya zuwa yau ilimin zamani bai tabbatar da samuwar halittu masu rai a cikin sauran duniyoyi ba sai dai kawai tsammani hakan, saboda haka ba zamu iya alakanta ma Kur’ani kai tsaye cewa ya yi bayanin samuwar wasu halittu masu rai sauran duniyoyi ba.
  2. Sakamakon bincike shi ne wasu masu tafsire suna nuni da cewa wadannan ayoyin suna bayanin sirrin ilimi ne wanda har yanzu masana ba su gano ba wanda sai nan gaba ya iya bayyana.

 


[1] Shura, 29; daga cikin ayoyin mu akwai halitta sama da kasa dad a abin da ya yadu tsakanin sun a masu tafiya a kan tatara su shi mai iko ne,

[2]Rahaman 29 yana tambaya a kan abin da ke cikin sama da kasa ko wane lokaci ya na cikin sha'ani,

[3] Nahal,49 ga Allah suke sujudi abin da ke sammai da kasa na daga dabbobi da mala''iku kuma bas a girman kai.

[4] Isra,44 abin da ke sammai da kasai yana tisbihi ga Allah da abin da ke tsakanin su.

[5]Miraj,40 ba sai nayi rantsuwa da ubangijin sammai da kassai cewa mu masu iko ne, dafat,5 : aaraf. 137.

[6] Wannan kalma 61 tazo cikin kur''ani.

[7] Fatiha,2

[8]Shura,29

[9] Dan neman bayani, riza isfahani. Bincike a kan ilimin mujizojin Kur’ani, jildi na 1,shafi ,195-206

[10]Almizan jildi 18, shafi na 58.

[11] Tafsir namune jildi na 20, shafi 436-439.

[12]Safinatulbahar, jildi na 2, shafi 574

[13]Tafsir namune jildi 1 shafi 165-166

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa